Ticker

6/recent/ticker-posts

Mutum Ne Aka Bashi Rikon Maraya Saiya Mutu Da Dukiyarsa A Hannunsa Yaya Za Iyi Da Ita.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mutum Ne Aka Bashi Rikon Maraya Saiya Mutu Da Dukiyarsa A Hannunsa Yaya Za Iyi Da Ita.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله

Wanda aka bashi rikon maraya sai Allah yayiwa marayan rasuwa kuma akwai dukiyarsa ahannun mai rikon nasa abun da yakamata ya yi shi ne:

Idan akwai bashi a kan marayan yabiya masa duk wani bashi dake kansa, haka idan ya yi wasiyya kafin rasuwarsa cikin abun da bai haura ɗaya bisa ukun dukiyarsaba yazartar da wannan wasiyyar idan ta aikin alkhairice ko sadar da zumunci saboda faɗin Allah madaukakin sarki:

كُتِبَ عَلَيْكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ إِنْ تَرَكَ خَيْرًا الْوَصِيَّةُ لِلْوَالِدَيْنِ وَالْأَقْرَبِينَ بِالْمَعْرُوفِ ۖ حَقًّا عَلَى الْمُتَّقِينَ

An wajabta muku idan mutuwa tazowa mutum sai ya yi wasiyyah dawani abu cikin dukiyarsa ga mahaifansa ko 'yan'uwansa da kyakkyawan abu, hakkine a kan makusantansa zartar da wannan wasiyyar. (Suratul Bakara Ãya ta 180)

فَمَنْ بَدَّلَهُ بَعْدَمَا سَمِعَهُ فَإِنَّمَا إِثْمُهُ عَلَى الَّذِينَ يُبَدِّلُونَهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Duk wanda yacanza wasiyyar mamaci bayan yaji wasiyyar/ ya gani to zunubin yanakan wanda yacanza ɗin lallai Allah maijine kuma masani a kan komai. (Suratul Bakara Ãya ta 181)

Dan haka dai Zai cika masa wasiyya idan marayan yabar wasiyya ga 'yan'uwansa haka zai bincika in akwai mai binsa bashi ya biya masa bashi.

Bayan haka inyanada Magada zai basu dukiyar su rabata tsakaninsu kamar yanda Allah ya yi Umarni, idan kuma bashi da magada sai ya yi masa Aikin alkhairi da ita kamar saka kafet ko tabarmi amasallaci ko zuwa kauye inda sukeda wahalar ruwa ya haka musu rijiyar daniyyar yiwa marayan sadaƙatul jariya da dukiyar daya bari, ko wani aikin alkhairi.

Saboda hadisi ya inganta cewa: idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa sunyanke sai guda uku ( Sadaƙa mai gudana, ko Ɗah nagari dazai dunga yi masa addu'a, ko ilmi daya bari ake amfana dashi).

Wannan shi ne abun da zaiyi in Shã Allahu.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments