Ticker

6/recent/ticker-posts

Ayar Da Ta Yi Bayani Kar Ana Kiran Manzon Allah ﷺ Da Sunansa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam ina son agayamin ayan datayi bayani kamar haka: (1). Ayan da ta yi bayani kar a kara kiran Sunan Mazon Allah da Sunan Sa. (2). Ayan Data Yi Bayani An Halicci Annabi adam daga yumɓu. (3). Ayan Data Yi Magana a kan Annabi adam da suka ci itaciya sun tuba.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Ayar datayi Magana a kan Muminai sudena kiran Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam da sunansa Ƙarara kamar yanda suke kiran Junansu ita ce Ayar datake cikin Suratul Nuur ayata (63)

Allah madaukakin Sarki ya ce:

لا تَجْعَلُوا دُعَاء الرَّسُولِ بَيْنَكُمْ كَدُعَاء بَعْضِكُم بَعْضًا قَدْ يَعْلَمُ اللَّهُ الَّذِينَ يَتَسَلَّلُونَ مِنكُمْ لِوَاذًا فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَن تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ.

Yaku Muminai kada kudunga kiran Manzan Allah da Muhammad ko ya Muhammad bin Abdullahi kamar yanda kuke kiran junanku, ku girmamashi Kudunga cewa Ya Annabin Allah ko Ya Manzan Allah, Allah ya san Munafukai dasuke sulalewa aɓoye daka Majalisin Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam batare da neman izininsa ba, Suna ɓoye junansu, Masu saɓa Umarnin Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam suguji kada wata masifa ta sakko musu, ko azaba mai radadi da wahalarwa tasamesu aranar alƙiyama.

2- Ayar datayi Bayanin An halicci Babanmu Annabi Adamu Alaihissalamu daka yumɓu tazo a cikin Surori maban-banta agurare daban-ban zamu ambaci guda ɗaya kawai wacce tazo a cikin Suratul Isra'i ayata (61), Allah Madaukakin Sarki ya ce:

وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ قَالَ أَأَسْجُدُ لِمَنْ خَلَقْتَ طِينًا.

Lokacinda Mukace da Mala'iku su yi sujjada ga Annabi Adamu dukkansu sai suka yi masa sujjada,  Sai iblis ne kaɗai yaƙi yin Sujjadar ya ce: Yanzu zanyi sujjada ga Wanda ka halitta daka yumɓu taɓo, yana fadawa Allah haka.

Wani wajen ya ce: Nafishi alkhairi ka halicceshi daka yumɓu nikuma ka halicceni daka wuta.

Yasha alwashin kuma Saiya hallakar da Zurriyar Annabi Adamu saboda baƙar adawa da girman kai.

3- Ayar datayi bayanin Bayan Annabi Adamu Alaihissalamu da matarsa sunci itaciyar da'aka hanasu ci a cikin Aljannah sun tuba kuma Allah yakarbi tubansu ita ce Aya ta (37) a cikin Suratul baƙara, Ayar datake cikin Suratul A'araf taƙara fito da Abun filla-fillah.

Allah madaukakin Sarki ya ce:

 فَتَلَقَّى آدَمُ مِنْ رَبِّهِ كَلِمَاتٍ فَتَابَ عَلَيْهِ إِنَّهُ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ .

Annabi Adamu Alaihissalamu yakarbi wasu kalmomi daka Allah daya kimsa masa  na tuba yayin da yagane kus-kurensa nacin itaciyar da aka hanasu ci, sai suka tuba ga Allah Allah yakarbi tubansu, Lallai Allah mai yawan gafarane mai jinkai.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀��𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments