𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin gaskiyane Allah yana yafe ko wanne zunubi
amma banda shirka, wanda ya yi sata ko ya cucu jama'a fa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Na'am gaskiyane Allah yana yafe kowanne zunubi da
bawa ya mutu yana aikatawa, idan yaga dama ga wanda yaso amma banda shirka hada shi da Wani bawansa
wajan bauta. Kamar yanda Ayoyi da hadisai ingantattu da dama Suka nuna. Hatta
ita shirka idan ka tuba kafin kamutu Allah yana karɓan tuban wanda yatuba.
Sata tana daka cikin haƙƙin bayi. Akwai sharudda
wajan tuba daka haƙƙoƙin dasuke shafi tsakaninka da bayi., shi ne Abun
da ka zalunci mutum ka mayar masa, koka war-ware in ƙazafine ko sharri.
Saboda hadisin da Bukhari ya ruwaito ( 2449) daka Abu huraira Allah yaƙara
masa yarda yace; Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Wanda akwai
wani abu daya zalunci ɗan'uwansa
a mutuncinsa ko wani abu yaje ya war-ware shi yau dinnan kafin ya zama dinari
ko azurfa, idan yana da kyakkyawan aiki a dauka daka ladan aikinsa gwar-gwadon
zaluntar ɗan'uwansa
da ya yi abashi, idan bashi da kyakkyawan aiki adakko mummunan aikin wanda ya
zalunta ajibga masa).
Nawawi Ya ce: Saɓo idan tsakanin bawane da Ubangijinsa
bashi da alaƙa da haƙƙin ɗan adam yana da Sharudda guda uku:
1. Dena zunubin.
2. Nadama a kan saɓon.
3. Ya ƙudurci niyyar bazai sake aikata aikin ba.
Idan aka rasa ɗaya daka cikin ukun nan tuba bai tabbata
ba.
Idan saɓo yanada Alaƙa da ɗan adam ne kawai, sharuddansa guda huɗu ne, wadancan guda ukun, sai barranta
daka haƙƙin ɗan'uwanka,
idan dukiyace ko wani abu ka mayar masa, idan ƙazafine ka sanar da shi koka
nemi afuwarsa, idan gulmar sa kayi sai kaje ka war-ware gulmar.
Riyazussaliheena shafi na (33).
Idan mutum yasaci dukiyar wani, kuma yanajin
nauyin fada masa, saboda yana tsoran zumuncinsu zai yanke, ko abokantarsu, ba
dolene ya bashi labari ba, zai mayar masa da dukiyarsa ta dukkan hanyar dazata
iyu, kamar ya shigar masa da shi cikin kayansa, koya baiwa wani yabashi abarsa.
Idan wanda kaiwa sata bakasanshi ba, to zakayi
sadaka da ƙiyasin abun da ka satar masa da niyyar shi kayiwa sadakar.
Fatawa islamiyyah Na Usaimeen (4/162).
Wajibine ka mayar da dukiyar da ka sata zuwa ga
wanda ka satarwa, ko zuwa ga magadansa idan ya mutu, idan ka kasa ganeshi,
zakayi masa sadaka da ita, da sharadin duk sanda kuka haɗu zaka bashi zabin a kan sadakar dakayi
idan yayarda abarshi asadakar shikenan, in yace dukiyarsa yakeso dole ka nemo
ka bashi.
Idan ka jahilci iya yawan dukiyar da ka sata,
saika rinjayar da Abun da mafi rinjayen zatonka ya karkata ka barranta da ita,
idan zatonka ya rinjyar maka misali tsakanin dubu takwas da goma, saika
rinjayar da goma.
Abun da ka kasa mayarwa na kayan sata bashi ne
akanka, bazaka kubuta daka zargi a kan saba sai ka bayar dashi, abun da yake
wajibi akanka anan, shi ne ka tabbatar da shi a cikin wasiyyarka, dan tsoran
kada Mutuwa tazo maka kafin ka bayar dashi, saboda hadisin da Bukhari ya
ruwaito (2738) da Muslim (1627) daka Ibnu Umar yaji Manzan Allah Sallallahu
Alaihi wasallam ya ce: ( haƙƙine a kan duk wani musulmi da ya san akwai haƙƙin
wani abu a kansa da zai wasiyya a kansa ya yi kwana uku face wasiyyar sa tana
rubuce, Abdullahi ɗan
Umar ya ce: Babu wani dare da zaizo ya wuce tun daga lokacin da naji Manzan
Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya fadi wannan, batare da wasiyyata tana nan
arubuce ba.
Wanda ya tuba, tuba na gaskiya kuma ya yi kokarin
bayar da dukiyar daya sata gamai ita, sai mutuwa tazo masa, ana fatan Allah ya
yi masa afuwa ya biya masa, yasa masu dukiyar su yafe masa ranar Alkiyama, zaka
yarda da wannan daka hadisin da Bukhari ya ruwaito (2387) daka Abiy Huraira
Allah yaƙara masa yarda ya ce: ( Wanda yadauki dukiyar mutane yanasan biyansu Allah
zai biya masa, wanda ya dauki dukiyar mutane da nufin ya wulaƙanta
musu ita, ( Lalata musu ita) Allah zai wulaƙanta shi).
Ha'inci kuma saika yawaita nemewa wanda ka ha'inta
koka cucesu gafara awajan Allah, tare da kyautata halayenka da ƙara
yawaita nagartattun ayyuka, domin dangane da Tuba Allah ya ce: ( Ni mai gafara
ne ga wanda ya tuba ya yi imani ya yi aiki nagari sannan ya shiryu) Suratul
Daha aya ta (82).
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.