Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Tasbihin A Inda Mutum Ya Yi Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Dazarar an idar da sallah, wasu saisu tashi daka gurinda suka yi sallah su koma gefe su yi tasbihinsu, shin barin gurin ya dace ko bai dace ba, dolene yin tasbihin a inda mutum ya yi salla?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Sunnah azikirorin da akeyi bayan Sallah, ana fadarsu dazarar an sallame daka Sallah, batare da wata rata ko jinkiri mai tsawo ba, Sallar farillah ko ta nafila, Babu laifi ayisu bayan an fita daka Masallaci, ko ana tafiya izuwa gida, ko ayi wasu a cikin Masallaci wasu kuma a kan hanya, idan daka gama Sallah ne, sai dai yinsu a masallaci ya fi falala.

Hadisai da aka ruwaito a kan zikirorin da akeyi bayan sallah ana fadarsu ne, da zarar an yi Sallama, Kamar fadinsa: ( Wanda duk ya karanta ayatul kursiyyu aƙarshen kowacce sallah, Babu abun da zaiyi masa shamaki da shiga Aljannah sai dai mutuwa) Ibnu sunni ya ruwaitoshi a cikin "Amalullaili wallailah" (124).

Uƙbah bin Ãmir Allah ya ƙara yarda da shi ya ce: Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya Umarceni in karanta Falaƙi da Nasi da Ƙul-huwa aƙarshen kowacce Sallah, Abu dauda ya ruwaitoshi (1523) Albani ya Ingantashi a cikin "Sunanu Abi Dauda".

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Sanar da Sahabbai zikirorin da akeyi bayan kowacce Sallah ya ce: ( Kudunga tasbihi da Kabbara da tahmidi aƙarshen kowacce sallah, ƙafa talatin da Uku) Bukhari ya ruwaito shi (843) da Muslim (595).

Muslim ya ruwaito hadisi (596), daka Ka'ab bin Ujrah Allah yaƙara yarda da shi ya ce: ( Zikirorin bayan Sallah mai fadinsu ko Mai aikatasu ƙarshen kowacce Sallar farillah, Baya tabewa).

Yazo a cikin Kashshaful Ƙina'i (1/365). Abun da ake nufi mutum ya yi Wadannan zikirori bayan Gama sallah yana zaune, idan ya yi su atsaye ko yana tafiya, abun da yake a fili shi ne: ya dace da Sunnah, da mutum zai shagala baiyi su ba, saiya tuna ya yi su, Abun da yake zahiri shi ne zai samu ladansa kebantacce, idan akusane ba'a dau lokaci mai Tsawo ba, kuma Abisa uzuri, Amma Idan da gan-gan yaƙi yinsu, sai bayan lokaci mai Tsawo ya tuna abun da yake afili shi ne bazai Samu kebantaccen ladan yinsu ba, Amma ladan zikiri na koda yaushe zai same shi.

Saboda babu Laifi ana Sallamewa daka Sallah mutum ya koma gefe ya yi azkar ɗinsa.

Ya halatta ya yi Wani bangare na Azkaar ɗin a cikin masallaci Sauran ya ƙarasa awaje, ko a kan hanya ko yana tafiya.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments