𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mallam wane ruwane ruwan alkausara kuma an ce wai
duk wanda ko wacce ta sha ko yasha ruwan alkausara bazai mutu ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله رب العالمين والعاقبة للمتقين،
Alkausar aharshen larabci sifanta abu ne wanda
yake nuna kaiwar abun makura wajan yawa.
Amma ashari'ance tana da ma'anoni guda biyu:-
1. Ma'ana tafarko shi ne wani tafkine na ruwa a
cikin aljannah Allah yabaiwa Annabinsa sallallahu Alaihi wasallam wannan
ma'anar ita ce ake nufi a cikin faɗin
Allah maɗaukakin
sarki:
إِنَّا أَعْطَيْنَاكَ الْكَوْثَرَ
Lallai munbaka ruwan alkausara.
Kamar yanda Annabi sallallahu Alaihi wasallam
yafassarashi dahaka kamar yanda yazo a cikin sahihul muslim ( 607) daka Anas
yardar Allah takara tabbata agareshi ya ce: watarana muna zaune tare da manzan
Allah sallallahu Alaihi wasallam saiya dan sunkuyar da kansa kasa, saiya dago
kansa yana murmushi sai mukace: mai yasaka dariya ya manzan Allah? sai yace
Ansaukar min da sura saiya karanta wannan sura
إِنَّا أَعْطَيْنَاكَ الْكَوْثَرَ
izuwa karshenta, sannan saiya ce: ko kunsan mene
ne Alkausar? Sai sahabbai suka ce: Allah damanzansa sune suka sani, saiya ce:
wani tafkine Allah yayimun alkawarinsa akwai alkhairi maitarin yawa atare
dashi, tafkine da Al'ummata za su dunga zuwa shansa ranar Alkiyama.
Wajan turmuzi ( 3284) daka Abdullahi dan umar
Allah yakara yarda dasu daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce: Alkausar
tafkine a cikin aljannah cikinsa na dinarene magudanarsa ta yaƙut ce,
Albani ya ingantashi a cikin sahihul turmuzi.
2. Ma'ana ta biyu: shi ne tafkine mai girma, tafki
shi ne matartarar ruwa, za a sanya shi afilin taron alkiyana ranar sakamako,
Al'ummar Annabi sallallahu Alaihi wasallam za su dinga kwarara zuwa gareshi,
wannan tafki ruwa zaidunga zuwar masa daka alkausar din dake aljannah, saboda
haka ake kiransa tafkin alkausara, dalili a kan haka shi ne abun da imamu
muslim yaruwaito daka hadisin abu zarri (4255) tafkin ana zubo masa ruwan
alkausara daka aljannah ta gurare biyu, zahirin hadisin yana nuna tafkin yana
gefen aljannah ne dan aringa zubo masa ruwan alkausarar dake cikin aljannar,
kamar yanda ibnu hajar yafada a cikin fathul baary ( 11/466).
Saboda haka ruwan alkausara babu shi anan duniya
ballantana mutum yasamu yashashi yaki mutuwa, wannan karyane irin wacce batattu
ke sacewa mutane imaninsu da ita dansu yaudaresu, Allah ya yi mana tsari da
miyagu masu batar da bayin Allah daka hakikanin shari'arsa.
والله أعلى وأعلم.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.