Ticker

6/recent/ticker-posts

Ruɓewar Jikin Mutum A Cikin Kabari

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Wai shin idan mutum ya mutu an binneshi bayan kwana uku jikinsa zai ruɓe yafarfashe, shin koda mutum ya mutu da imani hakan yashafeshi koya shafi mai imani da marar imani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله العزيز المنان.

jinkirtawa mamaci kwana uku sannan ayi masa addu'a ko kwana goma ko talatin ko arba'in da ƙudurce cewa jikinsa yana wuce wasu matakai nabala'ai atsakanin waɗannan kwanaki na zuwansa Kabari aikine daya sabawa sunnah, kuma abu ne dabashi dawani dalili, kuma bidi'ane wacce mutane suka farar da ita bayan shudewar Annabi da sahabbai.

Abun da yazo asunnah shi ne yiwa mamaci addu'a dazarar anbinneshi akabarinsa, sannan yiwa sauran matattun musulmai gaba ɗayansu a cikin jimillah da kuma keɓancewa batare da kayyade wani lokaci ba ko zamani ba, mamaci yana bukatar addu'ar 'yan'uwansa musulmi koda wanne lokaci, komai tsawon zamani.

Amma cewa jikin mutum zai ruɓe yafarfashe bayan kwana uku wannan ya Saɓawa sunnah bashi dawani dalili daya tabbatar dashi, kuma ba asamu wani daka cikin malamai magabata daya fadi hakanba, ko kuma wani daka cikin jagoririn musulunci, haka babu wani malami daka cikin malamai likitoci ko masu sharhi daya fadi hakan azamanin sahabbai ba.

Maganar wai cewa mutum yana fashewa ko kansa yana fashewa akwana ukunsa nafarko a kabari, sannan tunbinsa yana fashewa a kwanaki gomansa na kabari, sannan sauran jikinsa zaifashe gaba ɗaya a kwana arba'in, magane ɓatacciya, zancene nakarya, babu wani dalili a kansa, watakila wannan zancen shi ne asalin aikata bidi'ar arba'in bayan mamaci ya mutu, tayanda ake wasu ababe mutane sutaru dan ta'aziyyah, alaramomi sukaranta alƙur'ani, hakika malamai sunce wannan aiki bidi'ane.

Antambayi shaik usaimin rahimahullah makamanciyar irin wannan tambayar sai ya ce: Wannan yana daka cikin bidi'ar da mutane suke aikatawa idan mamaci yacika kwana arba'in, sai ahada masa wani dantaro wanda mutane za su hadu agidan mamacin, sukaranta alƙur'ani su kawata waje, wanda ahakikaninsa yana cikin babin tunawa mutum bakin cikinsa, wanda haramunne.

Fatawa Nurun Alardarbi ( 9/2).

Haka zama har tsawon kwanaki uku bayan mutuwar mamaci ana addu'a dakaranta alƙur'ani dakarbar masu ta'aziyyah shima yana cikin Abun da mutane suka kirkira bidi'ane baida asali a cikin addini.

Babu wani daka cikin malaman musulunci wanda ya yi fatawa da halascinsa, Balle yazamto sunnah ko aikin sahabbai.

Amma matakan da jikin dan Adam yake bi bayan ya mutu harya koma kasusuwa Al'amarine wanda Allah kaɗai ya sanshi, kowanne jiki yakan saɓa dana wani wajan matakan dazaibi kafin yazama kashi, ba dukkan jikin mutane ne sukebin mataki iri ɗaya ba, ko zamani ɗaya ba, babu bukatar musan waɗannan matakan, ko bincike akansu, jikin yana wuce waɗannan matakaine da gaggawa koda jinkiri, uwar hanjinsa tana fashewa akwana goma ko samada haka, ko kasa dahaka, shagaltuwa da wannan irin bincike da tunani da makamantansa zaikai mutum zuwa ga abun da ya fi wannan ɗin girma, abun da ya fi dacewa mutum yashagaltar da kansa akai shi ne ruhi "rai" shi ne halin da ran mutum zai tsinci kansa na Ni'ima ko azaba.

Sauda dama a kan samu jikin matacce yakwashe shekaru masu yawa babu abun da yafita daka gareshi, amma kuma yana cikin azaba makaskanciya.

Ga fir'auna Allah yace;

فَالْيَوْمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنْ خَلْفَكَ آيَةً ۚ وَإِنَّ كَثِيرًا مِنَ النَّاسِ عَنْ آيَاتِنَا لَغَافِلُونَ

Ayau zamu tseratar da gangar jikinka danya zamto izina gawanda za suzo bayanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu. (Suratul Yunus Aya ta 92).

Haka sau dayawa a kan samu gawar mutum ta rututtuke ta farfashe amma kuma mai gawar yana cikin Wadanda Allah yakewa ni'ima akabarinsu, kuma saika samuma yana daka cikin shahidai.

Yazo a cikin littafin Akbaaru makkah ( 2/351) da Muhallah ta ibnu hazam ( 1/42)

Daka mansuur bin Abdurrahman, daka mahaifiyarsa ta ce: lokacinda aka kashe ibnu zubair yardar Allah takara tabbata agaresu, Ibnu Umar yardar Allah takara tabbata agaresu yashiga masallaci, sai akace dashi, Asma'u bintu Abubakar yardar Allah takara tabbata agaresu tana wani bangare na masallaci, saiyaje wajenta ya yi mata ta'aziyyah, ya ce:  wannan lalacewar jikin bakomai ba ne, "rai" yana wajan Allah maɗaukakin sarki kiji tsoran Allah ki yi hakuri, saita ce: mai zaihanani na yi hakuri, alhali anbaiwa wata karuwa daka cikin karuwan banu isra'ila kyautar kan yahya bin zakariyyah, isnadin hadisin ingantaccene.

Sannan saiya sauka zuwa gefen kaburburan da alamunsu sun goge, saiyai duba zuwa wani kabari daka cikinsu, saiyaga kashin kansa yahade da juna, saiyayi umarci  wani mutum yarufeshi, saiya ce: Lallai irin wannan lalacewar jikin gawa ba abun da yake cutar da ita, kawai rayuka akewa uƙuba ko ni'ima har zuwa ranar alkiyama, Tafsiru ibnu rajab ( 2/102)

Asali shi ne azaba ko ni'ima akabari ana yiwa ran mutum ne, hakika ruhinsa yana kai ni'imar ko azabar zuwa jikinsa.

Dan haka cewa mutum yakan ruɓe ko uwar hanjinsa yana fashewa dayayi kwana uku akabari wannan bashi da asali, kuma babu bambancin kafiri da mumini, domin kamar yanda muka baiyana azaba ko ni'ima ana yiwa rai ne ba gangar jiki ba, sai rai ya isar zuwa ga jiki.

Allah yakan tseratar da jikin kafiri baiyi komai ba tsawon lokaci akabari amma kuma yana cikin azaba mai girma, haka yakan cakuda jikin mumini a kabari amma kuma yana cikin Ni'ima harzuwa ranar alkiyama.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments