Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zaman Makoki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam mahaifina ya rasu, sai wani malamin islamiyyarmu ya ce min ba kyau zaman makoki, to gaskiya kaina ya daure, saboda na taso na ga ana yi, kuma idan ban yi ba za a ce ban damu da mahifinmu ba, malam yanzu yaya zan yi ? Allah ya datar da kai zuwa dukkan alkairai .

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To dan’uwa Allah ya ba mu dacewa gaba ɗaya, tabbas malamai sun tattauna a kan hukuncin zaman makoki, sai dai sun kasu kashi uku:

1. Akwai waɗanda suka tafi a kan makaruhi ne, saboda hadisin Jarir R.A wanda Imamu Ahmad ya rawaito cewa: “Mun kasance muna kirga taruwa yayin mutuwa da kuma yin abinci ga gidan da aka yi mutuwa daga cikin rurin da Allah da ya haramta” , Musnad: 6905, don haka suna cewa, sai dai a haɗu da waɗanda aka yiwa rasuwa a kan hanya ko a kasuwa, ko masallaci ayi musu ta’aziyya, wannan ita ce maganar Shafi’i a cikin Umm 1\318, haka Nawawy a Majmu’u 3\306 .

2. Akwai waɗanda suka tafi a kan cewa bidi’a ne, kamar Ibnul-kayyim a zadul ma’ad 1\527

3. Akwai malaman da suka tafi a kan halaccin zaman makoki, saboda hadisin da nana A’isha ta rawaito cewa, lokacin da aka kashe Zaid ɗan Haritha da Ja’afar ɗan Abu-dalib Annabi ya zauna a wani wuri, duk wanda ya gan shi zai ga alamun bakin cikin tare da shi, sai wani mutum yazo yace masa: ga matan Ja’afar can suna ta kuka, sai Annabi ya umarce shi da ya je ya hana su, su kuma yi hakuri” Bukhari hadisi mai lamba ta: 1299. Waɗannan malaman suna cewa: za a iya fahimtar hallacin zaman makoki a wannan hadisin a wurare guda biyu:

1. Faɗin nana A’isha cewa: ya zauna ana ganin alamun bakin ciki tare da shi da kuma zuwan wancan mutumin, dalili ne da yake nuna cewa: yana zaune ne a wurin da mutane suka sani kuma suke zuwa su same shi.

2. Kasancewar bai hana matan Ja’afar taruwar da suka yi ba, kawai kukan ya yi umarni da a hana su.

Wannan magaanar ta hallaci an rawaitota daga Imamu Ahmad kamar yadda ya zo a Insaf 5\565 da kuma Ibnu-Abdulbarr na Malakiyya, kamar yadda ya zo a littafinsa na Alkafy 1\283, sannan wasu daga cikin Hanafiyya sun tafi a kan haka kamar yadda ya zo a Binaya 3\303

Prof. Khalid Al-mushakih (ɗaya daga cikin manyan daliban Sheik Bn Uthaimin) ya rinjayar da zance na uku, sai dai za a guji abubuwa kamar haka a lokacin wannan zaman:

1. Yawaita yin abinci, da masu karɓar gaisuwa, zai yi kyau ya zama makusantansa ne kawai za su amshi gaisuwa.

2. Nisantar yin laccoci a wurin, domin hakan na daga cikin bidi’o’in da ba su da hujja.

3. Nisantar tsawaita zaman, a yi shi gwarwadon bukata.

Don neman karin bayani duba: Fiƙhunnawazil na Khalid Al-mushaikih shafi na: 75

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments