Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Salon Amfani Da Harshen Fandarewa A Littafin ‘Yartsana Na Ibrahim Sheme

Cite this article as: Sabo, S. (2023). Nazarin Salon Amfani Da Harshen Fanɗarewa A Littafin ‘Yartsana Na Ibrahim Sheme. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 197-204. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.023. 

Daga

Saminu Sabo
Department of Hausa
College of Education and Legal Studies, Nguru,
Yobe State
, Nigeria
Imel saminusabo3467@gmail.com

Tsakure

Wannan bincike ne da aka gudanar ta hanyar nazarin Salon Amfani Da Harshen Fanɗarewa A littafin ‘Yartsana na Ibrahim Sheme. Muradin wannan binciken shi ne a fito da yadda aka yi amfani da salon fanɗarewa a littafin‘Yartsana na Ibrahim Sheme. A binciken an yi amfani da Ra’in Fanɗarewa daga Karƃaƃƃun Al’adun Al’umma (Deviantional Theory) wanda wani Bature mai suna Geoffry Leach (1969) ya samar. Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su domin tattattara bayanan wannan bincike kuwa akwai: karance-karance da hira da tattaunawa da marubuta ƙagaggun da masana da makaranta ƙagaggun labarai na Hausa. A binciken an gano salon fanɗarewa iri biyu: salon fanɗarewa a ɗaiɗaikun kalmomi da kuma jumlataccen salon fanɗarewa.

Fitilun Kalmomi: Salo, Fanɗarewa, Harshe, Nazari, Кagaggun Labarai

1.0 Gabatarwa

Masana da manazarta sun gudanar da aikace-aikace masu yawan gaske dangane da abin da ya shafi salo da kuma ƙagaggen labari. Wasu sun duba salon ne a karan-kansa, Yahya (2016). Wasu kuma sun yi nazarin salon ne a cikin wasu littattafai da aka wallafa, Haruna (2014) da Nafi’u (2012) da Yahaya (2021). Yayin da wasu kuma suka kwatanta salalai na marubuta daban-daban, Binta (2014) da Kukuri (2015) da Abdullahi (2014). Wannan aiki ya bambanta da waɗanda aka ambata a sama, domin an duba wani ƃangare ne na salo a cikinsa, wato salon amfani da harshen fanɗarewa a littafin ‘Yartsana wanda Ibrahim Sheme ya wallafa. Shi wannan littafi an wallafa shi ne a shekarar (2003) Marubucin littafin ya ƙoƙarin fito da halayyar mata karuwai da manemansu da yadda rayuwarsu take kasancewa a cikin littafin. Littafin yana /ƙunshe da ire-iren maganganunsu da mutanen da suke hulɗa da su, da irin makomarsu wadda take nadama ce. Domin kuwa duk wadda ta tsinci kanta a irin wannan hali to, tabbas sai ta yi nadama daga ƙarshe kamar yadda ta faru ga Zainab a cikin littafin. A wannan takardar an kawo maá’nar salo da ta fanɗarewa da salon fanɗarewa da ire-iren salon fanɗarewa sannan aka fito da wannan nau’i na salon fanɗarewa a littafin ‘Yartsana. A ƙarshen aikin an kawo wasu ire-iren salon fanɗarewa da aka gano a littafin da aka nazarta.

1.1 Ma’anar Salo

Masana da dama sun tofa albarkacin bakin su dangane da yadda suka fahimci salo. Misali: Ɗangambo (2007:37) yana ganin salo “hanyoyi ko dabarun isar da saƙo.” Shi kuwa Gusau (2013) cewa ya yi “salo ya shafi hanyoyi ko dabarun da aka yi amfani da su na ƙawata zance da ƙara masa gishiri ta yadda zai yi zaƙi.” Yayin da Mukhtar (2004) kuma ya bayyana salo da cewa “salo shi ne abin da ya danganci yadda mutane suke bambanta a wajen furucinsu.” A tasa fahimtar ‘Yar’aduwa (2007) ya fassara salo da “hanyoyin da marubuci ya bi wajen isar da saƙo ta yin amfani da harshe” Shi kuma Bayero (2001) yana ganin salo shi ne, “duk wata dabara ko hanya wadda aka bi domin isar da saƙo.” Ya ƙara da cewa dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana.

Idan aka yi la’akari da waɗannan ma’anoni da aka kawo a sama za a iya cewa salo wata hikima ce ko dabara da marubuta suke amfani da ita domin su cim ma burinsu na isar da wani saƙo ga al’umma.

1.2 Ma’anar Fanɗarewa

Kalmar fanɗarewa asalin wannan kalmar shi ne fanɗare shi ne aka yi mata ƙarin ɗafa ƙeya ‘wa’ ta koma fanɗarewa ta tashi daga matsayinta na aikatau ta koma suna. Ƙamusun Hausa (2006:133) ya bayyana wannan kalma da cewa “kauce ko karkace daga hanya. Ko saɓa ko bijire wa ra’ayin jama’a”. su kuwa Newman da Roxana (2020:353) sun bayyana kalmar da cewa “saɓa ko yin bidi’a daga tafarkin addini.

Idan aka yi la’akari da waɗannan ma’anoni da aka kawo a sama za a iya cewa fanɗarewa ta shafi bijirewa ko kin bin doka ko abin da al’umma suka yadda da shi.

1.3 Ma’anar Salon Fanɗarewa

Salon fanɗarewa ya shafi wani yanayi ne na sakin baki a magana wanda ya shafi maganganu na batsa da ashariya da cin mutunci da habaici da makamantansu. (Ruszkiewicz and Dolmage 2014) Exipository writing Blog: High, middle, and low style.

Bisa la’akari da wannan ma’ana da aka kawo a sama za a iya cewa, salon fanɗarewa ya shafi duk wani abin da yake da rauni wajen furta shi ko aiwatar da shi a al’adance. Misali: ɗanyen baki, da ɗanyar magana, da ashariya da makamantansu.

1.4 Ire-Iren Salon Fanɗarewa

 A wannan bincike da aka gudanar an kalli salon fanɗarewa ta fuskoki guda biyu kamar haka: Salon fanɗarewa a ɗaiɗaikun kalmomi da kuma jumlataccen salon fanɗarewa.

1.4.1 Salon Fanɗarewa A Ɗaiɗaikun Kalmomi

A irin wannan salo akan samu ɗaiɗaikun kalmomi ne da suke ɗauke da salon fanɗarewa wanda ya shafi zagi ko cin mutunci ko kuma rashin isa waɗanda ake ambatonsu a cikin kalma guda ɗaya tilo. Misali: zagi da batsa da wasu ayyuka da suka shafi assha.

1.4.1.1 Kalmomi Na Zagi

Idan aka ce zagi na nufin faɗa wa mutum baƙar magana ko ƃacin iyayensa. (CNHN, 2006:487)

Bisa la’akari da wannan ma’ana da aka kawo a sama za a iya cewa zagi na nufin faɗa wa wani ko wata baƙar magana don cin zarafinsa da wulaƙantashi a cikin bayyanar jama’a.

Ibrahim Sheme a cikin wannan littafin nasa mai suna ‘Yartsana ya yi amfani da irin wannan salo na zagi. Duba wannan bayani da ke ƙasa a inda yake cewa:

“Abin da nake son in sani shi ne, shin za ta zauna ta daɗe ne a nan gidan? Idan za ta zauna, to sai a yi mata tanadin ɗaki. Da ma ina cikin shirin korar ‘yar iskan nan Igge Bazamfara, in sanya wata a ɗakin.” (‘Yartsana sh 13)

Idan aka duba wannan bayani da ke sama a sheɗara ta uku za a ga mawallafin ya yi amfani kalma ‘yar-iska. Wannan kalma na nufin mace marar mutunci ko galihu. Don haka duk wadda aka kira da wannan kalma, zagi ne muraran aka yi mata kai tsaye. A taƙaice wadda aka kira da wannan kalma kamar ana danganta ta ne da mai yawan ta zubar (yawan karuwanci). Duk macen da aka kira da karuwa a al’adance ba ƙaramin cin zarafinta aka yi ba.

A wani shafin na daban mawallafin ya sake amfani da irin wannan salo karanta wannan bayani da ke ƙasa a inda yake cewa:

“Amma Maijigida a shirye take ta fanshe wani haushi da take da shi game da Magajiya. Ba za ta taƃa mantawa da yadda shegiyar tsohuwar ta ƙwace mata wani saurayi ba”. (‘Yartsana sh 16)

A wannan bayani na sama sheɗara ta uku za a ga mawallafin ya kawo kalmar shegiya wadda take nufin macen da aka haifa ba tare da an yi aure ba. Ko kuma zagin da ake yi wa mutum don wulaƙanta shi. Ke nan duk wadda aka kira da wannan kalma to ba ƙaramin cin mutuncinta aka yi ba masa ba. Duk wadda aka ce an haife ta ba ta hanyar aure ba, bisa al’adar Bahaushe wannan mace takan zama abar ƙyama a cikin al’umma domin ana mata kallon maras kyakkyawan asali. Idan kuwa haka ne, to ka ga ambaton mutum da wannan kalma ba ƙaramin cin mutunci ba ne.

Haka kuma, mawallafin ya sake yin amfani da wannan dabarar ta salon fanɗarewa a shafi na 46. A inda yake cewa:

“Amma yaro ya nemi ki ba shi ruwan ki na alkafira”. “kin sa ya ci uwarsa” (‘Yartsana sh 46)

Idan aka lura da wannan bayani na sama, a layi na biyu za a ga mawallafin ya kawo kalmar uwarsa wadda take nufin zagin da ake yi wa namiji mafi ƙasƙanci domin a wulaƙanta shi. Don haka kiran mutum da wannan kalma, bisa al’adar Bahaushe zagi ne a fakaice, mawallafin ya yi amfani da ita domin ya fito da irin tarbiyar mata masu zaman kansu.

Har ila yau, a cikin wannan littafi da aka nazarta, an ƙara samun wannan nau’i na salon fanɗarewa a shafi na 95, a inda mawallafin ya kawo shi kamar haka:

“Lokacin da Asabe ta shigo gidan duk mazajen sun waigo sun kalle ta. Basiru ya ƃara ya ce, “kutumar uban nan kai. Amma Asabe kin haɗu. Danƙari, sai ya shiga lashe-lashe leƃƃansa kamar mage, amma zolayar ta yake yi”. (‘Yartsana sh 95)

Bisa la’akari da wannan bayani da aka kawo a sama, za a ga an kawo kalmar kutumar da ta uba. Abin da ake nufin da kalmar kutumar shi ne sunan da ake kiran azzakari ta hanyar batsa. Ita kuwa kalmar uba na nufin laƙabin mutumin da aka sa wa sunan kakansa ko mahaifin mutum. Akan yi wa kalmar ƙari da wasu kalmomi don samar da wata ma’ana. A nan shi ne abin da mawallafin ya yi, ya haɗa wannan kalma da kalmar kutumar sai suka bayar da wata ma’ana ta daban da ya shafi zagi. Sai dai a wannan bayani da ya gabata, mawallafin ya yi amfani da su ne da nufin ban mamaki. Amma bisa al’ada da zarar mutum ya faɗe su za a ji kawai ashar ya yi.

1.4.1.2 Kalmomi Na Batsa

Batsa na nufin maganar banza, musamman wadda ta danganci ambaton al’aurar mace ko namiji. (CNHN,2006:41)

A taƙaice batsa na nufin duk wata kalma da ta danganci ambaton al’aura ko maganar tsaraici ko bayyana abubuwan da suka shafi mu’amullar saduwa tsakanin namiji da mace ko namiji da namiji ko mace da mace.

Ibrahim Sheme a cikin littafin da ya wallafa mai suna ‘Yartsana ya yi amfani da irin waɗannan kalmomi na batsa. Duba waɗannan bayani da ke ƙasa kamar inda yake cewa:

“Da ya dubi yarinyar da kyau sai ya ce a ransa kai, amma dai wannan ba gaja ba ce, don ko yadda ma take takawa ɗai-ɗai ta miskile shi. Ta haɗu. Nan da nan ya ɗimauta da kyaunta, yana mai lura da cikar halittarta: madarar idanunta da tsayiwar gorunan madarar nan da ke kan ƙirjinta, da gashin kai liya-liya tamkar na Nasara, kutirin nan kuma da ta wuce… kai sai wata makyarkyata yake yi. Abin dai ba a cewa komai”. (‘Yartsana sh 23)

Idan aka sa ido sosai a wannan bayanin da ke sama, sheɗara ta biyar da ta shida za a ga mawallafin ya kawo kalmomin gorunan. Sannan a sheɗara ta tara ya kawo kalmar kutirin waɗanda ya yi wa ƙari da nasaba. Kalma ta farko gorunan wadda jam’i ne ta kalmar gora da ke nufin nonon shayarwa na mace. Ita kuma kalmar kutiri na nufin ɗuwawu, musamman na dabba. Amma a nan mawallafin na nufin na ‘ya mace. Waɗannan kalmomi da mawallafi ya yi amfani da su kalmomi ne na batsa domin dukkansu suna bayyana al’aura ne.

Daɗin da ɗawa mawallafin ya sake yin amfani da irin wannan salon na fanɗarewa a shafi na 44. Karanta wannan bayani da aka kawo a ƙasa:

“Ya tafi Kudu ya kwaso yaran mata ‘yan ƙasar Ghana da wasu ƙabilu, ya zuba a ciki. Kuma yana da wata ɗabi’a: duk wadda ya ga nononta ya kwanta sai ya kore ta, wai ta fara tsufa. Saboda haka sai ya kashe wa sauran gidajen kasuwa, nan da nan kasuwar isakanci ta koma gidansa”. (‘Yartsana sh 44)

 A nan mawallafin za a ga ya ambaci kalmar nononta a sheɗara ta uku wadda ke nufin hantsar da ke ƙirjin mace ko marar dabba ko kuma ruwan da ake samu a jikin hantsar. Idan aka karanta bayani kamar yadda mawallafin ya kawo za a ga kalami ne wanda ya shafi batsa domin yana bayyana wani ƃangare ne na tsaraicin ‘ya mace.

Haka kuma, mawallafin a wani shafin ya kawo irin wannan nau’i na salon fanɗarewa wanda ya danganci batsa. Duba wannan bayani da aka kawo a ƙasa a inda yake cewa:

“Tana ji tana gani Alhaji ya yi mata zindir, sannan shi ma ya kwaƃe kayansa. Da ganin haka ta san abin da zai yi mata”. (‘Yartsana sh 125)

Idan aka lura da kyau za a ga mawallafin a sheɗara ta farko ya kawo kalmar zindir wadda take nufin tsirara. A taƙaice kalmar zindir na nufin kwaƃe wa mutum kayan jikinsa. Don haka, wannan kalma ta zindir na ɗaya daga cikin kalmomin da ake amfani da su a game da abin da ya shafi batsa. Mawallafin ya yi amfani da ita domin ya nuna abin da zai wakana bayan an cire wa mace kayan jikinta.

1.4.1.3 Kalmomin Miyagun Ayyuka

Miyagu na nufin mutum mai mummunan hali na cuta. (CNHN,2006:348) Ke nan miyagun ayyuka sun shafi aikata duk wasu halaye munana ko marasa kyau.

A nan ma mawallafin bai yi ƙasa a guiwa ba domin an samu irin wannan nau’i na salo a cikin littafin nasa. Duba wannan bayani da ke ƙasa:

“Ran nan daidai goshin magariba, Asabe da Bebi Sai-Tumoro sun dawo daga wurin shaye-shayen su, sai suka tarar ana tafka rigima tsakanin Abu Maijigida da farkan ta Abdullahi Sitiyari”. (‘Yartsana sh 53)

Idan aka duba wannan bayani da ke sama, sheɗara ta biyu za a ga an kawo kalmar shaye-shayen wadda ke nufin nanata shan abubuwa musamman masu sa maye. Ke nan shaye-shaye na nufin duk wani hali da mutum zai sa kansa na shan abin da zai sa shi tangaɗi ko ya bugar da shi. Mawallafin ya yi amfani da wannan tagwan kalma domin ya nuna wurin da Bebi da Abu Maijigida suke zuwa ba wuri ne na aikata abubuwa masu kyau ba. A taƙaice mawallfin na nufin gidan giya, kowa kuma ya san gidan giya ba waje ba ne na aikata abin kirki.

Bayan haka, mawallafin ya sake amfani da wannan nau’i na salon fanɗarewa a wani shafi na daban. Karanta wannan bayani da ke ƙasa inda yake cewa:

 “Кaurin ganye yana tashi daga cikin ɗakin, yana biyowa zuwa waje ta cikin wata ‘yar ƙofa dake gefen taga”. (‘Yartsana sh 56)

Idan aka duba sheɗara ta farko da ke cikin wannan bayani da aka kawo a sama, za a ga mawallafin ya kawo kalmar ganye wadda take nufin taba mai bugarwa. Don haka, ita ma ke nan tana daga cikin rukunin munanan ayyuka waɗanda a al’adance ake ƙyamarta. Duk wani abu da ake aikatawa a idon jama’a ana danganta shi da mai kyau. Abin da ake aikatawa a bayan idon mutane wannan abu ana danganta shi da abu marar kyau. Don haka, mawallafin bai bayyana shan ganye a idon mutane ba sai ya nuna a ɗaki ake yi kawai warin ne yake fitowa.

Har wa yau, mawallafin ya sake yin amfani da wannan dabara ta fito da wannan nau’i na salon fanɗarewa. Karanta wannan yanki na labari ka ji:

“Su Bara’u Emiya suna zazzaune a kan tabarmi suna yin karta shi da wasu maza uku da kuma wata karuwa guda ɗaya”. (‘Yartsana sh 94)

Idan aka duba wannan yanki na labari da ke sama a sheɗara ta biyu za a ga mawallafin ya kawo kalamr karta wadda take nufin wasu ƙananan katuna masu hotuna da rubutu da ake wasa ko caca da su. Irin wannan nau’i na wasa ko caca bisa al’ada an fi danganta su ga mutanen banza wato waɗanda su kame mutuncin kansu ba.

Daɗin da ɗawa, mawallafin ya ƙara fito da irin wannan nau’i na salon fanɗarewa a wannan yanki na labari da aka kawo a ƙasa inda yake cewa:

“Duk isakancin da ki ka ga Audu Dara yana yi, to da ɗaurin gindin Nakande. Ajiye mata suna karuwanci, neman mata -ke har mazan ma ba su bari ba- shan koken, murɗiyar zaƃe, har ma kisan kai…ba abin da suka bari”. (‘Yartsana sh 219)

Idan aka duba kalmomin da aka rubuta da tafiyar tsutsa da ke cikin yankin labarin da aka kawo a sama duka kalmomi ne da suka danganci munanan halaye. Kalmar karuwanci na nufin zaman mace maras miji da saduwa da maza don neman kuɗi. neman mata kuwa na nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure ba. Ita kuma kalmar koken kalma ce ta Turanci da aka fassara da hodar ibilis. Ana amfani da ita domin sa maye. Ita kuma kalmar murɗiyar tana nufin danniya ko rashin gaskiya. kisan kai wadda kuma nufin haddasa mutuwar wani. Duk waɗannan kalmomi da aka kawo a sama kalmomi ne da suke yin nuni da munanan halaye. Mawallafin ya yi amfani da su domin ya cim ma burinsa wajen isar da saƙonsa ga al’umma.

1.4.2 Jumlataccen Salon Fanɗarewa

Shi kuma wannan nau’i na salo ya shafi yadda ake samun wasu jumloli da suke ɗauke da maganganu na fanɗararru a jumlace walau na zagi ne ko na batsa ne ko na miyagun ayyuka ne waɗanda suke zuwa a cikin jumla. A taƙaice dai jumlar ce kacokan take ɗauke da irin wannan salo na fanɗarewa. Daga cikin irin wannan nau’i na salon fanɗarewa akwai:

1.4.2.1 Na Muzantawa

Idan aka ce muzantawa na nufin cin mutuncin wani. (CNHN, 2006:354) A taƙaice za a iya cewa muzantawa na nufin faɗa wa mutum Magana marar daɗi a idon jama’a. Mawallafin ya kawo irin nau’i na salo a wurare daban-daban a cikin littafinsa. Duba wannan bayani da ke ƙasa:

“Da abin ya ci ta ya ci ta, ran nan sai ta bayyana wa Bebi tunanin ta game da Cindo, tana cewa, wai ina ruwan mokaɗaɗɗiyar algungumar nan da ni ne har take shiga harkoki na”. (‘Yartsana sh 75)

A wannan bayani da aka kawo a sama, za a ga an kawo wani rubutu cikin tafiyar tsutsa tun daga kan sheɗara ta biyu zuwa ta huɗu. Idan aka karanta da kyau za a ga muzantawa ce mawallafin ya yi amfani da ita a wurin domin ci wa ɗaya daga cikin taurarin littafin mutunci. Tauraruwar da ake dangantawa da wannan maganar ta cin zarafi ita ce Bebi. A taƙaice mawallafin yana nuna ne a kan cewa Bebi ƙwararriya ce wajen iya munafurci.

Haka kuma, a wani shafin mawallafin ya sake amfani da wannan dabarar ta salon fanɗarewa inda ya kawo cewa:

“Karuwan cikinsa kuma kamar samarin cikinsa suke ke kidahumai kawai, ‘yan iska”. (‘Yartsana sh 76)

Idan aka lura da rubutun da aka kawo cikin tafiyar tsutsa za a ga mawallafin ya ambaci cewa kidahumai kawai, ‘yan iska. Wannan ƃatanci ne muraran mawallafin ya yi amfani da shi domin a ƃata wasu daga cikin taurarin littafin. Kalmar kidahumai na nufin bagidaje ko mai wauta. Ita kuma kalmar ‘yan iska na nufin waɗanda aka haifa ba tare an yi aure ba. Waɗannan kalmomi su ne mawallafin ya gina jumla domin ya ci wa taurarin mutunci.

Sannan a shafi na 128 mawallafin ya sake kawo wannan nau’i na salo na fanɗarewa inda yake cewa:

“Sai ka ga dattijo tukuf-tukuf, daga shi sai ‘yar shara, babu ko wando, an sa shi a bayan kanta, idanun nan nasa kamar mujiya a cikin bokiti, ko kuma ka ga karuwa da kai babu kallabi, ba ta da tufafi a jika in ban da rigar nono da siket, ko yaro wanda bai fi wata biyu da fara mafarkin balaga ba duk an kamo su”. (‘Yartsana sh 128)

A wannan bayani da ke sama kuma, mawallafin ya yi amfani da ba’a ne. Ba’a dai kamar yadda aka sani ita ce, zolaya ko muzantawa cikin wasa. Ba’ar da mawallafin ya yi amfani da ita a cikin wannan bayani da ke sama ita ce wadda aka kawo cikin rubutu tafiyar tsutsa kamar haka: idanun nan nasa kamar mujiya a cikin bokiti. Daga jin wannan ba’a ka san harka ce ta cin zarafi mawallafin ya yi amfani da ita ya muzanta ɗaya daga cikin taurarin littafin nasa domin ya cim ma wata manufarsa.

 

1.4.2.2 Na Batsa

 Kamar yadda aka karanta a baya, batsa na nufin maganar banza, musamman wadda ta danganci ambaton al’aurar mace ko namiji. (CNHN, 2006:) Wannan nau’i na jumlataccen salon fanɗarewa da ya shafi batsa shi ma an same shi a cikin littafin ‘Yartsana da aka nazarta. Duba wannan bayani da ke ƙasa inda yake cewa:

Amma da ya je ya dawo sai ta ga ya saki labulayen tagogi ya rarume ta, ita ko ta shiga ciccijewa da haure-haure na nuna ƙin amincewa da shi. Duk a banza. A nan dai ya yi amfani da ita, ya ƙosar da kansa daga ni’imar da Allah ya yi mata”. (‘Yartsana sh 26)

Idan aka duba dukkan bayanan da aka kawo a sama, za a ga wasu maganganu ne na banza da suka danganci mu’amalar da ke tsakanin namiji da mace irin wannan maganganu su ake danganta wa da batsa. Mawallafin ya yi hakan ne domin ya fito da mu’amullar da ke wakana tsakanin karuwai da manemansu.

Sannan kuma, mawallafin ya sake kawo irin wannan nau’i na salo na fanɗarewa da ya danganci batsa. Duba wannan bayani da ke ƙasa:

“An ce ta zauna a garuruwa da dama, musamman ma Agege inda ta koyo Yarbanci. Mace ce fitsararra, cikakkiyar ‘yar caburos, wadda ba ta san wani abu wai alkunya ba. Duk inda ta shiga tana kaɗa ɗuwawu tana girgiza mama sannan ga cingam koyaushe a cikin bakinta”. (‘Yartsana sh 47)

Idan aka duba kalaman da ke cikin tafiyar tsutsa a wannan bayani da aka kawo a sama za a ga cewa su ma maganganu ne da suka shafi batsa mawallafin ya yi amfani da su domin ya fito da halaye irin na karuwai. Domin karuwai ne suke aikata irin wannan halayya saboda su jawo hankunan manemansu. Ba a san macen ƙwarai da kaɗa ɗuwawu ko girgiza mama ba. Dukka dai mawallafin yana yin haka ne domin jawo hankalin mai karatu wajen isar da saƙonsa.

Har wa yau, a wani shafin na daban mawallafin ya sake yin amfani da wannan nau’i na salon fanɗarewa da ya shafi batsa. Karanta wannan bayani da ke ƙasa inda yake cewa:

“Da Basiru ya isa gidan ‘Yargata, sai ya sami Bebi Sai Tumoro da Isyaku kwance a kan gado suna sumbatar juna ba ƙaƙƙwatawa”. (‘Yartsana sh 87)

Idan aka lura da bayani da ke sama, za a ga an kawo wani rubutu a cikin tafiyar tsutsa, wanda idan aka karanta shi da kyau za a ga magana ce da ta danganci batsa. Domin mawallafin ya yi amfani da wasu kalmomi ne da suka danganci mu’amullar da ke haddasa saduwa tsakanin mace da namiji.

1.4.2.3 Na Zagi

Wannan kalma ita ma an kawo ma’anarta a baya da aka nuna cewa zagi na nufin faɗa wa mutum baƙar magana ko ƃacin iyayensa. A ta wannan fuska ma mawallafin ya kawo misalan nau’i jumlataccen salon fanɗarewa na zagi a cikin littafin nasa. Karanta wannan bayani da aka kawo a ƙasa:

Wane shegen ne ya ce miki mutuwa za ki yi? inji Bebi Allah wadaran mai tsoran mutuwa”. (‘Yartsana sh 106)

Idan aka lura da wannan bayanin za a ga cewa mawallafin ya kawo jumlar Wane shegen ne ya ce miki mutuwa za ki yi? Wadda take nufin ɗan da aka haifa ba tare da an ɗaura aure ba, ko zagin da ake yi wa mutum don wulaƙanta shi. Saboda haka, duk wadda aka gaya masa wannan kalmar to, an wulaƙanta shi a cikin mutane.

Sannan, mawallafin ya sake yin amfani da wannan dabarar ta salon fanɗarewa jumlatacce da ya shafi zagi a cikin littafin nasa da aka nazarta.

“Da jin haka sai ya ce mata a cikin hassala, uban wa ya ce miki ƙona ni za a yi? (‘Yartsana sh 141)

Idan aka duba kalaman da ke ƙarshen sheɗara ta farko zuwa ta biyu da aka kawo cikin rubutun tafiyar tsutsa za a ga kalamai ne da suka danganci zagi. Mawallafin ya yi amfani da su a wajen domin ya bayyana wa mai karatu abin da zai iya biyo baya yayin da rai ya ƃaci. Duk wanda aka yi wa kalami tamkar an zage shi ne ko da kuwa ba a kama sunan sa ba kamar yadda mawallafin ya yi.

Har wa yau, mawallafin ya sake amfani da wannan salo na zagi a cikin wannan littafi nasa. Duba wannan bayani da aka kawo a ƙasa:

“Bebi ta tsaya a karkace, ta dubi Maijigida a yanƙwane ta ce “kan bu…Maijigida, lafiya kike tsina ta haka? Kan ki ɗaya kuwa?” Kaina dubu don kwandon buhun ubanki, shegiya ‘yar Chadi baƙuwar haure. Ke Bebin ga ana ɗan raga miki, ashe ‘yab banza take ko?”. (‘Yartsana sh 56)

Idan aka lura da kalaman da ke cikin rubutun tafiyar tsutsa za a ga cike suke da tsagwaron zagi da cin mutunci irin na ‘yan tasha. Ba komai ya sa mawallafin ya yi amfani da hakan ba sai don kawai ya fito da irin rashin mutuncin da karuwai suke da shi a cikin mu’amullar su.

Daɗin daɗawa, mawallafin ya sake amfani da wannan nau’i na salo a shafi na 268. Duba wannan bayani na ƙasa:

“Wuf, sai ga Manjo ya buɗe ƙofa ya fita, ya buɗe but ɗin motar, ya ɗauko wata bulalar dorina. Kafin su ankara, ya buɗe ƙofar gidan baya ya naushi Fati Gidauniya, kuma ya shiga lafta mata bulalar nan, yana cewa, “shegiya ‘yar buhun uba, wannan makirci ne kuka ƙulla ke da Asabe kada Allah ya jiƙanta ma. Wato kun san baku da lafiya kuka riƙa kwana da mu, watau ku ga sheɗanu, ko? To billahillazi la’ila ha illahuwa sai na kashe ki, allabashi ni ma a kashe ni da hujja”. (‘Yartsana sh 268)

Idan aka duba layi na huɗu zuwa na biyar za a ga an kawo wani rubutu wanda aka yi shi cikin tafiyar tsutsa, yayin da aka karanta shi za a ji kalamai ne na zagi a cikinsa. Dukka mawallafin yana yin hakan ne don ya bayyana yadda karuwai suke gudanar da rayuwarsu.

2.0 Kammalawa

A wannan bincike da aka gudanar an nazarci salon fanɗarewa a cikin littafin ‘Yartsana wanda Ibrahim Sheme ya rubuta. A binciken an gano ire-iren salon fanɗarewa guda biyu: salon fanɗarewa a ɗaiɗaikun kalmomi da kuma jumlataccen salon fanɗarewa. A ƙarshe dukkansu aka gano suna da wasu nau’o’i guda uku-uku. Nau’in salon fanɗarewa na ɗaiɗaikun kalmomi ya ƙunshi: na zagi da batsa da kuma na miyagun ayyuka. Wasu daga cikin kalmomin da aka gano mawallafin ya yi amfani da su a salon fanɗarewa na zagi sun ƙunshi ashariya ne kamar haka: kutumar uba da shegiya da kuma ‘yar iska. Kalmomin da aka gano mawallafin ya yi amfani da su na batsa sun haɗa da: nononta da zindir da gorunan madara da sauransu. Ta fuskar miyagun ayyuka kuwa an gano mawallafin ya yi amfani da kalmomi irin su: shaye-shaye da karta da karuwanci da sauransu. Idan kuma aka juya ta fuskar jumlataccen salon fanɗarewa kuma, a nan ma an gano mawallafin ya yi amfani da jumloli na zagi da batsa da kuma muzantawa. Dangane da abin da ya shafi zagi, an gano mawallafin ya yi amfani da wasu jumloli kamar haka: shegiya ‘yar buhun uba da kwandon buhun ubanki da shegiya ‘yar Chadi baquwar haure da uban wa ya ce miki ƙona ni za a yi da wane shegen ne ya ce miki mutuwa za ki yi. Ta fuskar batsa kuwa, an gano mawllafin ya yi amfani da jumloli ne da suka haɗa da: “Amma da ya je ya dawo sai ta ga ya saki labulayen tagogi ya rarume ta, ita ko ta shiga ciccijewa da haure-haure na nuna ƙin amincewa da shi” da “A nan dai ya yi amfani da ita, ya ƙosar da kansa daga ni’imar da Allah ya yi mata” A ƃangaren nau’in jumlataccen salo na muzantawa kuma, an gano mawallafin ya yi amfani da jumlolin ƃantanci ne kamar haka: “wai ina ruwan mokaɗaɗɗiyar algungumar nan da ni ne har take shiga harkoki na” da “idanun nan nasa kamar mujiya a cikin bokiti”. Daga ƙarshe dai waɗannan misalai da aka kawo na sama sun fito mana da ire-iren wannan salo na fanɗarewa da ake magana akansa a cikin littafin da aka nazarta.

Manazarta

1.       Abdullahi, B. (2014). “Kwatanta Salon Harshe a Littattafan. Wani Hanin Ga Allah da Na Budurwar Zuciya”. Kundin Digiri Na Biyu (M.A) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

2.       Ado, A. (2019). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina: Government Printing Press, Bugu na Ɗaya.

3.       Binta, A. (2014). “Kwatanta Salon Harshe A Littattafan Wani Hanin Ga Allah Da Budurwar Zuciya” Kundin Digiri Na Biyu (M.A) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

4.       C.N.H.N. (2006). Кamusun Hausa Na Jami’ar Bayero, Zaria Nijeriya: Ahmadu Bello University Press Limited.

5.       Haruna, K.D. (2014). “Nazarin Salon Harshe a Littattafan Tsumagiyar Kan Hanya na Musa Mohammed Bello da Zavi Naka na Munir Mamman Katsina”. Kundin. Kundin Digiri Na Biyu (M.A) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

6.       Kukuri, A.B. (2015). “Kwatanta Hoton Gurbi da Aiwatarwa Tsakanin Littafin Mace Mutum da Baƙin Kishi”. Kundin Digiri Na Biyu (M.A) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

7.       Kenzietorpy.blogspot.com/2014/10/high-middle-and-low- style. html? m

8.       Muktar, I. (2010). Jagoran Nazarin Кagaggun Labarai. Kano: Iya Ruwa.

9.       Mujaheed, A. (2021). “Aminu Alan waƙa a Fagen Rubutattun Кagaggun Labarai na Hausa”. Algaita: Journal of Current Research in Hausa Studies Vol.14, No, 1. pp`173-183 Kano: Department of Nigerian Languages, Bayero University.

10.    Mu’azu, A. (2006). “Tasirin Baqin Al’adu a Qagaggun Labaran Soyayya na Hausa”. Kundin Digiri Na Uku (Ph.D) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

11.    Mustapha, A. S. (2018). “Karin Maganar Hausa: Nazarin Salo” Faculty of African Postgraduate Studies, Department of African Langauges, Cairo University.

12.    Marafa, N.I. (2016). “Кaddara da Tasirinta a Кagaggun Littattafan Gasar Hausa na 1933.” Kundin Digiri Na Uku (Ph.D) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

13.    Nafi’u, A.M. (2012). “Magana Jari Ce 1-3 Nazarin Salo da Sarrafa Harshe” Kundin Digiri Na Uku (Ph.D) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

14.    Newman, P. da Roxana (2020) Ƙamusun Hausa: Hausa-Ingilishi/Ingilshi-Hausa Kano: Bayero university Press.

15.    Salihi, T.M. (2020). “Kwatanta Littafin Kitsen Rogo da Jatau na Kyallu Dangane da Dabarun Jawo Hankali”. Kundin Digiri Na Uku (Ph.D) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

16.    Saleh, Z.U. (2013). “Nazarin Rukunan Aikatau a Littafin Ruwan Bagaja da Amadi na Malam Amah ta Fuskar Ginin Jumla”. Kundin Digiri Na Biyu (M.A) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

17.    Suleiman, (2005). “Nazarin Dabarun Bayar da Labari a Littattafan Dare Ɗaya (1973) da Budurwar Zuciya (1987) na ɗaya”. Kundin Digiri Na Biyu (M.A) Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

18.    Sulaiman, A.I. B/S Course Guide. Hausa Literary Criticism. National Open University. Department of Languages Faculty of Arts.

19.    Sheme, I. (2003) ‘Yartsana. Kaduna: De Young Printers.

20.    Xiaomeng, S. (2013). Rubutaccen Wasan Kwaikwayo a Rukunin Adabin Hausa: Haƃakarsa da Muhimmancinsa Kano: Gidan dabino Publisher.

21.    Yahaya, I.Y. (1988). Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce – Rubuce Cikin Hausa. Zaria: N.N.P.C.

22.    Yahaya, da Ɗangambo (1986). Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: N.N.P.C.

23.    Yahaya, U. (2016). “Salon Amfani Da Lokaci A Littafin Tauraruwar Hamada Na Ahmad Daura” Center For Research in Nigerian Languages,

24.    Yahaya, I.Y. da Wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare Na Ɗaya (1). Ibadan: University Press Plc.

25.    Yahaya, U. (2021). “Nazarin Salon Amfani da Magana da Dalilansu a cikin Littafin Amadi na Malam Amah na Magaji Ɗambatta” Yobe Journal of Language, Literature and Culture vol: 9 No 1 pp108-118.

26.    Yahya, A. B. (2016). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Post a Comment

0 Comments