Ticker

6/recent/ticker-posts

Nan Ko Kudu Ba Abun Da An Nan Ba Azna...

.. Nan ko Kudu ba abun da an nan ba azna..

.... Nan ko Arewa Na Yakuba na ga Jan Gwarzo..

.... Yamma Tutam Mujaddadi ɗai ta ah Hausa...

.... Gabas ɗakin Kaaba shi muke tcinka don haske...

..... Da imanin Shehu yai tudu, Ummaru  yad daho...

Waɗan nan ɗiyan waƙa dake cikin Bakandamiyar Malamin Waƙa da ya yi wa Marigayi Mai girma Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba na ƙara bayyana nason Hijira da Gwagwarmayar Fulani Alibawa na Zurmi da Ƙaura Namoda da Moriki  a Jihadin jaddada addinin musulunci wanda Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya jagoranta a Daular Usmaniya a cikin ƙarni na 19.

Kafuwar Daular Usmaniya da hedikwata a Sakkwato ne ya ke nufi da "Nan yamma babu kowa Tutam Mujaddadi ɗai ta ah Hausa.. watau kenan Daula ta Musulunci ta kafu har ma an yi hedikwata a Sakkwato (ita ake kira Hausa saboda sabon matsayin da ta samu na jagorantar dukan lamurran Daulolin Sarauta na Hausa irin su Gobir da Kano da Katsina da Zazzau da sauransu).

Ya kuma bayyana abubuwan da ke akwai a sauran sassa na Daular : Kudu da Arewa da ma gabas inda ya nuna "Ɗakin Kaaba shi  muke dubi don haske.. Watau saboda hasken Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, mu da ke wannan yanki na duniya Kaaba ce muke fuskanta mu bayar da farali na Sallah da sauran matara kama na Addinin Musulunci wanda ya bayyana cewa yin tuwassuli da  mubaya'a ga Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da Jagororin wannan Masarauta ta Ƙauran Namoda suka zamo abun tink'aho ga na bayan su. Allahu Wa'alam!.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments