Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Yi Alƙawari Zan Aure Ta, Sai Iyayena Suka Zaɓa Mini Wata, Mene Ne Mafita?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Dafatan Allah ya yi mawa wannan group albarka tare da karin ilmi ga malamin mu. Tambayata itace meye hukunchin mutumin da yake soyayya da wata mace bayan ya mata alkawarin aure kuma sai iyayensa suka zabar masa wata macen daban don ya aure ta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumasalam warahmatullahi wabarakatuh.

 Alhamdulillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.

Da farko dai kulla alaƙa ta soyayya da wata mace  irin wanda akeyi a wannan lokaci  bai halatta ba ko da kuwa da niyyar aure ne, dalilan kuwa sune;  Hakan yana haifar da kalamai masu mattuƙar gaggauta faruwar ɓarna ta hanyan magana ta waya, chatting, sakon katta kwana sms, kallo, taɓa jikin juna wasu lokuta har da zina ko kuma mafi karanchi yaudaran juna.

Wannan bai hallata bah idan mutum ya yi haka batare da neman iznin auren ta ba, yin  hakan wata irin salo ce ta yaudaran abokin alaƙa.

Idan muka ɗauka bisa ga kaddarawa shi wannan saurayi ya barta neh saboda yin biyayya ga iyayensa to mai yasa ya yi mata alkawarin aure tunda ya san cewa ba shi yake da cikakken iko da kansa ba game da al'amarin samar ma da kansa  matar da zai aura?

Hukunchi wannan mutumin hakika ya faɗa cikin kananan alamu na munafinci, saboda ya nuna dabi'a irin ta ƙarya, karya alkawari, tare da yaudara, waɗannan duka kananan alamune na munafinci kamar yadda yazo a cikin hadisin manzon Allah : An karbo daga abu hurairah " manzon Allah tsira da aminchin Allah su tabbata a gareshi yace ayoyin munafiki guda uku neh idan zaiyi magana zaiyi karya, idan ya yi alkawari sai ya karya, idan aka yarda da shi sai ya ci amana"

A karshe yakamata ya ma iyayensa bayani a buɗe cewan ya yi wa wata macen alkawarin aure, idan sun amince Alhamdulillahi, idan kuma basu amince ba sai ya auresu duka biyu. Idan ko bahaka ba Allah mai girma da daukaka zai iya yimasa hukunci ta hanya da bai taɓa zato ba.

Allah shine mafi sani.

Amsawa

Malam Aliyu Masanawa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments