Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Auren Kashe Wuta.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne hukuncin auren wanda yasaki matarsa saki uku, sannan yasa wani ya aure ta yasaketa domin yasake aurenta tadawo gidansa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله والصلاة والسلام على أشراف الخلق الله.

Idan mutum yasaki matarsa saki uku, ba za ta sake zama halal agareshi ba harsai wani ya aure ta, Aure na kwadayi bawai Auren kashe wutaba, Sannan suka rabu da ita, saboda fadin Allah madaukakin Sarki a cikin Suratul Baƙara ayata (230):

فَإِنْ طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُ مِنْ بَعْدُ حَتَّىٰ تَنْكِحَ زَوْجًا غَيْرَهُ ۗ فَإِنْ طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا أَنْ يَتَرَاجَعَا إِنْ ظَنَّا أَنْ يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ ۗ وَتِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ

Sa´anan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima´i da wani miji waninsa. Sa´anan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cewa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.

Abu dauda yaruwaito hadisi (2076) Annabi Sallallahu Aaihi wasallam ( ya tsinewa mai Auren kashe wuta, dawanda ya aura danta halatta gawanda yasaketa).

Albani Ya Ingantashi A cikin sahihu Sunan Abu dauda.\

Haramunne da mijin farko suka hada baki banda sanin daya mijin, ko matar da mijinne suka hada baki banda sanin ita matar, Malamai Sunyi Saɓani Amma ingantacciyar magana shi ne kota wacce hanya akayishi haramunne.

Shaikul Islam Ibnu taimiyyah ya ce: " Hasan da Naka'iy suka ce: idan daya daka cikin ukun yabada himma to Auren kashe wutane, mijin farko dana biyun da ita matar, An ruwaito haka daka Ibnul Musayyeeb, lafazin Ibrahimun naka'iy: idan niyyar daya daka cikin Su ukun ( Mijin farko, kona Biyu, ko matar) Auren kashe wutane, wannan nakarshen bataccene ba za ta halatta ga mijin farkon ba....

Fatawa Kubra na Shaikul Islam ( 6/298)

Domin Samun cikakkun bayanai a kan hakan duba " Madalibu Ulin nahayi (5/127) da Al-Mugny " (7/139 " da " Kashshaaful Ƙina'i" (5/96) da " Hashiyatu Dasuƙy " (2/258),  Da I'lamul muwaƙƙe'iynah (4/36)

Saboda haka wannan Aurene batacce kuma bata halatta ga mijinta nafarko ba, kuma kaba'irane cikin manyan zunubai.

Zata halatta agareshi ne kaɗai idan miji nabiyu abisa radin kansa yanemi Aurenta, harsai yadan-dani dadinta ta dan-dani dadinsa sunzauna sosai, randa Allah yakawo musu rabuwa suka rabu, idan mijin farko yaga haryau yanada Bukata a kanta saiya aure ta tadawo wajansa.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments