Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsayin Cin Amana A Musulunci

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Kana Cin Amanar 'Yan Uwanka?

Ga Illolin Cin Amana Da Manzo (S.A.W) Ya Ambata...

1. Cin amana yana daga cikin halayen munafurci. Manzon Allah (S.A.W) ya lissafta wasu halaye guda uku, ya ce duk wanda yake da su a cikin halayensa, to hakika shi munafiki ne. Koda ya yi sallah ya yi Azumi, koda ya yi Hajji ya yi Umrah, koda ya ce shi Musulmi ne (Subhanallah).

2. CIN AMANA yana daga cikin abubuwan da suke tauye imanin mutum. Matukar mutum zai rika cin amanar mutane, to kullum imaninsa raguwa yake yi.

 3. CIN AMANA yana daga cikin halayen da suke kaskantar da darajar mutum a wajen Allah. Matukar mutum bai rike amanar bayin Allah ba, to Allah ne zai zama abokin rigimarsa a ranar alkiyama (Subhanallah).

 4. CIN AMANA yana sanya mutum ya yi bakin jini a cikin al'umma, darajarsa da mutuncinsa su zube, sannan kuma al'umma su rika gudunsa.

5. CIN AMANA yana zama sanadiyyar dulmiyar mutum cikin wutar jahannama. Kamar yadda ya zo a cikin hadisi, Allah zai sanya amanar a cikin can kasan wutar Jahannama, sannan a umurci maciyin amana cewa ya shiga ya dauko ta. Sai ya dauko ya hauro wani babban tudu, sannan sai ita kuma amanar ta subuce ta koma can kasan ramin Jahannama. Sai Mala'iku su daka masa tsawa su ce ya koma ya daukota. Haka zai yi ta yi har illa masha Allahu.

 6. CIN AMANA yana zubar da albarkar dukiya. Domin kuwa komai yawan kudi, in dai aka cudanya shi da kudin cin amana sai ya lalace.

Yaku Jama'a!!! Ya zama wajibi mu rika kiyaye amanar junanmu don samun mutunci a wajen Allah da bayin Allah.

Allah y asa mu dace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W).

Post a Comment

0 Comments