Ticker

6/recent/ticker-posts

Gamshe

Gamshe ciyawa ce mai kyau musamman a wajen masu kiyon dabbobi

Gamshe tana cikin ciyawa da doki ya fi daso fiye dakowace ciyawa awajen ƙotonsa

Gamshe ciyawa ce dabaka samunta a kan sahara sai dai a fadama wajen da ke da Dausayi musamman bakin Tafki ko korama ko kuma bakin kogi/rafi

Gamshe ciyawa ce gwanin sha'awa za ka same ta tsanwa shar/koriya,

Gamshe takan yi ƙonshi ya fitar da kai fari idan ya ƙosa kaman kansu kusan ɗaya da kan rake, sai dai kansa bai kai na rake girma da fadi ba, amman duk kansu fari fat maikama daya.

Gamshe ciyawa ce da Doki yake ci sosai amman dabbobi kaman su shanu da tumaki da awaki da jakai da rakomi Duk sunacin Gamshe

Yakan fito ne a lokacin damina idan rani yakama yakan chanza kala daga tsanwa/kore zuwa ɗorowa  ɗorowa dagan nan dai idan rani yayinisa yabushe ƙomomus

Gamshe masu dabbobi sukan yanki ciyawa Gamshe da damina suke baiwa Dabbobinsu idan rani yayikuwa sukan rinka tonon sayyunsa akaima dabbobin da muka ambata asama

Gamshe kunnuwansa tsanwaye ne/koraye karansa kuma yanada ga'ba ga'ba, kaman karan gero ko Dawa, ko wata ciyawa da muke kira da suna ILLiri, kunnuwansa da ga'bo  'binsa tsanwaye ne/koraye sai dai Sayyunsa farare ne fat

Gamshe sayyunsa sunada zaƙi zaƙi, hakama karansa, sai dai kunnuwansa sukan yanka mai aikin yankansa kaɗan kaɗan saboda sunada dan kaifi

Gamshe akansame shi acikin fadamar kanwa ta gefen yankin Gobirawa, Sabon birni L/G Sokoto State, takan yuyu asameshi acikin fadammu dayawa a kowane yankin,

Gamshe muke kiransa a namu yankin takan yuyu wasu sukan kira shi da wani sunan daban ba Gamshe ba.

Gamshe

Daga Taskar

Mai Girma Sarkin Rafin Gobir
Mai Girma Isma'il Muhammad Yusuf

Post a Comment

0 Comments