Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko Wac Ce Za Ya Ba Ka

Ko Wac Ce Za Ya Ba Ka

"Kowac ce za ya ba ka,
Ka bi shi kamab bita zai yi ma,
Al'amarin duniyag ga sai Allah Ɗan Tumba Rungumi" 

Inji Makaɗa Sa'idu Faru, Maradun, Jihar Zamfara a cikin Waƙarsa mai amshi 'Gwabron Giwa Uban Galadima ɗan Sambo ginshimi, gamshik'an Amadu na Maigandi kai Uban Zagi' wadda ya yiwa Marigayi Dagacin Banga, gundumar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar (ya yi Sarauta daga shekarar 1934 zuwa rasuwarsa a cikin 1960s). Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments