Ticker

6/recent/ticker-posts

Kucaka

Na lura ƙwarai da gaske

Ba kucaka duk a mata

Sai wadda ta maida kanta

Gantalalla wadda kullum

Ita ce ɗakin samari

Ƙafa tata ta fitsare

Akuya ta mai da kanta

Toka ta sa idonta

Dangi ba mai kwaɓarta

Don gudun haushi da cizo.

 

Tambari duk taiwa kanta,

Daraja tata ta zubarta

Kurma ta maida kanta

Bata son wa'azi nasiha

Ita nan ai tayi 'yanci

Ilimin boko wajenta

Yasa bata sana'a

Sai bin ofis abokai

Na karatu wai su ba ta

Kwangila Naira ta samu.

 

Meeting kullum takan ce

Zata je domin a bar ta

Tai ta shawagin ta cafke

Gantalalle mai fasadi

Su je otel su hole

Burinta kawai ta watse.

 

Mijin aure na gaske

Taƙi fiddawa a bata

Buri kullum takan yi

Sai mai Naira ta aura

Domin son zuciyarta

Duk ta tsofar da kanta

Yawon ofis Abuja

Jari wai sai su ba ta

Ta je ta Dubai da niyyar

Yin fatauci har fa Chana

Ta ƙi yin aure ta raya

Sunnan Manzo Aminu.

 

Sai randa ta tsinki kanta

Ta zan guzuma a loko

Ba sauran mai taya ta

Sai ka ganta cikin hijabi

Ita ce kullum da carbi

Wai ita yau ta bi Allah

Tana neman na aura

Miji ko bai da Naira.

 

Ke kucaka da ki gane

Rayuwarki taƙi kaɗan ce

Ki tuba ki kama Allah

Tun da sauran lokacinki

Ni Imam Khalid da gaske

A yau na gargaɗe ki

Ki buɗa ido ki lura

Ba rabo sai an bi Allah

Babu dacewa da riba

Sai a layin raya Sunna.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments