Ticker

6/recent/ticker-posts

Illar Kwashe-Kwashe

Lokacin da a da iyaye,

Su ke aurar da 'ya'ya,

Lokacin wallahi Allah,

Auren da yawa a baya,

Ya yi danƙo ya yi ƙarko.

 

Amma da yawa mutane,

'Yan boko ma su gilli,

Masu sharri a zuciyarsu,

Sun ce sun tauye haƙƙi,

Kuma wai sun zo da ɓarna.

 

Duk da mata lokacin can,

Daraja wallahi sun yi,

Sun mutunci sun yi ƙima,

A ido na miji da dangi,

Rayuwar jiya na da daɗi.

 

Sai ga shi a yau a fili,

Matan ne su da kan su,

Su ke talla da kan su,

Suna neman mazaje,

Ba mutunci babu kunya.

 

Masu ma har shela ke yi,

Don Allah don Ma'aiki,

A ba su miji su aure,

Har lefe za su yafe,

Sun gane gaskiya yau.

 

Dama ƙarshen alewa,

Ƙasa ni ban musawa,

Al'adu masu kyawu,

Mun watsar mun bi gaibu,

Rami mun jefa kanmu.

 

Yau mata don takaici,

Wasu sun maishe da kansu,

Akuyoyi ba su kunya,

Ko karuwa da sanina,

Tana kunyar iyaye.

 

Don ba ta karuwanci,

A gidansu gaban iyaye,

Amma da yawa wasunmu,

A gidansu su ke baɗala,

A idon dangi iyaye.

 

Shawarata ni gare mu,

Ɗabi'un can na dauri,

Mu dube su da kyau a yanzu,

Mu daina biye wa gangan,

Mu bar yin kwashe - kwashe.

 

Dubi illar kwashe - kwashe,

Na al'adu na Turai,

Da Indiya ko ƙasar Sin,

Sun kai mu sun baro mu,

Babu gaira ba dalili.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments