Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsokaci Game Da Masu Sarautar Bunguɗu

Masu sarautar Bunguɗu jinsin Fulani ne da ake kira 'Kasarawa' da suka fito daga Katsina. Sun samu wannan laƙabin na 'Kasarawa' ne bayan sun fito daga Katsina kafin su kawo inda suke yau sai suka yada zango da dabbobin su a wata Ƙorama da ake kira 'Kasara' dake cikin Masarautar Zurmin Jihar Zamfara ta yanzu inda daga nan suka 'Bunguɗo'  da dabbobin su zuwa inda suke a halin yanzu. A lokacin wurin ya na karkashin mulkin Sarkin Gobir Malam Ummaru Bawa Jan Gwarzo ɗan Sarkin Gobir Ibrahim Babari ɗan Sarkin Gobir Ashi/Ashe a cikin ƙarni na 18 wanda shi ne ya aminta dasu zauni wannan wurin har ma ya naɗa Jagoran su Malam Muhammadu Ɗan Zundumi a matsayin "Arɗo" daga baya laƙabin Sarautar ya canza/canja ya zuwa "Sarkin Fulani" da suke amfani da shi a yau.

Ƙila wannan dangantakar ce dake tsakanin gidan Mujaddadi da gidan Malam Muhammadu Ɗan Zundumi da kuma girmamawa tsakanin Malami da Ɗalibin shi ta sanya Marigayi Mai girma Sarkin Sudan na Wurno murabus, Alhaji Shehu Malami ya sayi mota ƙirar Marsandi Benz ya baiwa wanda aka yi ma wannan Waƙar (Ɗanmadamin Sakkwato). Ɗanmadamin Sakkwaton ya karantar da Sarkin Sudan a Middle School, Sokoto. Domin nuna girmamawa rana ɗaya ya yi odar irin wannan motar guda biyu, ya baiwa matar shi (Matar Sarkin Sudan, Hajiya Asma'u yar Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba ɗan Magajin garin Sakkwato na 9 Shehu ɗan Magajin garin Sakkwato na 5 Muhammadu ɗan Magajin garin Sakkwato na farko, Jikanyar Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato a wajen Mahaifiyar ta) guda ɗaya, ya baiwa Malamin nashi, Ɗanmadamin Sakkwato guda ɗaya kyautar Allah.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments