Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Kammalawa
Hausawa dai na cewa “komai nisan
jifa ƙasa za ta faɗo”. Wannan zance ne mai nuna an zo ƙarshen
wannan aiki nawa mai taken “Bara Da Mabarata A Ƙasar Hausa”. Aikin ya tattauna abubuwa muhimmai da suka shafi al’amarin
bara. Da farko an gabatar ma’anar bara kamar yadda wasu jama’a suka samar tun
daga gida har zuwa wajen ƙasar Hausa, sai
hakan ya zama hujjar da aka kafa domin ingancin gudanar da shi.
An kawo nau’in mabarata da waɗanda ake yi wa bara da yadda ake aiwatar da waƙoƙin a wajen yin bara.
An bayyana falsafa da sigogin waƙoƙin baran masu bambanta su da sauran waƙoƙi da ba na bara ba. Ta fuskar falsafar waƙoƙin aka fito da wasu ɓoyayyun manufofi da waƙoƙin ke nuni zuwa gare su, kamar ƙimar mabaraci da dangantakar almajiri da mata da da irin halayyar da ya kamata a ce mai bara ya sifantu da ita, da sauran irinsu.
Bayan wannan an dubi jigogin waƙoƙin bara waɗanda mabarata ke bara da su a ƙasar Hausa. Bayan faɗin ma’anar jigo kamar yadda manazarta suke gani, sai kuma aka ci gaba da fito da jigogin ɗaya bayan ɗaya, kamar su fatar alheri da ban tausayi da ƙasƙan da kai barkwanci, da nishaɗantarwa da sauran matara kama da su.
Daga nan kuma an dubi salon waƙoƙin. An dubi salon sarrafa harshe da ake samu a cikin waƙoƙin kamar sifantawa/kinaya da kamance da jinsantarwa da alamci da zayyana da sauransu. Haka ma an dubi zubin waƙoƙin ta amfani da ra’in Gusau (2003), aka dubi awon baka wanda ya shafi zubin ɗiya da tsarin ɗiyan waƙa. Har ila yau an dubi karin waƙoƙin aka yi amfani da kowanne daga ra’i biyu, wato Gusau (2003) da Dunfawa (2003). Daga ƙarshe aka kawo Jawabin kammalawa wanda ya taƙaita abin da aikin ya ƙunsa tun daga farko har zuwa ƙarshe tare da ambaton sakamakon aikin, wato abubuwan da aikin ya fito da su ga masu nazari.
A lokacin
gudanar da wannan aikin na gana da mutane daban-daban tun daga almajirai da
sauran mabarata da kuma masu ruwa da tsaki a kan sha’anin bara akwai wani
almajiri Sanusi Zawiyyar malam Murtala, Gusau Mal.
Isah Bala Homawa F.C.E.(T) Gusau, Jihar Zamfara da Alhaji Ibrahim Waziri, Ɗan Bedi Birnin Ruwa Gusau, da Malam Shanwilu, Makarantar
Malam Mu’azu, Gangaren maƙabarta Gusau, da sauran wasu manyan masana irinsu Farfesa Aliyu Muhammad
Bunza da Alhaji Sharif Sulaiman Bunguɗu da Dokta Ibrahim Sarkin Sudan Abdullahi da sauransu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.