Koda yake muna maganar alamu ne da yadda ake ganewa mace mai mummunan kishi, sai dai wannan ba zai hana mu tabo babban abin da yake fito da alamomin a baina ga jama'a ba. Duk lokacin da mace ta fara ganin cewa wata ta fi ta wani abin, kuma akwai yuwuwar ta hada hanya da ita matsala ta samu, misali tana tsoron ta fada idon mijinta ne, sai aka yi sa'a tana da miji da yaranta a gabanta, wannan ba za ta zama ƙalu bale ba ba ta da matsala da ita, ko maigidanta na son farar mace ne, sai wannan ta zama baƙa kuma tsohuwa, ita ma hankalinta zai kwanta tunda tana da tabbacin ba za ta zama mata ƙalu-bale ba anan gaba.
Amma in ta taras da cewa fara ce, matashiya kuma ba ta da miji, ko maigidanta bai ce yana so ba, bai yi wata magana dangane da ita ba za ta fara tunanin cewa nan gaba fa za ta iya samun wurin zama a zuciyarsa, sai ta fara yi mata wani irin kallo, sai soke-soke, duk abin da za ta yi zai zama abin da za a yi magana a kai. In tadan yi magana za ta ce da mijinta take yi, ko shuru ta yi sai ta ce yanzu haka tunaninsa take yi.
A wani nazari da aka aiwatar a Mujallar
"Gender in Management" a shekarar 2009 wanda nazarin ya maida hankali
kan yadda mata kan ƙi junansu masamman a wurin aiki. Sakamakon ya nuna
cewa mace ko kadan ba ta so a ce 'yar uwarta mace ce ke shugabantarta, akwai
tunanin cewa matsayinsu guda ne kamar yadda suke a gidan miji, ita kuma
shugabar za ta yi ƙoƙarin nuna cewa ba haka ba ne a aikace wanda
sakamakon hakan zai nuna mugancinta da rashin tausayinta. Ko ba don haka ba ma
ba abin da 'yar uwarta mace za ta yi na kwalliya ta sami abin da take so a
wurinta, dole ta ƙi ta.
.
8} In aka lura galibin mummunan kishin dake kai
mace ga ƙiyayya lullube yake da suka ta fuskoki daban-daban, yau ta yi kaza gobe ta
yi wani abin daban, da wahala a sami inda za ta yabe ta. Duk lokacin da mace ta
yi niyyar yin kishi da 'yar uwarta za ka ga ta kawar da kanta daga duk
alkhairanta, so take a fito da inda take da rauni, in ma wani ya fara fado
kyawawan halinta takan yi shuru a inda ba za ta iya cewa komai ba, ko in ta
sami dama ta ce ba haka ba ne, wannan kam mummunan kishi ne.
.
9) Sa ido: Wannan ma wata alama ce da ake gani,
yadda duk abin da maigidan zai yi da wahala ka ga ba ta sani ba, labari ake ba
ta? Wasu ta saka su riƙa yi mata aiki? Kamara ta saka ko me ke faruwa
Allah ne masani. A baya a kan wannan mun yi maganar daukar waya, ƙari a
kansa in maigidan zai daga waya ko tana nesa sai ta zo wurin duk da za ta iya
ji daga can, ƙoƙarinta ta saka masa ido ta karanci abin da yake
fuskarsa a lokacin da yake maganar.
.
Wasu lokutan ma takan tambayi sunan wanda ake
maganar da shi ta yi ƙoƙarin sanin ko shi waye, bayan maganar ba ta shafe
ta ba sam, to bare kuma a ce da mace ake yi, wata tana da ƙwarin gwiwar da za ta
tambaya ko matar da ake magana kanta tana da aure ko ba ta da shi, shekarunta
nawa? Yaranta nawa? Duk fa a maganar da ta sami ana yi a waya ne wace samsam ba
ta shafe ta ba. Da a ce za a gaya mata abin da take son ta ji, za ta yi ƙoƙarin
sanin inda take zaune da alaƙarta da maigidanta.
.
Matsalar da za ta ji wani abin ba yadda ta so ba
shi ma wata matsalar ce ta masamman, ranta zai baci, duk lamuranta zai dawonan
ta fara wani binciken wanda kowa sai ransa ya baci, ita da maigidan nata, shin
sonta yake ko me? Sabuwar matsala ta shuku kenan, za ta ce yana magana da
'yanmatansa ko zawarawa a gabanta. In zai fita ya dauki waya ta ce "Ina
kuma za ka da waya? Za ka je ne ka buga mata a waje?" Alla-alla take wani
ya bugo masa waya tana kusa da ita ta ga sunan wanda ya bugo din, namiji ne ko
mace?
.
In kuma ya ji hayaniya ya yi yawa ya dan matsa
gefe shi ma wata matsalar ce ta daban: Me ya sa ya matsa din? Yana maganar
soyayya ne da wata? Me ya sa ba ya so a ji abin da suke tattaunawa?
10) Alama ce ta baƙin kishi idan ka ga ma
ce ba ta so a yi maganar wata, ko da kishiyarta ce kuwa bare wata? Ana kama
sunanta ma sai ta bata rai, a nata ganin maigidan bai isa ya kama sunan
kishiyarta ba, ba zai yi magana da ita ba matuƙar yana gidanta. Bayan
kuma ta san cewa ita ma matarsa ce.
A Nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.