6) Taimako: Kowa dai ya san ƙauna ke kawo taimako amma baƙin kishi ma kan kawo irin nasa, sai dai a kan same shi ne a inda bai kamata ba, ya zama na banza kenan, galibin kiyoshin da ake kawo su suna yara ƙanana ba su gama sanin duniya ba su suka fi fadawa wannan matsalar, yadda kishiyarta za ta ba ta shawarar yadda za ta gina gidanta, ko yadda za ta tafiyar da maigidan da sauran 'yan uwansa, alhali ita ba haka take yi ba. Hatta yadda za ta dafa abinci da wadanda za a ba su da gwargwadon rabonsu takan nuna mata.
Wannan abu ne mai kyau kuma ta taimaka mata, sai
dai abin da yake boye in ka bincika sai ka taras ko dai gwargwadon da ake ba su
ya yi kadan, kuma za su yi ƙorafi ga maigidan su zarge ta da yi musu ƙoro,
ko kuma ta kamfata musu yadda ran maigidan zai baci ya zarge ta da
almubazzaranci. Abin da ke maganin irin wannan in amaryar ta fara jin cewa wasu
abubuwan ba sa tafiya daidai ba zargi za ta yi ba, sa ido za ta yi ta ga yadda
ake yi ita ma ta tafi a hakan, kar ta ce wani abu bare a ce ga abin da ta ce,
kuma ba ta bude ƙofa ta tashin hankali ba tsakaninta da abokiyar
zamanta.
.
Babban abin da ke da ban haushi shi ne lokacin da
mace ke nuna tana tare da kishiyarta, kuma tana taimakonta ne don Allah, amma
idan wani abu ya faru wanda ya kamata a ce ba wanda ya sani daga maigidan sai
su, sai a ji shi ya fito ta bakinta, wai ta kai ne da niyyar gyara, gashi dai
kamar taimakonta take so ta yi, amma ba haka abin yake ba, so take a san
ainihin abin da kishiyarta ta yi ne don baƙinta ya bayyana. Tana
sane cewa ba a son maganar ta fita, ita kuma sai da ta kintata yadda za ta yadu
kafin ta fitar da ita, wannan ma mugun kishi ne amma na boye.
.
Akan gane irin wannan kishin ne a lokacin da aka
ga tana yin wasu abubuwan ba tare da sanin kishiyarta ba, asali an bar abin a
boye amma sai ta je ta yada maganar ba wanda ya sani, ta kuma san tasirin da
zai yi wa kishiyarta in maganar ta fita, to bayan ta yi duk abin da za ta yi,
ta san asiri zai iya tonuwa a kowani lokaci a ce ga wace ta fada sai ta dawo ta
fara yi wa abin kwaskwarima yadda zai zo da sauƙi. A duk inda ta sayar
da labarin zai yi wahala ta nuna rashin laifin kishiyar, sai dai ta ce kuskure
ne ba da gangan ta yi ba amma abin da ba a so tabbas ta aikata, a ƙarshe
ba ta so a ce ita ta fada don kar maganar ta kawo tashin hankali.
.
Amma tun farko me zai hana ta tsaya su tattauna da
kishiyar, su magance abinsu a cikin gida? In ma za ta fitar da maganar don me
ba ta tuntube ta ba tukun ta ji ko ranta ba zai so ba? Sai da ta aikata abin da
take so sannan za ta dawo ta gaya mata? Bayan kuwa in ita ce ta yi wani abin
kishiyar ma ba za ta sani ba bare har a kai ga cewa maganar za ta fita ko ba za
ta fita ba? Jan kunne kishiya kan cewa ta daina fada mata lamuranta ba mafita
ba ne amma ta san me ya kamata ta fadi? Wani abu ya dace ta boye?
.
7) Ƙiyayya: Wannan ya fi bayyana, domin in kishiya ta
nuna wa abokiyar zamanta cewa ba ta son ta ka ga ga za ta san matakin da za ta
dauka a kanta, za ta karanci yadda za ta zauna da ita sosai, sabanin yadda za
ta boye mata ta dauke ta a matsayin masoyiya. Kishi wanda aka san mata da shi
abu ne dake jininsu ba yadda za ka raba su da shi, ko Turawan da ake kira ba su
da shi mazan ne, a duba haukar da matan ke yi idan suka kama mazansu da wata
macen. Amma abin da muke ƙoƙarin fitowa da shi anan shi ne masifaffen kishi,
ko baƙin kishi, ko mummunan kishi, duka dai abu daya ne. Kishin da zai sa mace ta
yi abin da zai saba wa hankali ya kai ta ga son cutar da abokiyar zamanta ya
zama mummuna.
.
Wani abu mai kama da ƙiyayya kan faru tsakanin
wata macen da mijinta idan ta ji ko ta ga cewa zai ƙara aure, takan mayar da
abin muguwar ƙiyayya tamkar ba a taba yin wata soyayya a baya
ba, a kan kai ga yadda za ta ce baƙinsa take gani, ko ba ta son ta ji an kira sunansa
gaba daya bayan a gidansa take, abincinsa take ci, aurensa take yi, babban
dalili shi ne ya yi niyyar ƙara wata matar, irin wannan ba a samun mafita sai
ta bar gidan, abin takaici ma ƙila shekarunta sun kai yadda zai yi wahala a sami
saurayin da zai aure ta sai dai ta auri mai matan in za ta ƙara
yin aure nan gaba.
.
Idan kuma ta sami labarin cewa yakan tafi zance da
wani abokinsa to sun sa ƙafar wando daya kenan tare da shi, ya zama
munafuki, ta ƙi shi kenan har abada, bare kuma a ce 'yar uwarsa
maigidan nata zai aura. Irin wannan ƙiyayyar take fadawa a kan macen da aka
auro, zai yi wahala ta ƙi maigidanta a kan zai ƙaro aure sannan kuma ta
so wace za a aura, kodavkuwa ba gida guda za su zauna ba, ƙiyayya ta ƙullu
kenan.
A Nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.