Kishi Rahama Ne Ko Azaba // 48

    3) Haba-haba: ita kanta wannan kalmar ta kasu gida biyu: Akwai ta gaskiya akwai ta ƙarya, to ta ƙaryar muke magana idan ta fito daga mace mai baƙin kishi, kusan gwara ma mace ta nuna ba ta son kishiya kuma ba za ta yi da ita ba, da a ce za ta riƙa haba-haba da ita tana nuna mata ƙaunar da a zahiri babu wace take so ta ga bayanta irinta. Irin wannan kishin in ya hada da ƙaramar yarinya wace ba ta gama sanin kan duniya ba takan ji jiki da ita sosai.

    .

    Don uwargidan kan gasa mata aya a hannu a cikin gida, a waje kuma kowa ya riƙa yaba mata a matsayin tana yin abin ƙwarai. Wani sa'in za ta gasa kishiyar da zarar maigidan ya shigo sai ta janye komai ta nuna yadda take tarairayarta kamar wata diyarta ta cikinta. Na taba ganin kwatankwacin wannan, ko abinci kishiyar ta ƙi sakar wa amaryar, ita take yin komai, sai dai ƙananan abubuwa, ko su din cefanensu sai dai ta karba daga wurin uwargidar da hujjar cewa komai ba ta iya ba, amma in da gaske ne ita uwargidan mai zai hana ta koya mata? Sai kuma ta karbe komai ta riƙe?

    .

    Yadda na karanci rayuwarsu, maigidan ne a sama, da zai miƙa wa uwargidan komai, ita kuma amaryar ba ta da wata alaƙa ta kai tsaye tsakaninta da maigidanta sai ta hanyar uwargidan, ba iyakarta kenan ba, yana sukan amaryar da abubuwa da dama amma uwargidan ce ke nusar da shi don tsabar ƙaunar da ya tabbatar tana yi masa. Haka amaryar ke zaune cikin damuwa da ƙunci, tunda ba ta da ikon gudanar da wani abu a gidan in ba da yardar uwargidan ba, kamar yadda ba ta da ikon tabar komai.

    .

    Irin wadannan matan sukan fito wa mutane da fuska mai kyau a matsayin mutanen kirki, su nuna suna matuƙar ƙaunar kiyoshinsu a zahiri, wani sa'i ma har amana uwayen kishiyar ke bari musu saboda yarda, abin takaici ko'ina ba za a je ba za su ci amanar. Mai dan sauƙi kenan da za ta bar abin tsakaninta da kishiyarta, wata kan hada amaryar fada da kowa, daga minta zuwa maƙwabta da ma uwayenta. Ita za ta kintsa mata abu sai ta aikata ta fita tana zaginta a gari, muguwar kishiya kenan mai azababben kishi.

    .

    4) Daga cikin alamomin da ake gane irin wadannan matan akwai gasa, wannan kowace na yi, uwargidar ce ko amarya, amma bambancin wannan da wace muka fada a baya shi ne wannan kan yi ƙoƙarin cutar da kishiyar don abinta ya sami karbuwa a wurin maigida. A hadisai dai tun zamanin annabawa mun ga yadda wata macen ta kabe abincin kishiyarta, ba wai don ta ƙi jinin kishiyar ba ko don tana son ta saka ta a cikin bala'i, a'a tana so ne a karbi nata, kun ga wannan son kai ne zalla wanda yake lambar farko wajen nuna kishin mace.

    .

    Amma tunda duka matan na yin abinci lokaci guda sukai wa manzon Allah za mu dauka cewa ba a riga an raba kwanaki ba a lokacin, ba kamar mu ne yanzu da kowace mace ita ke yin abincinta a ranarta ta kai wa mijin ba, in irin wannan ya auku yanzu ko shakka babu tsabar baƙin ciki ne da mugun kishi. Ba yadda za ki bata wa abokiyar zamanki abin da za ta kai wa maigidanta a ce kishi ne kawai da za a iya kawar da kai, dole a gyara. Wace ta aikata kuma za ta karbi sakamakon abin da ta yi.

    .

    5) Dariyar ƙeta: Wannan ba ƙyalƙyalcewa ba ce, a'a, mace ta nuna jin dadinta da abu mummuna da ya sami abokiyar zamanta, da za ta yi wani dan kuskure kadan sai ta gaya wa maigidan, idan aka zo daukar mataki ƙila ta iya nuna cewa ba ta ji dadi ba a zahiri amma zuciyarta ya fi nono fari, a kan iya gano wadannan a wasu lokutan, in dai su suka hada rigimar ko maigida na bala'insa ko leƙowa ba sa yi bare su ce ya yi haƙuri.

    .

    Dalili kuwa shi ne idan suka kuskura suka fito kuma ba su ce komai ba kishiyar za ta iya zargin wani abu, in kuma suka nuna rashin jin dadinsu, maigidan na iya juyowa kan wace ta kintsa abin ya tona yadda aka yi don haka sukan yi zamansu a daki shi ne kawai mafitarsu. Wace ba ta boyewa tsab za ta fito ta yi shewa, wata har da guda tana habaici ta mayar da abin da ya faru. Wadannan sun fi dadin sha'ani tunda an san yadda suke kuma cikin sauƙi za a iya fito musu.

    A Nan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.