Kishi Rahama Ne Ko Azaba // 44

    7) Ganin likita. Wani zai yi dariya idan ya ji an ambato maganar ganin likita. Diyata, Manar, ta fara gaya min cewa ita fa tana so ne ta zama likitar ƙwaƙwalwa, na ce ina ta taba jin wani yana ciwon ƙwaƙwalwar da sai an yi masa aiki? Sai ta ce "A! Daddy, Psychiatric fa?" Tunanina bai taba zuwa nan ba, a yadda nake ganinta yarinya kuma ban yi tunanin nan ta nufa ba, sai na ce to Allah ya taimaka. Galibin maza ma muna da buƙatar ganin irin wadannan likitocin daga lokaci zuwa lokaci, bare matan dake da baƙin kishi.

    Kuskure ne a dauka cewa ƙwaƙwalwarsu ras take ba ta da wata matsala, da za a ce kowa ya kawo labarin wata hauka ta kishi guda daya da ya taba gani, wallahi sai an gaji da karatu a wurinnan, ba yadda za a yi mutum ya ce lallai abin da matannan ke yi hankalinsu guda. Wata haka za ta zauna ta yi ta sharbar kuka a yi rarrashin duniyannan a kasa gano kanta, wa ake so ya yi magana da ita in ba likitan ƙwaƙwalwa ba? Akwai wani abu da ta rasa kuma tana buƙatar a daidaita mata shi.

    A lokacin da mace ta ji mutane na fadin cewa ta rage wannan azababben kishin wanda ya fara shiga tsakaninta da wadanda ma a gidanta suke to ta fara duba kanta, a dabi'a in mutum ya sami matsala da wasu a waje na kusa da shi ne za su ba shi kariya. In mace ta yi fada da maƙwabta muna sa rai maigidanta da abokiyar zamanta za su ƙwato ta don ba ta da masoya kamarsu, lokacin da aka ce ba ta ga-maciji da su to ta fara samun matsala tana buƙatar shawarar yadda za ta gyaro lamarinta, ba yadda za ka saba da wanda ya fi kowa kusa da kai ka sa rai da samun zama lafiya.

    Kishi wani abu ne na gasa da ke sa mutum ya fara jin abin da ba haƙƙinsa ba cewa nasa ne, ko kuma shi ya kamata a ce ya mulke shi, ko ya fara jin tsoron cewa lallai zai iya rasa shi ta hanyar wane, don haka wane din ya zama abokin gaba wanda dole a yaƙe shi ta kowace hanya, ko mutum ya ga abin da ke hannunsa bai kai wanda yake hannun wani ba bayan shi ma ya cancanta a ce ya sami hakan. To daganan ne za a fara jin wasu abubuwa kamar fushi maras dalili, yadda mutum zai ji kowa ba shi haushi yake, ko damuwar da aka gina ta a kan tubalin toka wace mutum ba zai iya yin wani bayani akai ba duk sakamakon kishi ne dake buƙatar magani.

    Da yawa irin wannan matsalar kan kai mutum cikin shakku da abokan zamansa, kullum yana tunanin za su iya yi masa wani abu, ko takalmi ya manta da shi a wani wuri zai fara tunanin daukewa aka yi don a yi masa sihiri. Bare mace rigar nononta ta fada wani wuri ba ta gani ba sai daga baya, cewa za ta yi an dauke ne aka yi abin da za a yi aka dawo mata da shi, to da yake yana faruwa in ta gina shi a kan haka an gama. Mace kullum cikin tsarguwa take in ta dora wa kanta masifaffen kishi, ba za ta iya yarda da kanta ba ma bare wani, sakamakon hakan za ta fara ma'amalla da abokiyar zamanta kamar abokiyar gabar da ba kamarta a duniya.

    Wannan zai sa ta ja layi a tsakaninsu, sai ta fara gulmace-gulmace, da yada ƙarairayi, wani sa'in ƙwaƙwalwarta na ba ta wani abu za ta yada ta ce tabbas ya faru ta hada rigima a cikin gida. In wannan ya faru maigida kan kai ƙarar mace ne wurin wani malami wanda zai nemi yi mata awa'azi, ko maigidanta ya hada ta da uwayenta su yi mata fada, a zahiri wadannan ba abin da suka karanta ba kenan, da yake ya shafi ƙwaƙwalwa sau tari za ka taras matar izgili take wa malamin, ta wurin koyo muryarsa ko sifanta halittarsa kamar yadda yake yi da wuya ko geme ko yadda yake ƙifta idanu.

    In kuma wurin uwayenta aka kai ta bai wuce su nakada mata dukar tsiya ba, ko alal-aƙalla su zazzage ta, duka dai an daura alhakin abin ne a wurin wanda ba bangarensa ba ne, kamata ya yi a nemi malaman ƙwaƙwalwa, ba cewa aka yi ta haukace ba, shawarwari za su ba ta in abin bai yi tsanani ba, in kuwa ya wuce yadda ake buƙata har tsare ta za a yi, don ƙwaƙwalwar ta sami matsala. Da yawanmu muna raina kishi koda mummunan ne kuwa bayan mun san ma'auratan da suka kwana da wuƙaƙe a hannu, matar ta ce sai ta kai shi lahira, daren da ba a yi barci ba kenan, gari na wayewa aka rabu. Amma za a iya magance lamarin da zarar an je ga masana.

    Akwai aurarrakin dake baci wadanda da an sami likitoci da wuri da an iya maganin abin, tsakani da Allah wani kishi zai sa mace ta yi tsirara a gaban jama'a, ko ta yi ƙoƙarin kashe maigidan da take farfagandar ƙaunarsa, ko ta watsa wa kishiyarta gubar da ta san hukuncinsa ƙarewa za ta yi a gidan yari, ko ta zuba wa 'ya'yan kishiyarta makamashi ta yi ƙoƙarin kunna wuta, ko ta kashe yaranta gaba daya ta kashe kanta don ta baƙanta wa maigidan sannan a yi tunanin cewa ƙwaƙwalwarta lafiya lau? Kishi in ya yi tsanani a je psychiatric.

    A Nan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.