5) Yana da kyau kuma ga wace take son magance kishi ta yi ƙoƙarin wayar da kanta ta wurin bibiyar wasu abubuwa da suka ta'allaƙa da rayuwa: Na farko dai kar ta ba wa kanta damar da za ta zauna haka kawai ba wani abin yi komai sai dai ta bida a wurin maigida, idan hanyar samunta kenan shi, wata ma ta zo dole ta damu tunda komai za a raba biyu ne, wani sa'in ma a ce babu, amma idan tana da abin da ta dogara da shi ko mata nawa zai kawo cinsu da shansu ba sa wuyanta zuwansu ba zai rage ta da komai ba, ,ƙila sai dai ƙara customers, kishin zai zo mata da sauƙi, ba kamar wace za ta jira sai dai a ba ta ba.
Na biyu hankalinta ya koma wurin sana'arta, koda
yake maza da yawa ba sa son haka amma yakan rage mummunan kishin da ake fama da
shi a cikin gida, in ya zama mace ba ta zauna wuri guda ba bare shedan ya sami
damar kintsa mata abin da zai kawo tashin hankali tsakaninta da kishiyarta ko
kai da kake ƙoƙarin kawo mata wata. Manufa a maimakon ta tsaya ƙirga
minti nawa ka yi kana magana da kishiyarta, ko ta matso don sauraren me kuke
cewa? Me kuke yi da ta ji shuru ba ta jin muryarku? Ya aka yi ka san ƙannin
wance duka ni ba ka ma san hudu cikin 'yan uwana ba?
Yanzu koyaushe tunaninta wurin aikinta, ko sana'ar
dake gabanta, ya za ta ƙara jari, ko yaushe za ta ƙaro kaya. Ka lura maras
aikin yi ita ke kallon abin da kishiyarta ke sayarwa don ta fara kawowa ita ma,
ba ta da buƙatar kawo nata don magana take nema. Shagaltar da
kanki da wani aiki ko wata sana'a da za ta hana ki kallon wata bare ki sami
lokacinta. Daganan sai ki yi ƙoƙari ki sami wata makarantar islamiyya inda ake
gaya wa mutum Allah.
Amfanin wadannan makarantun mace za ta ji wasu
abubuwan da suka dace da rayuwarta a gidan miji, za a gaya mata lahira da
hisabi, yadda ko ta so yin wasu abubuwan in ta tuno uƙubar Allah sai ta yi
la'asar. Sai ta yi ƙoƙari ta sami littafai wadanda aka rubuta a kan
kishi. Akwai wasu shirye-shiryen mata da suke magana kan batutuwan da suka
shafi aure da kishi, akwai fima-fimai, akwai kotuna a kan talabijin da aka
tanade su don kishi, ina ganin in mace ta same su ta gama.
6) Sai kuma mace na buƙatar ta kula da kanta
sosai, ta riƙi wadannan abubuwan na gyaran jiki da ake cewa, na
ciki da waje, ba abu ne da za ta yi wasa da su ba, in dai ta riƙe su
ba ta da buƙatar sai ta yi fada da wata kafin ta jawo hankalin
maigida, na taba samun hirar wasu mata a social media lokacin da ake wa wata
jajen cewa maigida zai ƙara aure, cewa ta yi "Banda buƙatar
fada da wata mace a rayuwata ba ita ta kawo ni ba, miji ne dai ko? Bismilla, ni
na san yadda nake lallaba gidana, amma ta gwada kishi a wannan gidan ba da
hayaniya za a yi ba, ƙarfi da ƙarfe ne".
To dama aikin dan jarida shi ne bincike da ƙwaƙule
gaskiyar abin da zai amfani jama'a, da kuma baza shi don daukakarsu ko kare su
daga wani abubuwan da za su cutar da su, a ƙarshe dai an gano cewa
ita ke daukar nauyin gidan tare da kasancewar yana da sana'arsa mai kawo masa
kudi, ita ke yi masa dinki, ta sayo masa
kayan sakawa. Wankin kayansa kuwa ba abin da ya sani a ciki bare guga. Ga matar
gwana ce wurin dafe-dafen zamani da na dauri, kuma ba kasafai take neman ya ba
ta wani abu ba.
To sai dai wani hanzari ba gudu ba, lokacin da
amaryar ta shigo maigidan ya nemi hana uwargidar sana'ar da take daga kai da
ita sai zaman ya nemi ya gagara, shin amaryar ce saboda kishi ta nemi a hana
uwargidan yin sana'arta ko shi ne saboda shagalar da ta yi da kasuwanci ya yo
aure ita ma ta biyun ta kalli ta farkon ta ga tana son ta sami abin yi hakan ta
sa ya nemi hana su gaba daya oho, auren na farkon ya lalace yanzu haka, don
kowa ya ƙi ja da baya kan ƙudurinsa, shin akwai tasirin kishi a wannan?
Ƙila kowa ya ce babu,
amma ita tun farkon aurensa ta fada cewa amaryar ba za ta iya ja da ita ba,
tana ƙawata kanta a gaban maigidan wanka na ƙarshe kuma da kudinta
take yi, irin su gashi da matsi da tsumburkan Barebari ba wanda ba ta yi, 'yan
uwansa duk ta kama su a hannu bare mahaifiyarsa da ita take mata komai da kanta,
tabbas ba a ji hayaniyarta lokacin da ya ce zai ƙara aure ba sai lokacin
da ya nemi hana ta sana'a. Kenan ya yi ƙoƙarin dawo da ita matakin amaryar ne abin
ya gagara. Mata ku nemi sana'a.
A Nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.