4) Mace ta yi ƙoƙarin ganin ta jawo kishiyarta kusa, alal aƙalla ta rage matsalolin da za su dame ta na ƙalubalen rayuwa a gidan miji. Maigidan na buƙatar abubuwa da dama, ga yaransa in dai ba mahaifiyarsu ce ta yi musu abu ba gani za su yi kamar tana cutar da su ne don ba ita ce ta haife su ba. Tabbas akwai wahala kowa ya sani, amma ba abin da zai taimake ta sama da yin haƙuri.
Na taso na ga uwayenmu kan buga mana misali da
rijiyoyin kwakware, yadda ake haƙa su a sanya musu wani kwabren ita ce ana jawo
igiyar guga ta kansa yana jujjuyawa, sannu a hankali igiyannan za ta yi ta cin
kwabren har ta yanke shi ta ci koma kan ƙarfen shi ma din yau da kullum in dai ana
jan igiyar a kansa haka za ta raba shi biyu. Ma'anar wannan in dai igiya za ta
yanke katako ta yanke ƙarfe saboda yau da gobe ba abin da in aka yi haƙuri ba
za a ga bayansa ba.
Duk macen da ta saba zama ita kadai daga baya aka
yi mata kishiya ba yaƙi da kishiyar ko wanda ya kawo ta shi ne mafita
ba, ta tsaya ta yi karatu cikin natsuwa, ta san cewa yanzu fa su biyu ne a
wurin maigidansu, kuma ba ƙara masa abin da yake kawowa za a yi don ya ƙara
aure ba, dole dai abin da yake samunnan ne za a raba biyu. Kenan mace ta san
cewa abubuwa za su ragu, daga kudin da yake ba ta zuwa lokacin da ya saba zama
da ita su tattauna matsalolin gida, hatta shawarwarin da yake nema a wurinta
sai in ta fi nuna masa tausayi da sanin yakamata kafin ta iya riƙe shi.
Kenan nuna adawa da yin fito na fito da auren da
maigidanki zai yi ba shi ne mafita ba matuƙar ba za ki iya hana shi
abin da ya yi niyya ba, idan ma kin yi din mutane za su fassara shi da cewa
amaryar ce ba ki son ta shigo, don haka za a kwashe duk abin da ya wakana
tsakaninki da maigidan ƙarya da gaskiya a je a gaya mata, abin takaicin
wani sa'in ma maigidan naki ne zai gaya mata abubuwan da kuka yi, ya ce ba ki ƙaunarta
ko kadan don haka ki san yadda za ki fito mata.
Kin ga an riga an hada ku fada, tun ma kafin a
kawo ta gidan, domin za ta shigo ne da masaniyar cewa baki son ta, kuma ta ji
ne a bakin da ba zaibyi mata ƙarya ba, ita ma za ta gaya wa uwayenta wadanda za
su kintsa mata yadda za ta yi rayuwa dake. Yanzu dai sai haƙuri,
don kuwa an riga an hure mata kunne da cewa kar ta bari ki maida ita jaka ko ta
riƙa kallonki a matsayin wata babba.
Za a ce mata dake da ita duk mata ne a wurin
maigidanku don haka kar ta daga miki ƙafa a komai, kin ga anan in ba haƙuri ba
ba yadda za a yi zamanku ya yi kyau. Dole za ki kau da kai na tsawon lokacin da
za ta gano cewa duk abubuwan da aka fada dinnan a kanki ba gaskiya ba ne, hakan
zai tabbata ne kuwa da zaman da kuka yi tare na tsawon lokaci wanda sam ba ta
taba ganin komai na allawadai ba.
To kin ga duk tsawon wannan lokacin tana tafiya ne
kan abin da aka gaya mata kafin aure. In kika jure munanan abubuwan da take
miki sakamakon abin da aka gaya mata, kika kau da kai daga duk abubuwan da 'yan
waje ke cewa kika ci gaba da kyautata mata don gyarar gaba, wata rana da kanta
za ta gaya miki duk abubuwan da aka fadi a kanki, da ma wadanda suka fadi din,
in kuwa kika gaza kika fara nuna mata cewa ke ma fa ba kanwar lasa ba ce, za ta
ce lallai abin da ake fadi a kanki gaskiya ne gashinan ta gani.
Abin akwai wahala amma ana iya maganinsa don an yi
ma ba daya ba ba biyu ba, kishi tabbas cuta ne wanda yake da magani, matsalarsa
kawai mai cutar ko ta tabbatar da cewa tana da azababben kishi ba za ta yarda
cewa cuta ne ba bare ta yi tunanin ana magance shi ta je inda za ta a yi, sai
dai ta yi ta abinta ita kadai har sai ta debo abin da zai dame ta sannan ta
fara neman mafita, wanda galibi a irin hakan ba wata mafita kuma sai dai a
kiyayi gaba
A Nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.