Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsalar Istimna'i Da Illolinsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Inada tambaya Wato malan akwai wani bawan Allah dayaxo yasameni da wata babbar matsala Wai akwai wata dabi'a dayake yi wato yana masturbating, Shi ne yazo yasameni nikuma gaskiya banwaye da abun sosai bah seda nai browsing, Shi ne nakeso musani illar abun kuma yadda zaiyi yadena, Dan yace min abun nadamunsa kuma na tambayi wani malami yace gaskiya bazai iya fadamun ba sedai yaturan amsar ta Whatsapp kuma haryanxu bai bani amsar ba.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To ďan uwa ina rokon Allah ya rabashi da wannan ďabi'ar Sannan kuma tunatarwar da zanyi masa shi ne Idan har yana da halin yin aure to yaje ya yi aure, idan bashi da halin auren budurwa koda bazawara irin sakin wawannan ce yaje ya aura ba lallai dole sai ya samu budurwa ba musamman idan bashi da halin auren budurwar kaga auren bazawara be kai na budurwa tsada ba, idan kuma bashi da ikon auren gabaki ďaya to sai ya yi ri'ko da wasiyyar manzon Allah wato ya dinga azumin nafila zai samu sauki in Shã Allahu.

Sannan ya nisanci kallon haram da karanta haram da zantukan haram. ya lazimci Karatun Al'kurani dasauran azkar na yau da kullum wadanda manzon Allah ya koyar musamman na safiya da yamma sannan ya lazimci azkar na saukakuwar al'amura dasauransu in Shã Allahu, Allah zai kawo masa mafita, Amma dai lallai ya sani masturbation ɗin da yake yi ko ince biyawa kansa bukata shi kaďai da yake yi haramunne sannan baya ga haramcin yin masturbation ɗin Kamar yadda manazarta suka ce biyawa kai bukatar yana haifar da illoli da suka shafi lafiya ga wasu daga cikinsu kamar haka:

1. Yana iya sa wa idan mutum ya girma ya kasa rike fitsari.

2. Yana kashe sha'awar mace ko namiji ta yadda ko sunyi aure ba za su samu wadatacciyar sha'awar gamsar da aboka nan zamansu ba.

3. Kankancewar Azzakari ko Sassabewar kan Azzakari. Idan Mace ce kuma, Gabanta zai Bude (Disvarg).

4. Tsargiya, fitsarin jini. Yin Istimna'i ( masturbation) kan sa mutum ya ga yana fitsarin jini, ko in ya yi Istimna'i  (masturbation) ɗin ya ga ya taho har da jini.

5. Raunin jiki, duk mai yin istimna'i  (masturbation); yana yiwa jikinsa asarar wasu sinadarai masu kara kuzari. Don haka zai zama mai raunin jiki.

6. Ramewa. Mutum zai ta ramewa, komai cin abincinsa da shan magunguna kara kiba.

7. Karancin maniyy. Wanda hakan yake da illoli da yawa, kamar haifar da rashin gamsar da iyali, rashin iya haihuwa da dai sauransu.

8. Cutar ma kanta.

9. Duk mai wannan aiki zai gamu da yawan mantuwa da shiririta hakanan Yana rage hazaƙar kwalwa. Duk karatun da mutum yake ganewa zai dawo ya dena fahimta.

10. Fitowar Tsutsotsi daga gaban Namiji Ko mace.

11. Ciwon mara ga namiji ko mace.

 12 Mace mai yin istimna'i  (masturbation) yana jawo mata Kaikayi da kurajen gaba, doyin al'aura ma'ana: jin wari yana fitowa ta gabanta, Ko Ganin wani farin ruwa yana fitowa, ma'ana: ciwon sanyi infection.

13. Watery sperm. Yana sa maniyyin mutum ya tsinke ya zama kamar ruwa kuma mara kauri, wanda hakan ke nuna dakyar in mutum zai iya haihuwa.

14. Yana sa mutum haka kawai ya ji yauƙi yana fito masa koda bai yi masturbation ɗin ba.

15. In ya sarƙi mutum to in ya kwana biyu bai yi ba sai ya yi ciwon ciki kamar zai mutu.

16. Yana kawarwa da mace budurcinta.

17. Yana kawo zubewar nono ga mace.

18. Yana sa mace ta dena sha'awar namiji samsam, wato taji bata sha'awar namiji wanda hakan zai iya kaita ta dinga niman ýan uwanta mata Hakanan shima namiji zai dena sha'awar mace sai dai maza ýan uwansa.

Allah shi ne mafi sani.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments