Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
Kallo Na Ido
Bayarwa: Kallo na ido,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Mata ga garin magani,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Mata ku fito ga magani,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Duk ku fito ga magani,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: A yau ni zan ba ku shi,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: In har ba ku san ni ba,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Ni ce mai magani,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: A nan kin ga na kishiya,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Idan kika karɓi na kishiya,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Baɗi ya war haka,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Kin kore kishiyoyi ɗari,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Nan kin ga na mai gida,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Idan na ba ki na mai gida,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Kullum ba ya ƙi ta taki ba,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Nan kin ga na arziki,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Domin ki kore tsiya.
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: A nan kin ga na haihuwa,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Idan kin karɓi na haihuwa,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Ya war haka in mun je baɗi,
Amshi: Ɗan gajere.
Bayarwa: Kin haife ‘ya’ya ɗari.
Amshi: Ɗan gajere.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.