Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka Yi Rawa - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

Ka Yi Rawa

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ban yi ba.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da gemuna?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da carbi na?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da rawanina?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da allona?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: A ina wai?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ƙarya ne.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ban yi ba.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ku ji sharri.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: To bari in taɓa

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments