Ticker

6/recent/ticker-posts

Kuɗin Toshinki na Bara - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

Kuɗin Toshinki na Bara

Bayarwa: Malama ga kuɗin toshinki,

Malama: Bankaɗa lefena ku zuba mini,

 Ba na barin salla ta wuce ni.

 

Bayarwa: Malama me kike ta faɗi ne?

Malama: So nake na yi tarin salla,

 Don bana kun ga ko ba a wuce ni.

 

Bayarwa: Malama ya batun tashen ne?

Malama: Tashen bana ya fi na bara samu,

 Dole ne yanzu nai farawa.

 

Bayarwa: Malama me kike ta faɗi ne?

Malama: Ca nake ku taho mu yi taku,

 Mui haka mui haka mui juyawa.

 

Bayarwa: Malama kin yi sallar safe?

Malama: Ban yi ba in kun yo taku,

 Anjima ni zan yo tawa.

 

Bayarwa: Malama ashe halinki yana nan?

Malama: Kai ku ƙyale ni tashen za a yi,

 Koko tambaya kuke so kui min?

 

Bayarwa: Malama ai dukka muna so,

Malama: To ku bari sai gari ya waye,

  Tambayarku dole in amsawa …

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments