𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Allah ya ƙara ilimi, ya bada ladan
fatawa. Malam don Allah, taron addu’a da sadakan uku da akeyi bayan zaman
makoki na kwana uku yana da hurumi a musulunci? Shin akwai wani amfani da
wannan adduar take da shi ga mamaci? Har
akanyi abinci, kamar waina, a dinga rabawa ga duk wanda yazo wurin zaman
makokin a ranar, da sunan sadaƙa. Shin Abincin da ake rabawa yan zaman makoki, ya
halatta aci ? Don Allah Malam ayi min bayanin matsayar musulunci a kan wannan
al’amarin. Na gode kwarai, Allah ya saka ma Malam da alkhairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaykumussalam. Sadakar uku ba karantarwar
manzon Allah ﷺ ba ne,
hakanan ba aikin sahabbai da tabi’ai ba ne, shari’a bata iyakance lokuttan da
ake yiwa mamaci addu’a ba, dazarar mutum ya rasu yana bukatar addu’a har iya
rayuwar shi mai Addu’ar.
Tara mutane bayan kwana uku, ko bakwai ko arba'in
da dafa abinci da raba waina duk waɗannan bidi’o’ine da aka kirkiro daga baya, Babu
wani dalili na shari’a a kan haka.
Manzon Allah ﷺ ya fada cewa: …. “duk wanda ya kirkiro a
cikin al’amarin mu (Addini/shari’a) abin da baya cikin
addinin/shari’a toh an mayar masa”…. Don haka nisantar aikata haka shi ne dai
dai.
Abin da sunnah ta tabbatar shi ne makwafta su dafa
abinci su kai gidan da akayi rasuwa kamar yadda Hadisi ya zo cikin sunan
“Attirmizy 998 da sunan abu dauda 3132” hadisin Ja’afar ibn Abi
dhalib, hakanan imam Shafi’i a cikin littafin sa” Al’ummi 1/317” shima ya
tabbatar da haka.
Jamhurun malamai sunce makaruhi (Abin kyama/ki)
raba abinci ga wadanda sukazo ta’aziyya wasu ma sunce bidi’a ne yin hakan kamar
yadda ya zo cikin “Fathul ƙadeer 2/142”
Babban malamin a mazhabar Malikiyya imam Alhaddabi
Almaliki yace cikin sharhin muktasar kaleel wato mawahibul jaleel 2/228
makaruhi ne rabawa masu ta’aziyya abinci don ana kirga hakan cikin bidi’a.
Hakanan Sheikhul Islam ibn taymiyya a cikin fatawar sa 24/316 yace taron mutane
a gidan mamaci da raba abinci a ci wannan bidi’a ne ya kawo maganar jareer ibn
Abdullahi cewa mukan dauki taron jama’a da raba abinci a gidan mamaci a zamanin
mazon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) a matsayin `Niyaha’ wato shelar mutuwa
irin wanda shari’a ta haramta.
WALLAHU A’ALAM
Malam Nuruddeen Muhammad Mujahid
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.