Wai daga kanmu aka daina ne ko me ya faru matasa suka daina kafewa, gwagwarmaya da yaƙi akan so da ƙaunar juna wajen yin aure ?
Don na daƙe ban ji ana kai ruwa rana ba akan wani
saurayi da budurwa a farfajiyar so da ƙauna har ka ji duk unguwa ko gari ya
dauka.
Ka ji ko'ina ana labari soyayyarsu ya yi shura yaro na so
yarinya na so iyaye sun ce alanfur ba su san zancen ba, a hana su auren juna.
A da ba fa da daƙewa ba 1990 abinda ya yi baya an samu
ire-iren waƙannan
tata6urzar tsakanin iyaye da y'ay'ansu wajen fidda miji.
Inda za ka ga uwa ko uba ko danginsu sun tsaya tsayin daka
wajen hana yarinya masoyi ko yaro budurwa su ce sam ba su isa ba!
Haka za a buga a tashi hankalin juna wasu har ta kai ga
samun matsalolin rashin lafiya irinsu hauhawan jini bugawar zuciya ko ma mutuwa
ga su manyan saboda wasu dalilai na ƙin abin.
Su kuma saurayin da budurwar ƙarfi da yaji su zama wasu salumburiti a
unguwa duk inda suka wuce ka ga ana nuna su da ido ana bawa waƙanda
basu sani ba labarin soyayyarsu.
Daga ƙarshe ko su ci nasara su auri juna ko a ci galaba akan su a
hana su aure kowa ya ƙare da auren wasu daban cikin ƙunci da zulumi su zama wasu abin tausayi
abin Allaah Sarki.
2000 abin da ya yo sama kawo yanzu aure sake salo ya yi ya
sake suna inda aka kama kiransa Auren Zamani. So da ƙauna suka koma baya aka
kama auren je ka na yi ka. Yau ga shi.
Kusan gaba ƙaya samarin da y'ammatan ba za ka ji ana
labarin soyayyarsu ba balle ka ga ƙauna na safa da marwa tsakaninsu a'a. Sai
dai ka ji ana zanjen a soke lefe da kayan ƙaki.
Idan kuma ba ka ji hakan ba to lura da kyau ba ta so da ƙauna
ake yi ba a'a ta irin shagali da sharholiyar auren ake yi. Wane mawaki ne ya yi
wasa a wajen bikin shi ne abin dubawa.
Yanzu fa an daina damuwa da lobayya ko ƙauna
tsakanin angon da amaryar a'a wa da waye suka zo daurin auren, da me da me aka
yi a wajen bikin, a ina aka yi risafshan ƙin shi ne.
Sai dai in za mu yiwa al'amarin adalci ba a taru an zama ƙaya ba
don ko kwanan nan na ga kwatankwacin irin auren nan na da inda angon ya tsaya
kai da fata ya auri wacca yake so.
Na kuma ga budurwar da ta yayewa saurayinta kuma yanzu
mijinta dukkan wani tashin hankali game aurensu har ta kai ga cewa kusan auren
sahabbai suka yi asirinsu a rufe.
Sai dai a gaskiya irin wannan auren na so da ƙauna
tsakanin ma'aurata kullum daƙa ƙaranci daƙa janyewa daƙa gushewa yake yi. Allaah
dai Ya sa mu dace amin.
©2023 Tijjani M. M.
Daga Taskar
Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960
A Kiyayi Haƙƙin Mallaka
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.