𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam shin ya halatta ayi gini a
kan tsohon ƙabari? Shin ya halatta ayi sallah a Masallacin da
aka gina shi a kan ƙabari?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wajibine Ga Musulmi ya Mutunta Ƙabur-buran
Matattu, Bai halatta shafe Ƙabari ayi filet da shi ya Zama fili dan Amfani ba,
sai inda lalura, idan akwai lalura, to idan aka tone kowacce Gawa Aƙabarinta,
Wajibine aje abinneta A wani Sabon Ƙabarin.
Shaik Usaimeen Ya ce: Bai halatta tone ƙabari
ko yin Gini a wajanba, Matuƙar Guri yana Amsa Sunan Maƙabarta, kada atone Ƙabur-buran
dake Ƙasar, koda Guri ba Maƙabarta ba ne, Sai aka Haƙa a kaga Ƙasusuwan
Matattu dolene a haƙura da gini awannan wajan, abinne Ƙabur-buran
a ciki, Bai halatta mutane su tone ƙabari su gina gidajensu ko Makarantunsu ko
Kasuwarsu ko Asibitinsu ko Masallacinsu a inda Ƙabari yake ba, Wannan
ta'addancine ga Matattu da Zaluntar Matattu, Bai halatta ba.
Akwai Abubuwan da suke halatta idan lalura tasa
dole ayisu, kamar buƙata ta kama za'ayiwa Musulmai titi, sai titin ya
biyo ta Wani bangare na Maƙabarta, kuma Babu wata dabara da za'ayi a kauce
masa, ko kawar da titin daka Maƙabartar, anan ya halatta atone Wani bangare na Maƙabarta,
Ƙasu-suwan da sauran Sassan mutum a daukesu akaisu wani wajan daban Abinne,
idan Lalura tasa dole sai an fadada ko sai an yi hanyar ko titin, kuma babu
wata dabara ta kaucewa ƙabarin, Amma haka Kawai mutum ya share Maƙabarta
don yin gida ko wata buƙata wannan bai halatta ba.
Fatawa Nurun Alar darbi tambaya ta (110).
Idan Aka tone maƙabartar Kafirai, ko
akaiwa maƙabartar Musulmi ta'addanci aka tone ta, ya halatta gina masallaci a wajan
da aka tone Ƙabur-buran, idan akwai Abun da yai Saura na Ƙabur-bura
bai halatta gina Masallaci ko wani gini akansu ba, Hadisai Ingantattu a cikin
Bukhari da muslim sun Tabbatar da haramcin gina Masallaci a kan Maƙabarta
ko Ƙabari, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya gina Masallacinsa A madina
bayan an tone Maƙabartar Kafirai.
Idan Aka gina Masallaci a maƙabartar Musulmi bai
halatta ayi Sallah a cikinsa ba, wajibine a rushe shi, a gina bango dazai rabe
masallaci da Maƙabartar, idan akai haka ya halatta ayi sallah a
Masallacin kuma ta halatta, Ga fatawowin Malamai a kan Wannan mas'alar.
Fatawa Lajnatul da'imah Ta ce: Ƙasar
da Aka gina masallaci a kanta idan ta kubuta daka maƙabarta ya halatta Sallah
a cikin masallacin, idan kuma bata kubuta daka Maƙabarta ko Ƙabari
ba, dolene arushe masallacin da'aka gina a kanta.
Fatawa lajnah (1/418).
Suka Sake cewa: idan Masallaci ya kasance aƙasar
da babu ƙabur-bura a cikinta, abun da yake Wajibi, shi ne tone Ƙabur-buran da Suke gefen Masallacin a binne su wani wajan
daban, idan Na Musulamine akaisu maƙabartar Musulmi, idan na kafiraine akaisu
Maƙabartar Kafirai, a sanya ƙasu suwan Ƙabari ai masa ƙabari nasa guda daya, a
dai-daita saman ƙabari kamar Sauran ƙabur-bura, idan ba zai
iyu a tone ƙasusuwan daka gefen masallaci akaisu Wani wajan
ba, Babu laifi arabe tsakanin Maƙabartar da Masallaci ta hanyar yin Katanga don
rabeta da Masallaci.
Amma Idan Asalin ƙasa maƙabarta
ce, Abun da yake Wajibi shi ne anemi wata ƙasar wacce take
kubutatta ayi masallaci ko duk wani gini a kanta.
Fatawa lajnah (1/419).
Kamar yanda Shaeik Bin baaz ya bayyana, Malamai Suka
ce: idan aka Sanya Ƙabari a cikin Masallaci, wajibine a toneshi a
nisantar da shi da Masallaci, idan kuma Masallacin ko ginin daka baya aka
yishi, Ƙabarin aka Samu awajan, wajibine arushe masallacin ko ginin da kawar dashi,
domin shi ne ginashi zai farar da Abun da aka haramta, Domin Annabi Sallallahu
Alaihi wasallam ya tsoratar da gina Masallaci a maƙabarta, ya tsinewa
yahudawa da Kiristoci a kan haka, ya kuma hani Al'ummarsa da yin kaman-ceceniya
dasu, yacewa: Aliyu Allah yaƙara yarda da shi ( kada kabar duk Wani hoto face
Saika shareshi ka gogeshi, ko ƙabari da aka daukaka shi face saika Sassabe
gininsa da tudunsa ka dai-daita shi.).
Maj-mu'u fatawa bin Baaz (6/337-338).
Saboda haka Duk Wani gini ko Masallaci idan aka
duba aka ga, gurinda aka ginashi, Ƙar-ƙashin Ƙasar akwai ƙabur-bura, bai halatta
ayi Sallah a cikinsa ba, idan Ƙasansa babu Ƙabur-bura ya halatta ayi Sallah a cikinsa.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.