Cite this article as: Bashir, A. & Sabitu Sani, S. (2023). Nazari A Kan Hausar ‘Yan Lakum A Garin Gusau Na Jihar Zamfara. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 124-133. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.014.
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunana Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
mabunza@yahoo.com
Tsakure
Tunanin wannan bincike shi ne, fayyace
yadda sunan hannu ya yi naso da malkashi cikin tunanin Bahaushe da ke bayyana
cikin adabinsa, da al’adunsa, da harshensa. Binciken da aka yi na take da
kirarin da Bahaushe ke yi wa hannu, na cewa ba ya da tsoro. An yi amfani da
kayayyakin adabi da al’ada da harshe domin tabbatar da dugadugan bincike.
Karance-karancen ayyukan magabata kawai ba zai warkar ba, dole sai an haɗa da yawon rangadi da tattauna na rukunin mutane daban-daban.
Da aka fahinci babu wani aiki bugagge ko wani ba shi ba da aka yi a kan
Bahaushen tunani kan hannu sai aka kwakkwahe takardun rubutu. An ɗora wannan ‘yar takarda bisa fasula (13) haɗe da gabatarwa da naɗewa.
Takarda ta yi wa hannu karatun ƙwaƙƙwafi bayan fayyace suna (2) na hannaye,
ta sake ƙwalailaice
abubuwa (15) da ke liƙe ga
hannun ɗan Adam da sunayen da Bahaushe ya laƙaba musu. A jimlace an leƙo amfanonin hannu (23) tare da fayyace
nau’o’in rabe-raben hannu (9) a Hausance, An kafa hujja da sassan adabi (23) da
suka ambaci hannu a mahanga mabambanta, tare da amfani da ɗiyan waƙa
(7) na mawaƙan
baka daban-daban domin kwakkwahe bayani. Labaran raha (2) aka yi garkuwa da su
na tabbatar da samuwar shawagin hannu cikin tunanin Bahaushe. A jimlace an
sarrafa haujjoji (81) da suka tabbatar da da’awar wannan bincike. A kan haka,
binciken ya hango sakamako (5) da aka rairaye cewa, babu wata gaɓa daga cikin gaɓɓan ɗan
Adam da ta kai hannu tasiri cikin tunaninsa. Don haka ya zama jagora daga cikin
gaɓɓan ɗan
Adam. Tabbas! Yadda Bahaushe ke kallon bahagon hannu haka nan yake a addinance
da kimiyance. A kan haka ne wannan takarda ke da fahintar ya kyautu a saka
nazarin sassan gaɓoɓin
jikin ɗan Adam cikin manhajar koyarwar
harsunanmu. Akwai buƙatar
mayar da himma ga wannan fanni na nazari.
Fitilun Kalmomi: Hausa, Hausawa, Al’ada, Hannu
Gabatarwa
Tunanin ‘yan Adam a koyaushe ba ya tsallake al’adunsu na
rayuwa. Matsalolin da suka fuskanta da ci gaba da suke samu na hanyoyin warware
matsalolin da samun nasara a kansu; su ne suke adanawa cikin taskar adabinsu. A
cikin adabi da al’ada da harshe; adabi ne rumbu, al’ada ita ce kundi, harshe ne
alƙalami.
Alƙalamin
harshe ne ya rubuce taskokin hikima irin su tatsuniya, karin magana, kirari, waƙa, tarihi da tarihihi aka kai su cikin
rumbun adabi aka adana, bayan an adana aka taskace su cikin taskokin al’ada.
Idan akwai lokacin da ake ganin ɗan Adam ya fara tunanin karin magana,
to, da wuya in ba tun halittarsa ba ne, da ya fara lura da sauye-sauyen da gaɓɓansa ke yi tare da amfanoninsu da yake
morewa. Babu wata gaɓa da ba ta da muhimmanci ga jikin ɗan Adam, amma na zaɓi hannu in ɗora shi ga ma’aunin tunanin Bahaushe.
Warware
Taken Bincike
An ɗora
wannan bincike a kan kirairan da Bahaushe ke yi wa hannu. Matuƙar hannaye na aiki ba za su bari komai
ya samu gangar jiki ba, ko da ya fi ƙarfinsu. Irin yaƙi tuƙuru da hannu ke yi na kare mai shi, shi
ne dalilin yin masa kirari, hannu ba ka da tsoro. Buƙatata binciko amfanonin hannu da
Bahaushe ya taskace cikin adabinsa, da al’adarsa, da harshensa. Da gangan na sa
“masu abu” domin duk wani bunƙasashen
harshe ba ya rasa karuruwan magana da zantukan azanci da za su taɓo sassa na gaɓoɓin ɗan Adam ba. Don haka, wannan bincike da
Hausa zai yi garkuwa. Zai binciko irin matsayin da hannu yake da shi a
tarsashin tunanin Bahaushe. Babu wai, mun san idan aka rasa ƙafafuwa gaba ɗaya hannu na wakiltarsu ya yi aiki irin
nasu. Haka yake idan an rasa hannaye gaba ɗaya ƙafafu na wakiltarsu ga dukkanin
ayyukansu. Hannaye ke sama, ƙafafu
ke ƙasa,
don haka wannan bincike zai fara duba hannu.
Ina
Ne Hannu?
Bincike ba ya rena bayani, don haka
komai ƙarancin
bayani sai bincike ya ƙwaƙwalo shi, ka da a bar shi a baya ya ɓata tsari bayan an kama hanya. A taƙaitaccen bayani hannu shi ne:
i.
Farkon samansa kafaɗa ita ke riƙe da shi
ii.
Ya ɗan yi ƙasa kaɗan aka samu hamuta/hamuce
iii.
Ƙashin farko da ke biye da hamuta shi ne dantse
iv.
Matuƙar
dantse shi ake cewa maƙizumu/guiwan hannu.
v.
Ƙashin da ke riƙe da maƙizumu shi ne hannu.
vi.
Ƙarshen hannu shi ne wuyan hannu wadda ke riƙe da ƙassan yatsu. Idan an cire gaɓar hannu ya koma gundumbuli.
vii.
Ƙassan da ke soke ga gundumbuli su ne yatsu gaba ɗayansa sunansu hannu ɗaiɗaikunsu
ake cewa yatsa kowannensu
biyar/shida da sunansa.
viii.
Ƙashin da aka shimfiɗa su aka daɗɗaure su da jiyoji sunansa tafi/tahi don haka yake karɓa sunan tafin hannu.
ix.
Abin da ke liƙe a ƙarshen kowace yatsa shi ne ƙumba/akaifa.
x.
Ɗan hirkakin fatan da ke ɓantalewa gefen yatsa sunansa ɗan
uba.
xi.
Shimfiɗar gadon bayan tafin hannu shi ake cewa ban hannu.
Idan aka karanci waɗannan abubuwa sosai; za a ga sai an ce
hannu za a tsaya a bi abubuwan da ke tare da shi daki-daki. Ka da a yi mamaki,
waɗannan abubuwa duk ana iya tsintuwarsu
cikin harshe, ko adabi, ko al’ada, a yi amfani da sunansu ko ba a ambaci hannu
ba. Sai dai a kowane lokaci aka ambaci hannu duk sun shige cikin lissafi. A taƙaice, ya kamata a kula da waɗannan abubuwa wajen karatun hannu:
i.
Hannu babu yatsu sunansu dagin
hannu.
ii.
In an cire dagin sunansa gundumbuli.
iii.
In an cire gundumbuli aka bar dantse sunansa ɗan
hannu.
iv.
In an cire ɗan hannu zancen hannu ya ƙare.
Idan aka kula da abubuwan da aka lisafa
waɗanda hannu ya ƙunsa za a ba hannu fassarar cewa:
Hannu
shi ne yanki na jiki dogo mai reto sassan dama da hagu na gangar jiki wuce
kwankwaso daidai tsakiyar ɗuwawu. Yana da manyan gaɓoɓi huɗu daga kafaɗa zuwa turakun yatsu. A al’adance, su ne
makamin mai su ga kowane aiki ya tunkara.
Dabarun
Bincike
Abin da ake son a yi bincike a fili
yake, amma abubuwan da ake son a ƙyallaro
cikinsa sai da dabaru. Na farko, an ratsu ayyukan adabi da al’ada da harshe na
magabata da aka yi tsintuwar wani abu kan hannu a ciki. An tattauna da mutane,
mata da maza, yara da manya, a kan yadda suke ganin hannu da abubuwan da ke liƙe da shi. A yi zuzzurfar binciken adabin
baka na waƙoƙi da karin magana, da zantukan azanci da
suka taɓo hannu gaba ɗayansa ko sassansa. Da yake ba a ci karo
da wani bahaushen aiki ko baturen aiki da aka yi kan hannu a mahangar Bahaushe
ba; don haka ba a samu wani aikin da za a yi bitar sa ba. An yi amfani da
sadarwar zamani ta waya da google da saƙon text domin faranta kayan aiki. A
wajajen shekarar 1989 na ci karo da wani littafin Ingilishi mai suna Left and Right da hoton tafin hannu biyu
na yi cigiyarsa Agusta, 2022 na rasa. Na tuna da UNESCO Courier sun taɓa buga wani bincike mai taken: “the
Hand(s) that speak volumes” na kasa gano ma’ajiyar. Duk da haka na san an yi
ayyuka kan hannu a fannin Tsibbu da tsafe-tsafe wanda wannan gama garin bincike
ne, bai hau doron tunanin wannan bincike da ke son leƙo tunanin Bahaushe a kan hannayensa ba.
Waɗannan karance-karance sun taimaka ga ƙara wa wannan bincike ƙarfin guiwar a matsa gina ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba.
Matsayin
Hannu a Jikin Mai Shi
Wannan fasali wata gaɓa ce, ta tabbatar da dalilin wannan
bincike. Abin da baya da amfani, ba amfanin a yi bincike a kansa. Irin
amfanonin da wannan bincike ya hango ga hannu a rayuwar masu shi, da yadda masu
shi suka sarrafa amfanonin cikin adabinsu da tunaninsu na al’adunsu shi ya ba
da damar a yi wa hannu karatun kansa. Tunanin wannan faslain ya lisafa amfanoni
ko ayyukan hannu ga mutum, kana a dubo yadda ya sarrafa waɗannan ayyuka cikin tunanins.a Kaɗan daga cikin ayyukan hannu ko amfanonin
hannu akwai:
i.
Bayarwa
ii.
Karɓa
iii.
Gaisuwa
iv.
Susa
v.
Riƙo
vi.
Duka
vii.
Rubutu
viii.
Runguma
ix.
Fada dambe/kokuwa
x.
Tsaftace jiki
xi.
Magana
xii.
Kariya
xiii.
Yaƙi
xiv.
Cin abinci
xv.
Sana’a (ɗinki, saƙa, kaɗi, fawa, farauta, gini, noma, ƙira, su, kiɗa, tuƙi, da sauransu).
Idan aka ce, za a ƙididdige abubuwan da hannu ke yi za a ga
kamar in ba hannu mutum zai zama hoto. Kasancewar hannu komai da ruwanka cikin
rayuwar mai shi, shi ya ba shi damar sassaka ayyukansa da amfanoninsa cikin
taskar adabinsa da al’adunsa. Wannan bincike tuni ya kamata a ce, an yi tunanin
yin sa da tuni ya samu gurbi cikin gurabun darusan da ake koyarwa a manyan
makarantu da jami’o’i ba kawai a ji zarmoɗansa
a waƙoƙi ko karuruwan magana ba, a’aha, ya samu
wani bagire cikin gurabun darusan koyarwa.
Hannu
a Gurabun Al’ada
Al’ada ba ƙaramin matsayi ta yi wa hannu ba ga irin
karance-karancen camfe-camfenta da abubuwan da aka saba da su yau da gobe. A ɗan wannan bincike, karon farko al’ada ta
kasa hannu kashi biyu:
i)
Hannun dama
ii)
Hannun hagu.
Ga al’adar ƙirar da Allah Ya yi wa Hausawa masu
amfani da hannun dama cikinsu sun fi yawa. Duk wani aiki nagartacce da hannun
dama ake yi, kamar cin abinci, da gaisawa da juna, da riƙon hannun yaro ko babba. Ashe gaskiyar
Dakarkari da ke yin waƙa
cewa:
Jagora : Hannun dama kamar lauje
:
Da shi muka yanke tuwo ƙauna
:
Surub! Surub! Mu sa baki
Jagora Yara : Lukkutu, lukkutu, a ba Dukku
:
Badukku ba su rainawa.
Babu shakka Bahaushe ma yana yi wa
hannun hagu kirari ko suna da “gatarin tuwo”. Saɓanin hannun dama, Bahaushe duk wani aiki
na share ƙaznta
da hagu yake yi, kamar tsarke da fyace majina, da matsar ƙurji da wankin gyambo da kawar da mushe.
A al’adance waɗannan ayyuka marasa tsafta da ake yi da
hagu shi ya sa al’ada ta zarge ta da dahi mai tsanani. Bugu da ƙari za a ga, ko mutum buwayayye ne ko
buwai shiri sai a ce: “ai wane bahagon mutum ne”. A fagen daga irin su dambe da
kokuwa ana tsoron bahago. Cikin fitattun ‘yan damben duniya Muhammadu Ali na
Amurka, da Shagon Ɗan’anace
da Garba Mai’addar Sababi, da Bahagon Nahantsi da Dogo Baƙo, da duk da hagu suke aiki. Ai saboda ƙarfin ta ne a Turai sitarin motocinsu
hagu yake, ko a Nijeirya da shi aka fara da baya aka koma dama har Shata ya yi
waƙar, “kiliya
ta koma dama”. Bahago in ya bugo ba ya kuren mabuga, in harbi ya yi da wuya ya
yi kuren “bara” da kibiya ko bindiga. Dalilin haka shi ne, zuciyar ɗan Adam a hagu yake, don haka duk
tunaninsa a hagu yake hannun da ke hagu tare da zuciya suke aiki, in zuciyarsu
ta yi ƙuduri
sai hannun ya yi abin da ta buƙata.
Wannan ba al’mara ba ne domin a Musulunce komai da dama ake yin sa in ba tsaki
ba, amma a ɗawafin ɗakin Allah aka sunnanta a sa kafaɗar hagu ta kusanci ɗakin Allah domin nan ne zuciyar ɗan Adam take.
Hannun ɗan Adam ya yi tasiri sosai ga karatun
sassan jikinsa. A al’adance abubuwan da ke gefen hannu da sunan hannun ake
kiran su. Dubi wannan ɗan misali ka gani:
a.
Hannn dama
b.
Kafaɗar dama
c.
Dantsen dama
d.
Yatsun dama/hannun dama
e.
Haƙarƙarin dama
f.
Kuiɓa dama
g.
Ƙafar dama
h.
Idon dama
i.
Kunnen dama
j.
Haɓar dama
k.
Cinyar dama
l.
Hannun hagu
m.
Kafaɗar hagu
n.
Dantsen hagu
o.
Yatsun hagu
p.
Haƙarƙarin hagu
q.
Kuiɓin hagu
r.
Ƙafar hagu
s.
Idon hagu
t.
Kunnen hagu
u.
Haɓar hagu
v.
Cinyar hagu
Abin lura a nan shi ne, da an ce “dama”
hannu ake nufi, haka da an ce “hagu” hannu ake nufi. In an ce “gehen dama” abin
nufi gehen hannun dama; haka idan aka ce, gehen hagu, ana nuni ga gehen hannun
hagu. Ita dai hagu muguwa ce tun ma ba a yi zancen dambe ba kamar yadda Ɗan’anace ke ce wa Shago:
Jagora: Ka
iske Ɗandunawa,
: Ka rimbiɗe shi da hauni
: Tun da ba ubanku
guda ba.
(Bakandamiya).
A rawar da ‘yan dambe ke yi, gabanin a
fara dambe cewa suke yi:
Jagora:
hauni ba garaje
:
mai sa ido hawaye
Jimillar
Sunayen Hannu a Al’adance
Sunan dama da hagu gama gari ne kowa haka
yake kiran su da shi ake rarrabe su. A al’adance, Hausawa na yi wa hannu sunaye
bakwai gwargwadon halin da mai su yake ciki da irin tasirin su gare shi:
i)
Dogon hannu
ii)
Kararren hannu
iii)
Rariyar hannu
iv)
Saurin hannu
v)
Hannun ƙwarai
vi)
Mugun hannu
vii)
Dahin hannu
viii)
Daɗin hannu
ix)
Albarkar hannu
Ga al’ada da an ce: dogon hannu, ba
tsawon ake nufi na ainihi ba, sata ake nufi. Ke nan kowane ɓarawo mai dogon hannu ne. Kararren hannu
a waje mata ita ce macce ragguwa wadda ba ta iya daka wa mijinta abin da zai
ci. Wannan ragganci shi ya sa suke ƙaddara hannun kararre ne a waƙarsu da suke:
Jagora: Tashi
mai kararren hannu
: Hannu da ba ta shi
tashi ga daka,
:
Ga cin tuwo shi ka tashi.
A tunanin Bahaushe duk mutumin da arziki
bai karɓa ba komai aka ba shi na tanadin sana’a
sai ya tarare ya nakkashe, za a ce: “wannan mutum rariyar hannu gare shi”.
Yadda rariya ba ta riƙon
ruwa, haka hannunsa ba ya riƙon
arziki. Abin mamaki akwai mai saurin hannu amma babu mai nawan hannu. Mai
saurin hannu shi ne, wanda ba ya jinkirtawa wajen kai duka da hannu ko sanda ko
wani abin bugu in an husata shi. Hannun husata ƙwarai shi ne, wanda idan ya ajiye abinci
kamar wake har ya shekara ba ya tsutsotsi. Idan za a ajiye wani abu shi ake ba
domin babu wani da za ya lalata su. Mugun hannu shi ne hannun da duk aka sa ga
wani abu sai ya lalace. In ya ajiye wake ya yi ƙwari, in igiya ya ajiye ta yi gara, in
taɓo wata haja ta sayarwa masu cinike sun ɗauke ƙafa. A tunanin Bahaushe hannu dafi ne,
ai shi ya sa, da an sa wa miya hannu kamin safe ta lalace. Idan mai ciwon ido
ya murzar idanunsa da yatsunsa sai ƙara ja suke ba zance warkewa ba. A fagen
magani Hausawa cewa suka yi, ba a wanke gyambo ko wani tsohon mike da hnnu tsirara
domin hannu dahi ne, da wuya a ci nasarar warkewarsa. Tsoron dahin hannu ya sa
ko dukar dabba aka yi da hannu ko aka sa wani makami aka doke shi ya faɗa ƙasa, take za a “hura hannu biyu”, wato
rage kaifin dahin hannu. Idan ba a yi haka ba, to, abi nan ko ba ya tashi,
harshe ya mutu.
Daɗin
hannun yana da alaƙa da
haguntaka. A kan hannu hagu mun ambaci gehen da take da kusantaka da zuciyar ɗan Adam. To, mai daɗin hannu shi ne, wanda in maharbi ne ko
na baka ko bindiga kai ko da dutse ya jefi wani abu yana samunsa wurin da yake
son ya same ta. Ire-iren waɗannan ake ce wa masu daɗin hannu. A ko’ina mai daɗin hannu abin so ne, kuma abin nema ne
ga mazaje. Ga al’ada mafi yawan masu daɗin
hannu za a taras da hagu suke aiki. A zamanin Jahiliyya akwai Warsh wanda ya
soke Sayyidina Hamza da mashi a ƙirji.
An ce William Sirry wanda Ya harbe Janar Murtala Ramat Muhammed (1976) bahago
ne daɗin hannu gare shi. An tabbatar da cewa Nabame
kakan Kabawa daɗin hannu gare shi kuma bahago ne da
mashi shi ke yaƙi. A
kowace shekara ake bukin kamun kifi na garin Argungu akwai wasar maharba ta daɗin hannu. Haka kuma, da duk sarkin baka
ya haɗa biki na suna ko aure, ko naɗin sabon sarki akwai wasu gwajin daɗin hannu ta musamman. An ce, mai daɗin hannu ko da jefa da dutse ne, to ko a
baka da bindiga duk za a same shi haka. Albarkan hannu ya fi daɗin hannu, domin mai albarkar hannu komai
ya ajiye yana ƙaruwa
da yaɗuwa har sai kowa ya wadata. A nawa
tunani “albarka” kalmar Larabci ce” dole akwai sunan da suke yi masa gabanin
zuwan Larabawa. Ina zaton gabanin Larabci suna amfani da kalmar “Marmasa” abin
da ke barbaɗa zuwa ya je ko’ina kowa ya samu. Idan
mai hannu da shuni ya shigo jama’a za a ji talakawa na tambaya: “Ko ta Marmasa”?
Wai ko ya ɗan ba su wani abu? A nan nake zaton
Sunan hannun irinsu “Marmasar hannu”, Allah Masani.
Ɗangantakar Hannun da Abinci.
Ayyukan da hannu ke yi sun fi na cin
abinci yawa, amma duk abincin da ya shigo hannu zuwa baki, hannu ya nemo shi.
Zantukan hikima da karuruwan magana da suka danganta hannu da baki suna da
yawa. Haka kuma ma’anoninsu abin a lura da su ne, a yi nazari: Ga kaɗan daga cikinsu mu yi nazari bisa taken
wannan fasali.
1.
Hanun bawan baki
2.
Hannu baka hannu akushi
3.
Hannu mai miya aka lasa
4.
Gatarin tuwo
5.
In wanke goma in tsoma biyar
6.
Kowa ya ɗebo da zafi bakinsa
7.
Kuturu da kuɗinsa, alkaki sai na ƙasan kwano
8.
Babbar yatsa ko ba ta cin tuwo ta iya ɓare malmala
9.
Bakin wani ba ya suɗe wa
hannu wani miya.
Komai nisan baki ko kusancinsa ga abinci
hannu ke sadar da shi da abincin don haka ake ganin sa bawa ga baki. Aikinbaki
kawai ya buɗe ya jira hannu, idan ya gaza zuta ɗiba yana kai baki, ya zama hannu baka
hannu akushi wato cin yunwa ke nan. Da hannu ake ɗanɗanar
daɗin miya da jin gishirin ta, shi kuma ake
suɗewa don lashe ragowar miyar da ke hannu.
Yatsun duka suna shiga cikin cin abinci ban da babbar yatsa, domin ita ɓare malmala ne aikinta. Yatsun ke himmar
cin abinci, amma idan an yi amfani da tafin hannu ya zama rugewa na handama da ake
kira gangame ruge. Ko da sha’anin kuɗi ne
ba abinci ba aka ce wa mutum: gangame ruge ya zama mai zari, ficen da hannu ya
yi wajen katsar abinci yana ba baki shi ya sa ake yi ma sa kirari da “gatarin
tuwo”. Wannan ya tabbatar da cewa bagiren hannu yaƙin cin abinci da wajen karin magana da
zantukan azanci ba ƙarami
ne ba. A cikin wasannin raha tsakanin Sakkwatawa da ranawa an ce:
Wai
wata mahaukaciya ake kira Ladi, ta je wani gida ak ba ta abinci tana jin yunwa
sosai ta zauna ta fara ci. Aka lura a haukace ta hau tuwon hannu baka hannu
akushi. Can sai jama’ar gida suka ce”, Ladi me ake ciki? An ƙoshi? Ta zura musu na gani, ta ce: “To,
wa ya iya gane wanga al’amari, tun da hannu sa wa yake ana sharɓewa”.
Sa
Hannu a Al’adance
Matsayin hannu a al’ada ya zarce na cin
abinci da faɗa har ya kai na babbar magana. A tunanin
Bahaushe sa hannu, magana ce mai faɗi
sai an ji mafarin ta za a iya fassara ta. Ganin irin dambarwar da ke ga kalmar
“sa hannu” ya kamata a ɗora ta a sikelin al’ada a ga irin mauyinta,
Ga wasu ‘Yan zantukan da ke waƙiltar
“sa hannu” da na tsinto.
a)
Sa hannu yana ɗaukar ma’anar sa hannu na taimako.
b)
Sa hannu yakan ɗauki ma’anar shiga cikin al’amari
c)
Yana da wata fassara ta sa hannun alƙalami na shaida (signature)
d)
Yana da fassar taya mutum wani aiki ba don ya kasa ba yana
neman taimako, a a, albarka yake nema don haka mafaɗin ke cewa: “wane a sa muna hannu ba ga
ido ba”.
e)
Yana ɗaukar ma’anar duka. Wa ya sawa yarona
hannu?
f)
Ana fassara shi da shigar da hannu cikin wani abu don lulube,
kasada, da tabbatarwa.
Kai tsaye muna ɗaukar fassar Alhaji Muhammadu Narayau
Makaɗin dambe a Zamfara (Bukuyum) a waƙarsa da yake yi wa wani ɗan dambe a ƙasar Bunza wai shi Kogo taken wakar shi
ne:
Jagora: Kogo
ba a sa ma hannu
Yara: Ko was
sa da gangan yay yi
Jagora: Ga
‘yan dambe sun naɗe hannu
Yara: Sun
ce ba su yi sun tuba
Gindi: Kogo
ba a sa ma hannu
:
Ko was sa da gangan yay yi.
Mai wayo da hankali ya sa hannu cikin
kogo bayan ya san da cewa, Kogo sai da hayaƙi, ko hayaƙi fid da na kogo, kuma ya ga ɗan dambe mai suna “Kogo” in ya kama shi
da gangan ya yi. Wani makaɗin zari ya fito da irin wannan fassara
yana wasa sarkin Maƙera
Balarabe Bunza yana ceewa:
Jagora: Ina
nika samun mahaukacin yaro wawa?
:
Ya tankwahe wando ya sa ƙafa
ramin kura.
Sai da ya kira yaro “mahaukaci” kuma
“wawa” domin wanda zai jaye ƙafar
wandonsa, ya saka ƙafar
tsirarar ta ramin kura, ba ƙafar
yake so ba ƙarya
yake yi. Bahaushe na cewa, hanjin jimina akwai na ci akwai na yarwa. A cikin
wani labarin raha an ce:
Makaho
ne ya tarar da an farauto jimina, ana raba nama. Ya ɗan tsaya domin a ba shi na tausayawa. An
san hanjin jimina ba sa ciyuwa, wanda duk ya yi izgilin cin su ajalinsa. Aka ce
wa makaho “ga rabonka nan gabanka kwashi: Ya sa hannu ya laluba ya ji a binda
yawa, babu iyaka ka ce shi ya yi rabo ya ware wa kansa, Ya ci gaba da sa hannu
yana laluba, sai ya ce: “Kai mai ido, anya! Abin nan na ci ne”? Dole da wata magana
mai dio ya ware wa makaho, irin wannan kashi.
Ka ji aiki da hankali wanda Hausawa suka
ce, Ya fi aiki da agogon hannu. Ashe, sa hannu. Ashe, sa hannu alƙalanci ne, ko ido bai gani ba ya yi
hukunci.
Hannu
a Hukuncin Al’ada
A cikin al’adun mutane dokokinsu suka
fito. Doka tantagaryar al’ada ce, matuƙar aka take ta, to, al’ada aka taka. A cikin
kowace doka saukakka ce daga mahalicci ko halittu suka ƙirƙiro abar su? Al’ada na da babbar hurumi
a cikin shi kuma hannu da al’adar doka yake tafiya, za mu yanke hukunci idan
mun dubi waɗannan zantuka.
1.
Hannu dumu-dumu
2.
Na ɗebe hannuna
3.
Babu hannuna babu ƙafata a ciki
4.
Hannu-da-hannu
5.
Hannun karɓa, hannun maidawa.
A ko’ina Bahaushe ya yi amfani da hannu
dumu-dumu shaida ta tabbata ga mai bayar da ita. Ko ya ce: na ɗebe hannuna”, alƙalami ya bushe, muddin an tabbatar da
kasancewar hannayen dumu-dumu, Kasancewar mutum bararre ga abin da ake zarginsa
shi ke sa ya ce: “babu hannuna babu ƙafata”. Ƙafar za ta iya kai shi wurin da ake
zarginsa, amma sai da ya fara gabatar da “hannu” ya kawo ƙafa. A cikin sha’anin ciniki da fatauci
da saye da sayarwa, ma’ana, ga kaya, ga kuɗin
kaya. Ciniki ya tabbata ko an ƙulla
ya tashi a nan ake hannun karɓa, hannun mayarwa wato duk karen da ya
yi cizo da gashinsa ake magani.
Hannu
a Wasu Muhimman Maganganu
Hausawa na cewa, aikin wani sai kallo,
Hannu na fitowa cikin wasu muhimman zautuka da ke neman fashin baƙi ga wanda Hausarsa ba ta ji gishiri ba.
A dubi waɗannan zantuka sosai domin misali.
1.
Hannu ya iya jiki ya saba
2.
Hannu ba ka da tsoro
3.
Na hannu
4.
Hannu har gulbi
5.
Ban hannun makafi
6.
Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka
7.
Hannun adashe
8.
Hannun adashe
Bahaushe a ko’ina ba cimakwance ba ne,
mutum ne mai son ya nema wa kansa na kansa. Duk wata tsirfa da ake yi, yana son
ya yi na kansa ya mora wa kansa. Duk wata dabara ta azanci na tanadin sama wa
kai abinci yana ce da ita sana’ar hannu. Idan an kware sosai ga aikata wani abu
ko samar da wani abu ake, yi wa gwanin ko ƙwararren kirari da cewa hannu ya iya
jiki ya saba. Hannu muhimmi ne, a koyaushe sai an fara gabatar da shi domin shi
ke yi wa jiki amfani, ba jiki ke yi masa aikin amfani ba. Kariyar da yake yi wa
jiki ga duk abin da ke yi wa rayuwa barazana shi ne dalilin yi masa kirarin
hannu ba ka da tsoro. Samar wa rayuwa abin yi da kare rayuwa ga hadurra da kuma
manyan ayyukan da hannu ke yi wa rayuwa. Da ba don hannu ba rayuwa ta tagayyara
komai dabarar mai ita.
Daga cikin manyan muhimman abubuwa da sunan
hannu ke taka rawa akwai ‘yancin ɗan Adam. Tsananin nauyin kalmar rashin
‘yanci ga ɗan Adam watau, “bauta” ya sa Bahaushe ke
amfani da kalmar “Nahannu” a madadin ya ce “bawa”. Zumuntar bawa ko kusantar bawa
ga uban gidansa ya sa ake ce masa “Nahannu”. Haka nan, idan abota ta ƙarfafa kusanci aboki da aboki ya cika
akan yi amfani da “hannu” a nuna zumuntar abokantaka a ce: “wane da wane hannu
har gulbi/kogi”. Ko dai tafiyar da suke yi ana jifar hannu tattare; ko kuma ƙulla hannun juna tare ana tafiya duk
tabbatar da zumuncin soyayya ne. Da an ga an saɓa wa juna ga ra’ayi, ko fahimtar juna,
ko an sha bamban da juna a hanya, nan ake amfani da faɗar, ai mun yi ban hannun makafi da shi.
Ashe ban hannu na gaisuwa gaba da gaba ake yin shi, a yi ido huɗu don ƙara danƙon zumunci, makaho da ba ya gani ana miƙa hannu gabas yana yi yamma. Tabbas,
muhimman abubuwa na soyayya da akasin ta, duk “hannu” ake amfani da shi wajen
tabbatar da su. Idan hannun juna na haɗe
babu abin da ke buwaya. Bisa ga al’ada, haɗin
kai da haɗa ƙarfi wuri ɗaya a tunkari kowace irin matsala har
sai an shawo kanta sh ya sa Bahaushe ke da karin magana hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka, A taru a yi abu tare ya fi
a y shi wawware ko daban-daban. Alhaji Sulaiman Dundaye mazauni Kano, a waƙarsa ta siyasa da ya yi wa jam’iyyar NPN
bayan fitansa PRP cewa yake:
Hannun ɗaya bai aza ɗaki
Kashin ɓera bai taki,
Mai aure ta fi kilaki
In ban da shirin
lalata.
Amshi: Yan santsi kun zama kaya
Da ma ba ma ƙaunar ku
Mu mun koma Enpi’yan
(NPN)
(Sulaiman
Dunɗaye: 1982)
Hannu
a zamanance
Buƙatar bincike ya tabbatar da cewa
matsayin hannu ga al’adar Bahaushe idan aka nazarci yadda ake lugudensa a adabi
ba ƙaramin
filin tunanin Bahaushe ya mamaye ba. A kowane zamni za a ga kalmar “hannu” na
taka rawa a cikin tunanin al’ada. Dubi waɗannan
batutuwa da idon basira.
1.
Aron hannu
2.
Hannu Adashe
3.
Hannu mai tafiya/Matuƙi
4.
Satar hannu
5.
Hannu saƙo
Masana adabi musamman waƙoƙin baka da rubutattu idan sun fahinci
wani adiibi ya aro karin wani ko muryarsa ko fasaharsa kai tsaye ko kaikaice
sukan ce: “aron hannu” aka yi. Haka yake ga duk wani aiki ko fasahar hannu irin
su ginar yumɓu da ta zamani, ko ɗinkin sutura da dai sauransu akan ce,
“an yi aron hannu wane” wato an kwaikwaye shi, shi ya riga yi da baya aka zo da
irin nasa salo. Kai tsaye masu adashi suka aro wannan fasaha ta hannu idan mai
adashi kwasa ɗaya zai yi, a ce “hannu ɗaya”, Idan kwasa biy ne a adashi ɗaya, a ce: “hannu biyu”, ga su nan dai.
A da makaho in ya kuskuri hanyarsa mai gani ya lura zai jawo hankalinsa da faɗan: “hannunka mai sanda” ko “hannunka maras
sanda”. Haka yake yau a zamanance, da can da tuƙi na hannun hagu sai a ce: kiliya na
hugu, yayin da ta koma dama, aka ce kiliya ta koma dama, amma idan ana jawo
hankalin mai tuki akan ce: yana kan hannunsa ko ya sake hannunsa na tuƙi. Kai! Hatta da haɗari ya haddasa idon aka je bincike, ƙoƙari ake a gano a kan hannunsa yake, ko
ya sake hannunsa? Idan ya sake hannunsa, za a ce: “Ya yi aron hannu”. Idan saƙon biyan bashi ko kyauta ko biki ko
sadaka ne aka bayar a ba wani shi kuwa ya isar da saƙon, mai karɓa idan ya haɗu da mai bayarwa yakan ce, wane na ga
hannunka, ko hannunka ya iso, ko mun haɗa
hannu da wane (a ambaci sunan wanda ya kawo saƙon).
Sakamakon
Bincike
A ɗan
binciken da wannan takarda ta yi, ta gano abubuwa da ɗan dama da suka kakkamo hannun su ka yi
garkuwa da sunansa wajen isar da saƙo. Tunanin Bahaushe Ya yi madogara da
hannu wuraren daban-daban. A kan abubuwan da aka nazarto ga hannu an gano
abubuwa guda biyar:
a)
Babu sassan jiki da ya kai sunan hannu sassakaɗuwa cikin tunanin Bahaushe
b)
A tunanin Bahaushe hannu shi ne ubangijin jiki, jiki bawa ne
c)
Yadda tunanin Bahaushe ke kallon hannu hagu ya yi canjaras da
yadda Allah Ya halitto shi ga jikin ɗan
Adam
d)
Hannu ya mamaye sauran gaɓoɓin
Bahaushe cikin tunanin adabinsa harshensa da al’adunsa.
e)
Sassan jikin mutane sun cancanci shiga cikin manhajar koyar
da adabinsu, harshensu, da al’adunsu.
Naɗewa
Babu binciken da ya fi muhimmanci kamar
wanda ɗan Adam zai san kansa da kansa. Abin da ake
nufi da cigaba shi ne sanin inda aka kwan domin sanin wurin da za a tashi.
Tashin da za a yi zuwa gaba shi ne “cigaba”. Idan aka kasa zuwa gaba duk abinda
aka yi sunansa” ci baya” domin da a koma gidan jiya, da a tabbata inda ake, duk
ba a “cigaba” ba. Manazarta da masana da matarka adabi, da al’ada, da harshe ya
kamata su fara tunanin abubuwan da ke kusa da su da ke buƙatar nazari su ɗan ce wani abu kansu tun ba a rigaye su
ba, aka lalata fage ba a taɓuka komai ba. Yau ibadoji sadarwa ta
cigaba a wurarne iadoji, da taimakon ilmi, da siyasa, ci ko’ina za a taras da
masu fassara wa kurame bayanan da ke gudana da gaɓɓan jikinsu (ishara). Ba dole sai mun ari
na wasu ba, mu dai fara saka namu a manhajojin karantar da yaranmu ya shiga
makaranta sosai a san yadda za a tafiyar da shi. Da fara tunanin nazarin hannu
a tunanin Bahaushe ban yi zaton akwai abubuwan cewa da yawa ciki ba. Bayan da
na kammala wannan bincike sai na sake yin wani kan ‘yatsar manuni”..., ina gama
shi na ga wata babbar tazara ta magana da hannu/hannaye. Lallai hannu ya yi
tasiri sosai cikin adabi, da al’ada, da harshen Bahaushe. Fatata samun
gudunmuwa daga masana mu ga yadda za mu haɗa
hannu mu ciyar da Hausa gaba.
Manazarta
1.
Bunza, A. M. (2022).
“Sarrafa Yatsar Hannu a Bahaushiyar Magana.” Takardar Bincike da aka Gabatar a
Jami’ar Maiduguri Domin a Wallafa a Kundin Girmama Farfesa Minkaila.
2.
Fischar, S. R. (2003) A History of Writing. London: REACTION
BOOKS, LTD 79 Farringdon Road.
3.
Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa,
Edenburgh: University Press.
4.
Malumfashi, I. (Ed)
(2019). Labarin Hausa a Rubuce
(1927-2018). Zaria: Ahmadu Bello University Press.
5.
McNeil, D. (1992). Hand and Mind. What Gestures Reveal About
Thought. Chicago: University of Chicago Press.
6.
Morris, D. et al
(11979). Gestures: Their Origin and
Distribution. London: Cape.
7.
Pawlak, N. Hanwa, R.
Izabel, W. ed (2016).African Studies
Forging New Perspectives and Directions, Warsaw: EUPSA Publishing House.
8.
Sommer, G., Vierke, C.
(eds). 2011 Speach Acts and Speach,
Events in African Languages. Koln: Koppe.
9.
Schon, J. F. (1885). Magana Hausa Native Literature Proverbs,
Tales, Pables and Bisto Fragment in the Hausa Language. Society for
Promoting Christian Knowledge. North Umberland Avenue, London.
10.
Umar, M. B. (1984).
“Symbolism in Oral Poetry: A Study of Symbolical Indices of Social Status in
Hausa Court Songs.” M. A. thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
11.
Will, I. (2010).
“Function and Meaning of Symbolic Gestures in th Hausa Films.” in : S. Baldi,
H. M. Yakasai (eds). Proceeding of the
3rd International Conference on Hausa Studies: African and European
Perspectives. Napoli: Universita di Napoli “L’Orientale” Dipatimento di
Studi e Ricereche in Africa e Paesi Arabi, 329-341.
12.
Will, I. (2014).
“Beyound the Words. The Role of Gestures Contemporary Hausa Sermons (Wa’azi).”
Unpublished Paper Presented at the International Conference “African Studies in
the Contemporary World.” University of Warsaw, October 14-10-2014.
13.
Will, I. (2015).
“Gestures and Indirect Statements As Means of Expressing Emotions and Opinions
Among Hausa Women.” In: G. C. Batic, S. Baldi (eds). Selected Proceedings of the Symposium on West African Languages
(Naples, 27-28 March, 2014) (Studies Africanistic/ Serie Ciado- Sudanese 7)
Naples:11 Tacoliere Universita I.Oriental, 233-248.
14.
Yahaya, I. Y. (1988). Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-rubuce Cikin
Hausa. Zaria: NNPC.
15.
Yakasai, H. (2014).
“Gesture As Negative and Emphatic Markers in Hausa.” in: N. Pawlak., E.
Siwierska., I. Will (eds) Hausa and
Chadic Studies in Honor of Professor Stanislaw Pikazew: Warszawa: Dom
Wydawniczy Elipsa 1188-199.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.