Ticker

6/recent/ticker-posts

Halilu

Bayarwa: Ruwa-ruwa-ruwa Halilu,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Ɗan sarkin ruwa,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Limamin ruwa,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Mai wandon ruwa,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Mai rigar ruwa,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Mai hular ruwa,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Takalmin ruwa,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Ka ba mu ruwa mu sha,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Gero ya bushe,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Ka ba mu ruwa mu sha,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Dawa ta bushe,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Ka ba mu ruwa mu sha,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Tsuntsu na kuka,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Ka ba mu ruwa mu sha,

Amshi: Halilu.

 

Bayarwa: Ruwa-ruwa-ruwa,

Amshi: Halilu.

Muhammadu

 

Bayarwa: Allah ba mu ruwa,

Amshi: Muhammad.

 

Bayarwa: ko yau ko gobe,

Amshi: Muhammad.

 

Ko tashin asuba,

Amshi: Muhammad.

 

Ko yanzu ya zubo.

Amshi: Muhammad.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments