Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Ka Taɓa Yiwa Mace Don Nuna Mata So Da Ƙauna

So fa wata kyauta ce ta musamman daga Allaah AWJ da Yake baiwa wasu za6a66un bayinSa maza da mata kai har ma da dabbobi. In kuwa abin ya tashi daga so ya koma ƙauna to fa zance ya ƙare.

Duk wanda ka ji yana lissafin nawa ya kashe wajen hidimtawa macen da yake so to bai san so 👍🏾 ko ƙauna 💗 ba. Ai in ciwon so ya kama mutum maganinsa kawai shi ne gani ko ji ko kasancewa tare da kwayar cutar da ta kama shi.

Wani abin mamaki shi ne cutar so ko ƙauna masu ita ba sa fatan su samu sauƙi ko waraka in dai cutar ba mai cutarwa ba ce kuma ba mai kisa ba ce. Sauƙi daya kawai za ka ga masoya juna na nema wato su yi aure wanda wannan shi ne maganin ciwon so ɗaya tilo. Aure!

Babu nisan gari ko nisan kwana babu tsawon tafiya ko zafin rana ko ma a ce sanyin hunturu, kai ko ana ruwan ƙankara kuma komai duhun dare ko ana markamarka ko a ce jaura ce da jikinsa duk ba zai shanye su ya nemi ƙari ba.

Kai komai tsananin tudu ko zurfin kwari sannan babu faɗin teku ko haɗurran dake cikinsa balle wajensa ko samansa ko a ce wani ƙungurmin daji ne da aljanu da iblisai suka cika shi suka yi masa ƙawanya suna cin kasuwarsu a ciki.

Ko kuma ka ce sheɗanun mutane y'an ta'adda y'an fashi da makami y'an kidmashin da dai sauransu suka yiwa hanyar zuwa ƙwanƙwasar zuciyar masoya katutu da masoyi ba zai iya ketawa ya kutsa ya fasa taro don ya isa gare ta ba rabin rai gatar lafiyarsa.

Amma fa sai in son ya kai so ƙaunar ta kai ƙauna har ta ma wuce. Sai in tamatar ta cancanta ta kai a sadaukar da rai don a aureta. In kuwa ta zam sa6anin haka to kallo ɗaya ma na kirki don a yi zina da ita ba za a yi mata arziki da shi ba.

A nan ne za ka ga jarumta da juriya da jajircewa. A nan ne za ka ga ana azumin kwana uku ba don neman lada ba sai don neman a kalli mace kallon ma a 6oye don sanyaya zuciya kuma ko da matar ba ta gari ba ce. So mai sa sa6o mai hana ganin laifi.

A wannan shaƙar ce ta so da ƙauna za ka san me Hausawa ke nufi da karin maganar nan dake cewa "Sa kai ya fi bauta ciwo." Ba ci ba sha ba barci balle mutum ya nemi hutu da sharholiya. Fafutuka kawai ba ƙaƙƙautawa ita ce abar yi.

Sai ma an gamu anyi ido da ido tsakanin masoyi da masoyiya a nan ne fa za ka ga hawayen gwal na zuba don nuna lobayya, ka ji sautin ƙauna mai garɗi na 6u66ugowa daga gungumen duwatsu, ka ga bege irin wanda ba ka ta6a ji ba daga tsatson zuci ana 6arinsu.

Don haka zuba mai Naira dubu ko fiye akan kowace lita a abin hawa mai dauke da dukkan ni'imomin sauƙaƙe wahalar tafiya zuwa dausayin soyayya da ƙauna ai bai kai kiftawa da bisimillah ba a tsadar hidimtawa wacca ake so ake ƙauna.

Ni dai ganau ne kuma jiyau ne na abin da masoya musamman maza kan yi a fagen nunawa mace irin darajarta a zuciyarsu. Abin dai ba a cewa komai. Ban sani ba ko har yanzu akwai irin wannan son da ƙaunar?

Don alamu na nuna cewa masoyan zamani kuɗi ne ma'aunin so da ƙaunarsu. Ku ji fa don Allaah! Hmmm, Mafi sauƙi dai a nan shi ne kawaikawai mu bar zancen. Sai an jima.

Daga Taskar

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960

A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

Me Ka Taɓa Yiwa Mace Don Nuna Mata So Da Ƙauna

Me Ka Taɓa Yiwa Mace Don Nuna Mata So Da Ƙauna

Post a Comment

0 Comments