Ticker

6/recent/ticker-posts

Falalar Ambaton Allah {2}

Yaku bayin Allah! ambaton Allah wato zikiri shi ne yake raya zukata, zukata ba su rayuwa sai da shi, Buhari ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Abu Musa Al’ash’ari (RA) daga Annabi () ya ce: “Misalin wanda yake ambato ko tuna Ubangijinsa da wanda ba ya ambato ko tuna Ubanginsa kamar misalin mai rai ne da matacce.”

Hakika zukata ba za su samu tabbatuwa da natsuwa ba, ko su samu jin daɗi su samu sa’ada ba, sai tare da zikirin Allah da tunawa da Shi. Allah Madaukaki Yana cewa:

الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللَّهِ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ

. “Waɗanda suka yi imani, zukatansu suna samun natsuwa ne da ambaton Allah. Ku saurara! Da ambaton Allah zukata suke samun natsuwa.”.

Ambaton Allah shi ne ke kawo mafita a bayan kunci, ya kawo sauki a bayan tsanani, ya kawo farin ciki a bayan wahala da damuwa. Shi yake kwaranye abubuwan da suke kawo bakin ciki ya saukaka al’amura ya tabbatar da raha da sa’ada a duniya da Lahira. Babu abin da yake magance bakin ciki ya gusar da tsanani kamar ambaton Allah da zikirin Allah Madaukaki. Annabinmu () ya kasance a duk lokacin da wani abin bakin ciki ya same shi yana cewa: “La ilaha illallahul azim, la ilaha illallahul halim. La ilaha illallahu rabbus samawati wa rabbul arshil karim.” Ma’ana: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai haƙuri. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa kuma Ubangijin Al’arshi Mai girma.” Sannan Mai Tsira da Amincin Allah yana cewa: “Addu’ar ma’abucin kifi: “La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimina.” Ma’ana: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Tsarkinka ya tabbata, lallai ni na kasance daga cikin azzalumai.” Babu wanda zai fada a cikin bakin ciki da zai yi addu’a da ita face an kwaranye masa bakin cikinsa.”

Ina roƙon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alƙur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai

الله تعالى أعلم

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​

****************************
Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************

Telegram

https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx

WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.

Sheikh Muhammad Auwal Albany

Post a Comment

0 Comments