Ticker

6/recent/ticker-posts

BABI NA BIYAR - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 122)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

WAƘOƘIN TATSUNIYA

5.7 Tatsuniya

Tatsuniya ƙagaggen labari ne mai tattare da hikima da fasaha da akan gina bisa wani jigo na musamman da ya danganci ilimantarwa ko faɗakarwa ko koyar da jarumta ko dabarun zaman duniya ko gargaɗi da makamantansu. Akan samu waƙoƙi a cikin wasu daga cikin tatsuniyoyin Hausawa. Irin waɗannan waƙoƙi na cikin misalan waƙoƙin gargajiya na Hausawa. Duk da cewa maƙasudin wannan littafi shi ne fitowa fili da waƙoƙin gargajiya na Hausawa, za a kawo wasu daga cikin tatsuniyoyin kafin bayyana waƙoƙin da ke ƙunshe a cikinsu.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments