Ticker

6/recent/ticker-posts

5.7.1 Tatsuniyar Icen Ƙosai - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 122)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

5.7.1 Tatsuniyar Icen Ƙosai 

Ga ta nan ga ta nanku:

Akwai wata yarinya ne dai uwarta ta mutu. Ta kasance maraya a gaban kishiyar uwarta. Kullum kishir uwarta na gallaza mata idan ubanta ba ya nan. Ita ce take shara, take wanke-wanke da wanki da ɗebo ruwa a rafi da kuma kai dabbobi kiwo.

Ana nan ana nan, sai kishiyar uwar ta ƙudiri ta hallaka ta ta hanyar yunwa. Saboda haka ta ƙuduri aniyar ba za ta sake ba ta abinci ba. Da gari ya waye ta ce mata: “Ɗauki gorar ruwanki ki tafi kiwo.” Yarinyar ta ce: “Umma ban ci ɗumame ba.” Kishiyar uwar tata ta daka mata tsawa: “Shashashar ‘ya, wuce ki ba ni wuri!”

Haka yarinyar nan ta nufi hanyar jeji tana tafe tana kuka. Tana cikin tafiya sai ta haɗu da babanta zai dawo gida. Ya tambaye ta me ya faru? Sai kuwa ta sanar da shi cewa yunwa take ji. Uban nata ya ɗauki sisin kwabo ya ce mata ta sayi ƙosai. Yarinyar kuwa ta je wurin mai ƙosai ta sayi ‘yan biyu sisi ta wuce da su jeji wurin kiwo.

Bayan ta isa jeji tumaki da awakin da take kiwo sun fara kiwo, sai ta zauna a gindin bishiya ta ɗauko ƙosanta guda biyu. Ta cinye guda ɗaya. Ragowar ɗayan kuwa a maimakon ta ci, sai ta shuka shi a ƙasa. Haka ma ruwan gorarta, ta sha rabi, rabin kuma ta yi wa ƙosan da ta shuka bayi da shi.

Da ta dawo gida kishiyar uwarta ba ta ga ta galabaita sosai ba, sai ta ce a zuciyarta: “Ke jaruma ko? Bari mu gani zuwa gobe, yunwa sai ta kashe ki.” Haka kuwa aka yi, washegari ta kora ta kiwo ba tare da ta ba ta abinci ba. Yarinya ta kama hanya tana kuka har ta isa wurin kiwo. Tana zuwa ta tarar da ƙosan da ta shuka ya tsiro ya yi nisa tsololo yadda ba za a iya ciran ‘ya’yan ba. Ko ƙarshensa ma ba a hangowa tsabar tsawo. A nan yarinyar ta yi farin ciki. Sai kuma ta fara waƙa kamar haka:

Ƙasa-ƙasa dai icen dabino,

Sauƙo icen ƙosai,

Ba don rashin uwa ba,

Ba zan shuka ka ba.

Sai kuwa ta ga bishiyar ta fara saukowa a hankali a hankali. Har dai ta sauko daidai yadda yarinyar ke tsaye. Nan kuwa yarinyar ta kalli ‘ya’yan ƙosai sun nuna sai maiƙo suke yi suna ƙamshi bus-bus. Ta cira ta yi ta ci, sai da ta ƙoshi. Sai kuma ta sake waƙa kamar haka:

Sama-sama dai icen maraya,

Koma icen ƙosai,

Ba don rashin uwa ba,

Ba zan shuka ka ba.

Sai kuwa ta ga bishiyar ƙosai na komawa sama a hankali a hankali, har ya ƙule ƙololuwa. Lokacin da yarinyar nan ta dawo gida, kishiyar uwar ta yi mamaki. Ta daka mata tsawa: “Me kika je kika ci?” Yarinyar kuwa ta ce ai ba ta ci komai ba. Kishiyar uwar ta ce ƙarya take yi. Amma yarinyar ta ƙi faɗa mata.

Haka dai aka ci gaba da yi kullum kishiyar uwar yarinya na sa ido don ta ga yarinya ta mutu da yunwa. Amma sai ta ga a maimakon ta rame, sai ƙiba da kyau take ƙara yi. Rannan sai kishiyar uwar ta yi shawarar za ta je ta ga me wannan yarinya ke ci a jeji. Ta bi ta a sanɗa har suka isa wurin kiyo. Nan kuwa uwar kishiyar ta ga duk abin da ya faru.

Uwar kishiyar nan ba ta zarce ko ina ba sai gidan sarki. Da ma sarkin garin wani azzalumi ne. Duk wani mai arziki sai ya ƙwace arzikin. Da isarta ta kwashe labari duk ta faɗa masa. Nan kuwa ya ce da fadawa maza a shirya masa sirdi a je wurin bishiyar nan. Da ma sarkin yana da wani ɗa, saurayi kyakkyawa. Shi kuwa wannan ɗa mai hankali ne da tausayin talakawa. Don haka ya ba da shawarar kada a taɓa wa yarinyar nan bishiyarta. Amma sarki bai kula ba.

Haka aka ɗunguma gaba ɗaya aka nufi wurin bishiya. Ana zuwa aka ga bishiyar ƙosai tana ta ƙamshi amma ba wanda zai iya kaiwa ga ‘ya’yanta. Uwar kishiyar nan ta zo wai za ta gwada waƙar da yarinya ta yi. Ta fara waƙar da gwardon muryarta kamar gogen raki:

ƘASA-ƘASA DAI ICEN DABINO,

SAUƘO ICEN ƘOSAI,

BA DON RASHIN UWA BA,

BA ZAN SHUKA KA BA.

Ta yi ta waƙar har sau uku amma babu abin da ya faru. Sai ta ba wa sarki shawara a je a kamo yarinyar ta zo ta yi waƙar da kanta. Haka kuwa aka je aka jawo wannan yarinya tana ta kuka. Aka sa ta dole ta yi waƙar ba tare da tana so ba. Sai kuwa ga bishiyar ƙosai na saukowa a hankali, har ta zo ƙasa-ƙasa. Fadawan sarki suka tsinki ‘ya’yan suka miƙo wa sarki. Da ya ci ya ji daɗin da bai taɓa cin wani abinci irinsa ba. Nan da nan sarki da fadawa da sauran mutanen gari azzalumai suka fara rige-rigen hawa wannan bishiya. Suka ɗale gaba ɗaya da yake bishiyar ƙatuwa ce, kowa na ta faman ci. Wasu suna ɗurawa a aljihunan manyan rigunansu.

Ɗan sarki da ke tsaye a gefe sai ya zo wurin yarinyar nan. Ya raɗa mata a kunne cewa, ta yi waƙar da bishiyar za ta tashi sama. Nan kuwa ta yi wannan waƙa kamar yadda ya faɗa mata. Sarki da azzaluman gari da azzaluman fadawa sun shagala da cin ƙosai mai ɗan karen daɗi. Ba su ma ankara da bishiyar nan tana tashi har ta luluƙa da su cikin gajimare ba.

Waziri da ya leƙa ya dubi sauran fadawa ya ce: “Allah Ya kawo mana ƙarshen zalunci ta hanyar wannan marainiya. Yanzu ba abin da ya fi sai a naɗa wa Yarima ɗan sarki sarautar wannan gari.” Ba tare da musu ba dukkanin fadawa suka aminta. Da ma duk suna son Yarima saboda hankalinsa da kuma adalci. Ba tare da ɓata lokaci ba aka shirya gagarumin bikin naɗin sarauta. Ranar biki aka ɗafa abinci iri-iri. Talakawa kowa ya ci sai da ya bari. Ga kayan sha kuwa sai an zaɓa.

Bayan komai ya lafa, sai ɗan sarkin da ya zama sarki ya aika a je a nema masa auren mareniyar nan. Aka je aka samu ubanta. Bai yi musu ba ko daidai da na ƙwayar zarra. Nan da nan aka haɗa ƙayataccen bukin aure. Shagalin da aka yi har ya fi na naɗin sarautar. Kowa ya yi farin ciki da wannan biki.

A can kan bishiyar ƙosai kuwa, sarki da kishiyar uwar marainiya da sauran azzaluman gari ba su ankara ba har sai da suka tsinci kansu a can cikin gajimare. A nan suka fara zare idanu. Suka duba suka ga ba sa ko hango doron ƙasa. A nan idanuwansu suka raina fata. Suka tsaya nan masu kuka na yi masu zawo na yi.

Ƙurunƙus!

Ba dan gizo ba da na yi ƙarya …

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments