Ticker

6/recent/ticker-posts

BABI NA BAKWAI - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 140)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

WAƘOƘIN BARA

7.0 Gabatarwa

A ɓangaren bara ma, ba a bar waƙoƙin gargajiyar Bahaushe a baya ba wurin taka muhimmiyar rawa. Mabarata na amfani da waƙoƙi daban-daban yayin gudanar da bararsu. Wasu daga cikin waƙoƙin bara na ɗauke da faɗakarwa da maganganun imani da tunasarwa game da Mahalicci da mutuwa da tashin ƙiyama da dai makamantansu. Wannan ya kasance babbar dabarar bara, domin kuwa irin waɗannan maganganu na sa wanda ake roƙa ya ji imani ya shige shi har ya ɗauki sadaka ya ba wa mabaraci.

Waɗanda aka fi sani da bara a ƙasar Hausa sun kasu kashi biyu kamar haka:

i. Yara, waɗanda mafi yawa almajirai ne.

ii. Manya maza ko mata, waɗanda mafi yawa musakai ne.

Lura da wannan, za a iya cewa, manyan dalilan da sukan sa bara a ƙasar Hausa su ne (i) almajiranci ko kuma (ii) kasancewar mutum musaki. Akwai wasu dalilan bayan waɗannan da suka haɗa da maraici da rashi da annoba da dai sauransu. Wannan babi na ɗauke da wasu daga cikin misalan waƙoƙin bara a ƙasar Hausa.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments