Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
7.1 Ko Ɗan Ƙanzo
Wannan waƙar bara ce wadda yara ne suka fi yin ta, musamman almajirai. Akan yi ta ne domin neman abinci, wato ba kuɗi ko sutura ba ko wani abu na daban. Ga yadda waƙar take kamar haka:
Iya ko ɗan ƙanzo
Iya ko ɗan dako-dako,
Iya yunwa ba ta da hankali,
Iya ko gaya ne ba miya,
Iya na yi bara ba a ba ni ba,
Iya ko loma ɗaya ma,
Iya haƙuri ko ya je?
Wannan waƙa tana ɗauke ne da jigon bara kai-tsaye. Ta ƙunshi kalaman ban tausayi inda take nuna halin yunwa da mabaracin ke ciki, musamman inda yake furtawa da bakinsa “Yunwa ba ta da hankali!” Saboda yunwar da yake ji ne ma, bai tsaya zaɓen abinci ba. A maimakon haka, sai ya ce a ba shi ko da “ɗan ƙanzo” ko “ɗan dako-dako.” A gaba kuma yake ƙara kokawa da cewa ya yi bara bai samu ba, saboda haka “ko loma ɗaya ma” idan aka ba shi yana buƙata. Lallai waɗannan kalamai ne masu karya zuciya. Daga ƙarshen waƙar kuma sai ya saduda, inda yake tambaya ya zo ne, ko dai ya yi haƙuri ya wuce gaba?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.