Ticker

6/recent/ticker-posts

Ayye Mama

Bayarwa: Ayye mama ayye mama,

Amshi: Mamaye iye.

Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Ayye Halima kin tafiyarki?

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Don haka kin shige ɗakinki?

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: An ce Halima mun rabu ke nan?

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

Amshi: Mamaye iye.

Ayyaraye

 

Bayarwa: Ayyaraye nanaye,

Amshi: Wa aka yaye?

 

Bayarwa: Sadiya, Amshi: Wa za a kai wa?

 

Bayarwa: Amadu,

Amshi: Ayyuriri mu yi guɗa.

 

Bayarwa: An yaye, an yaye,

Amshi: Eh, an yaye.

 

Bayarwa: Shekaranjiya,

Amshi: Wa aka yaye?

 

Bayarwa: Sadiya,

Ko ba ta kai ba?

Amshi: Ayyuriri,

 Ta kai,

 Wa aka bai wa?

 

Bayarwa: Amadu,

 Ko ba ku bayar ba?

Amshi: Mun bayar.

 

Bayarwa: Mun ba shi har ga Allah,

Amshi: Mun bayar,

 Ayyaraye nanaye.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments