Bayarwa: Ayyaraye daure jure,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: ‘Yar tsohuwa mai ɗan ƙoƙo,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: Allah Ya kashe ki mu sha gumba,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: ‘Yar tsohuwa mai ɗan ƙoƙo,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: Allah Ya kashe ki watan gobe.
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: Yarinya daure-daure,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: Ba a kanki ne aka fara ba,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: Kuma ba a kanki ne za a ƙare ba,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: Aure cikin farilla ne,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: Da babu shi ke ma ba kya zo ba,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: A yau aurenki ake yi,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
Bayarwa: Gobe na ɗiyarki za ay yo,
Amshi: Ayyaraye daure jure.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.