Ticker

6/recent/ticker-posts

Ƙazama (Waƙar Niƙa)

Zanka wanka da wanki,

Ke yi maƙal-maƙal.

Zanka wanka da wanki,

Ke yi daƙal-daƙal.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi ƙazan-ƙazan.

 

Zanka wanka da wnki,

Ke yi mujur-mujur.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi kuca-kuca.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi kurun-kurun.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi ƙirin-ƙirin.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi baƙi ƙirin.

 

A’a wanke zannanki sauna,

Sun yi tilin-tilin,

 

A’a zanka wanka da wanki,

Ko kya yi fari-fari. (Illo, 1980: 8)

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments