Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Assalamu Alaikum

Bayarwa: Assalamu alaikum,

Amshi: Assalam!

Bayarwa: Masu gida ku buɗe ƙofa,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Masu gida ku buɗe ɗaki,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Ga ɗiyarmu nan mun kawo,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Mun kawo ta ɗakin ango,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Ɗiyarmu ba ta tsegumi,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Ɗiyarmu ba ta ƙarya,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Ango ga ɗiyarmu nan,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Kar ka je ka koya mata ƙarya,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Kar ka je ka koya mata tsegumi,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Muguwar sarkuwa ja’ira,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: A jefa mata bargon ‘yan wuta,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Haihuwa muke kira har kullum,

Amshi: Assalam!

 

Bayarwa: Haihuwa muke kira gun Allah.

Amshi: Assalam!

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments