Ticker

6/recent/ticker-posts

8.8 Akwai Ƙarancin Kalmomin Aro Cikin Waƙoƙin Gargajiya - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 154)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

8.8 Akwai Ƙarancin Kalmomin Aro Cikin Waƙoƙin Gargajiya 

Akan samu kalmomin aro a waƙoƙin baka da kuma rubutattun, musamman kalmomin Larabci da na Ingilishi. Wannan ya samu asali kasancewar Hausawa sun fara rubuta waƙoƙi bayan cuɗanyarsu da waɗannan al’ummu guda biyu. Amma su waƙoƙin gargajiya, ba su faye zuwa da kalmomin aro ba kasancewar tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta; wato dai tun kafin zuwan baƙin al’umma, Hausawa suna da irin waɗannan waƙoƙi na gargajiya, musamman waƙoƙin cikin tatsuniya da na wasannin dandali da makamantansu.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments