Ticker

6/recent/ticker-posts

8.6 Waƙoƙin Gargajiya Na Tafiya Da Lokaci Ko Yanayi - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 154)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

8.6 Waƙoƙin Gargajiya Na Tafiya Da Lokaci Ko Yanayi

Yawanci akwai lokuta na musamman da aka fi rera kowacce daga cikin waƙoƙin gargajiya. Waƙoƙin tashe dai an fi rera su cikin watan azumi, sannan da dare bayan an sha ruwa, wato dai lokacin tashe. Waƙoƙin gaɗa kuwa, da dare aka fi rera su, sannan a dandali, musamman lokacin farin wata. Haka ma sauran waƙoƙi dangin niƙa da daka da daɓe, duk akan rera su ne a wasu lokuta (misali, lokutan da ake gudanar da waɗannan ayyuka).

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments