Ticker

6/recent/ticker-posts

8.5 Waƙoƙin Gargajiya Na Tafiya Da Jinsi Da Kuma Rukunin Al’umma - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 153)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

8.5 Waƙoƙin Gargajiya Na Tafiya Da Jinsi Da Kuma Rukunin Al’umma

Abin da ake nufi a nan shi ne, waƙoƙin gargajiya na keɓanta ga jinsi ko (mata ko maza) ko wani rukuni na al’umma (manya ko yara). Da zarar an rera ɗaya daga cikin waƙoƙin, wanda ya san waƙar zai iya tantance ta mata ce ko ta maza, haka ma zai gane yara ke rera ta ko manya. Waƙoƙin mata manya dai sun haɗa da na daɓe, da niƙa, da daka da makamantansu. Waƙoƙin yara mata kuwa sun shafi waƙoƙin gaɗa na dandali da waƙoƙin tashe. A ɗaya ɓangaren kuma, waƙoƙin yara maza sun haɗa da na tashe da kuma na wasanni kamar su wasan Sallar Kwaɗi, da wasan Jini Da Jini da makamantansu.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments