Ticker

6/recent/ticker-posts

7.6 Kammalawa - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 149)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

7.6 Kammalawa 

Haƙiƙa waƙa wata babbar dabara ce da mabarata ke amfani da ita yayin gudanar da bararsu. Amfani da wannan salo na waƙa a lokacin bara na samar da nishaɗi da ban dariya ga wanda ake roƙa. Wani lokaci kuma waƙoƙin na zuwa da wa’azantarwa ko faɗakarwa ko dai tunatarwa ga aikata ayyuka masu kyau, musamman sadaka. Irin waɗannan kalamai na jan hankalin waɗanda ake roƙo zuwa ga ba da sadaka.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments