Ticker

6/recent/ticker-posts

7.5 Almajiri Da Ƙaho - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 147)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

7.5 Almajiri Da Ƙaho

Wannan ma na ɗaya daga cikin waƙoƙin bara da suka zaga ƙasar Hausa sosai. Yara ne suka fi amfani da wannan waƙar bara, musamman almajirai. Kimanin yara uku zuwa sama da haka ne suke rera ta yayin yawonsu na bara. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Ɗan tuɓulle, tuɓulle,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ga almajiri da ƙaho,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ga almajiri da ƙaho uku,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Guda na shukar gero,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Guda na shukar dawa,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Guda na shukar marar tuwo a saka a baki da daɗi,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Sai ni malam Audu

Amshi: To!

 

Bayarwa: Naj je barar alkali,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ciwon ciki ya riƙe ni,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Daga mai jiƙa mini kanwa,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Sai mai jiƙa min manda,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ba magani ke nan ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: A samu farare-farare,

Amshi: To!

 

Bayarwa: A samu fararen mata,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Su ɗebo nonon shanu,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Su likkiɗa mini damu,

Amshi: To!

 

Bayarwa: In karkace hulata,

Amshi: To!

 

Bayarwa: In rangaɗa ma cikina,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ciwon ciki ya yi sauƙi,

Amshi: To!

Wannan waƙa ma tana ɗauke da barkwanci. Za a tsinci hakan daga kalaman mai ba da waƙar, inda ya nuna yana da ƙaho uku, yayin da guda ke shukar gero, guda kuma ke na dawa, na ukun yana can yana shukar marar tuwo a baki. ke nan dai yana ta lomar tuwo. Sannan ya yi amfani da salon alamci, inda ya bayyana yunwa a matsayin ciwon ciki.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments