Ticker

6/recent/ticker-posts

7.4 Kulle - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 145)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01. 

7.4 Kulle

Wannan ma waƙar yara ce, musamman almajirai. An fi gudanar da ita a lokacin sallar layya. Akan yi ta ne musamman domin barar nama. Mabarata kimanin biyu ko sama da haka ne ke zagayawa domin gudanar da wannan waƙar bara. Ɗaya daga cikinsu zai riƙa ba da waƙar, saura kuwa za su ci gaba da amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Ina iya, ina iya?

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Ina Baba mai gidan nana?

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Su zo su ba mu na Annabi,

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: In sun ba mu na Annabi,

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Allah zai saka musu,

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Annabi zai saka musu,

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Ɗan zabo da farar ƙafa,

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Ɗauki kara ka ga ya gudu,

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Ɗauki hatsi ka ga ya tsaya,

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Ina iya, ina iya,

Amshi: Kulle.

 

Bayarwa: Ina baba mai gidan nana?

Amshi: Kulle.

Za a lura cewa, wannan waƙa na ɗauke ne da jigon roƙo ko bara. Yaran sun fara da tambayar inda masu gidan suke (Iya da Baba), sannan suka nemi da cewa su zo su ba su na Annabi. Sai kuma suka ƙara da kwaɗaitar da masu gidan ga sakamakon alkairi da za su samu yayin da suka ba su sadaka. Wato kamar yadda suka faɗa, “Allah zai saka musu” sannan “Annabi zai saka musu.” Daga ƙarshen waƙar kuma sai suka yi wani shaguɓe da ke nuna, idan an ba su fuska sai su tsaya, yayin da kuma ba su ga fuska ba, sai su wuce. Wato dai tamkar yadda ɗan zabo zai tsaya idan aka ba shi hatsi, yayin da aka ɗauki kara kuma, zai kama gabansa.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA 

Post a Comment

0 Comments