Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
7.4 Mu Roƙi Allah Jalla Sarki
Wannan waƙar ma manya ne suka fi yin ta yayin yawon bararsu. Mutum ɗaya ma na iya yin bara da wannan waƙa, sai dai wani lokaci akan samu mutane biyu ko sama da haka na yin ta a lokaci guda, yayin gudanar da bararsu. Ga yadda waƙar take:
Mu roƙi Jalla Sarki,
Mai sarauta da’iman.
Ya ba mu iko ga Annabi,
Ran ƙiyama ba mu bara.
Ko wagga Annabi ranar ƙiyama,
Ya warke ciwon duniya,
Da na lahira duka babu shi.
Wannan waƙa na ɗauke da faɗakarwa. Mai waƙar na nuna cewa, kasancewarsa musaki daga Allah ne, wato dai Allah ne Ya jarrabe shi da wannan cuta (misali makanta ko kuturta ko gurgunta). Sannan yana nuna cewa, a ƙiyama ba haka zai tashi ba, kuma ba zai yi bara a ƙiyama ba, tun da za a tashi mutane ne duka bai ɗaya, kamar yadda addinin Bahaushe (Musulunci) ya nuna.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.